← Book details Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 45

Sashe 25

Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zafafe na arasa mi ewa sannan na kama handle ofar da niyyar bu ewa naje na ci musu mutunci, sannan na nuna musu cewar nasan duk abun da suke shirin aikatawa. "Amira!". Muryar Amrah ta dira a dodon kunnuwana hakan ya sanyani dakatawa daga shirin shiga akin da nayi. *Assalamualaikum dan Allah kuyi ha uri, nayi niyyar yi muku typing da yawa to amma hakan bai* *samu ba sakamakon an kwantar da anwata a asibiti, azu da azahar, wannan typing in ma tun safe na yi shi shiyasa, amma da yau kam ma ba zaku samu posting ba,dan haka kuyi ha uri kuyi manage har zuwa lokacin da za'a sallamo ta, kafin ta samu lafiya,ina fatan zaku mun* *uzuri* *MANGA* _Comment_ , _share_ _fisabillillahi_ *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA*: _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ *Free book* --------------------------------------------- *Bissimillahir rahmani rahim* *019* _____________________________ Takowa Amrah tayi cikin sauri har ta araso in da nake tsaye in,sannan ta sanya hannu ta juyo da fuska ta muka kalli juna cikin matsanancin mamaki Amrah ta furta. "Amira kuka!, Amira kuka kike mai ya sameki?". Duk yadda na so na daidaita kaina amma abun ya gagara inda a maimakon na bawa Amrah amsar tambayar da ta mun in,kawai sai gani tayi na rungumeta tare da fashewa da wani irin kuka mai ta a zuciya. "Innalillahi wa'innailaihi rajiun, Amira wai meye haka dan Allah?, Amira ko wanine ya mutu ban sani ba?, Dan Allah ki sanar dani". Amrah ta fa a cikin matsanancin tashin hankali a lokacin itama har idanun ta sun fara cikowa da hawaye saboda yadda nake rubzar kukan duk rashin tausayin mutum sai ya ji tausayi na domin kuwa zaku yi tunanin cewar ko uwata ce ko ubana wani ya mutu. ofar akin namu muka ga an bu e inda muka ga su Azra sun fito daga cikin akin alamar kukan da nake in ne ya sanya su fitowa. "Subhannallah Amira lafiya kuwa? Amrah mai yasameta haka?". Azra ta fa a tana arin kai hannun ta jikina dan ta ta a ni. Ai da sauri na ago da fuskata da niyyar balbale ta da bala'i, sai dai mai kallon da naga tana jifana dashi ne ya dakatar dani daga abin da nayi niyyar yi in, domin kuwa wani irin kallo mai cike da alamar garga i Azra in ta shiga aika mun,idanun ta ka ai na kalli na fahimci inda ta dosa da kuma abun da take nufi,watau Amira kar ki fara wannan gangancin domin kuwa zaki yi dana sani. Wannan kallon da naga Azra tana mun ba aramin tayar mun da hankali yayi ba,take jikina yayi sanyi inda na janye jikina daga na Amrah sannan na shige cikin akin ina tafiya kamar wadda wai ya fashewa a ciki,na bar su Amrah tsaye baki sake. Sai dai ina shiga cikin akin Amrah ta biyo bayana da sauri tana cigaba da jaifamun tambayoyin da tamun azun amma shiru nikam ba amsa. Sai dai a raina na uduri niyyar in sha Allah duk yadda zan yi sai nayi domin na tarwatsa shirin su Afrah in,sannan zan samu Azra ko gobe ne mu ke e da ita na mata nasiha ko Allah zai sa taji. Sai dai washegari tun da asubar fari aka irani a gida inda ake mun neman gaggawa sakamakon jikin mahaifina da ya tsananta har an kaishi asibiti. Cikin tashin hankali na tashi na shirya sannan na sanar da su Amrah abin da yake faruwa,sai dai sun bu aci na bari su shirya mu tafi tare,ban so su Afrah suka bini ba,amma ba yadda zan yi domin kuwa ina yin wani abu alilan Amrah zata iya fahimtar wani abu shiyasa na yale su muka tafi tare, inda bayan sun duba shi suka dawo makaranta nikuma suka barni a can. Allah sarki Amrah ashe wannan dawowar da suka yi ita ce mafarin komai. Bayan tafiya ta da kwana biyu abubuwa sun faru wa anda ban san wasu ba,wasu kuma na samu labarin su daga wajen wasu abokanan karatun mu. Yau ta kama Friday da wuri su Amrah suka tashi a lecture tafe suke su hu u a harabar makarantar,idan ka kalle su sai sun baka sha'awa domin kuwa zaka iya rantsewa zuciya aya suke zaune da juna sai da ta ciki na ciki. A dai-dai wajen roundabout in da zaka nufi hanyar hostel suka ci karo da wata ar class in mu in da tana hango su ta fara musu kirari tun daga nesa. "Kaga taurari guda biyar a ganku a barku tun daga nesa kuke haskawa,amma kuma gaskiya yau akwai abu aya da babu a cikin ku". ayar tauraruwar ce babu, watau Amira". Anisa ta fa a da sauri. "Tabbas!, Amma ina kuka baro ta". "Hmmm wallahi Fiddausi mahaifin ta ne ba lafiya tana gida an kwantar dashi a asibiti". Amrah ta fa a fuskarta da alamun damuwa. "Eyya Ubangiji Allah ya bashi lafiya". Fiddausi ta fa a cikin jimami sannan ta mana sallama ta wuce. Da Ameen suka amsa mata sannan suka wuce suka nufi Hostel. ***** angaren na kuwa a can asibiti yau mun tashi da matsanancin tashin hankali domin kuwa yau jikin mahaifina ya tsananta likitoci ne kawai suke kaiwa da komowa a kan shi. Sai dai abin da Allah ya nufa ba makawa sai ya faru,ashe jinyar mahaifina bata tashi bace,inda ba'a auki tsawon lokaci ba rai yayi halin shi, Allah ya yiwa mahaifina rasuwa. Wannan rasuwar ba aramin girgiza ni tayi ba dani da sauran an gidan mu musamman ma ni domin kuwa har aka kai mahaifina ma abarta aka dawo dashi ban san inda kaina yake ba. Bansan yadda aka yi su Amrah suka samu labarin rasuwar mahaifin nawa ba,sai ganin su nayi gaba ayan su a daren ranar har a lokacin ma ban farfa o ba, sai da na kwana ban san a wace duniyar nake ba kafin bayan gari ya waye na farfa o inda na tarar da su Amrah da Afrah a kaina suna mun firfita. Sannu suka mun gaba ayan su,amma ban samu damar amasawa ba sai ido da na bisu dashi. Kwanan su Amrah biyu a gidan mu kafin a ranar na uku suka kama hanya suka koma makaranta bayan sun raka mahaifina da addu'ar samun rahamar Allah. Tun daga bakin gate in makarantar mu Amrah ta fara ganin wani ba on al'amari yana faruwa domin kuwa duk inda suka wuce sai taga alibai ana binta da kallo wasu kuwa har nunata suke wanda ta rasa gane dalilin hakan. A haka dai suka cigaba da tafiya har suka doshi hanyar Hostel, sai dai abun mamaki shine suna isowa daf da wata dabar wasu an mata da samari,kunnuwan Amrah suka jiyo mata wata kalma da tayi matu ar bata mamaki. "Kun ganta waccan ta tsakiyar ita ce ai,ku ganta kamar ta Allah ashe munafuka ce kullum cikin hijab ashe na arya ne". Wani saurayi ya fa a yana nuna saitin inda Amrah in take. "To kai daman Hamza ai kawai ka kalli masu sanya hijab in nan ka yale su,domin kuwa duk munafukai ne,cikin su fal yake da iskanci". Da sauri Amrah ta kai duban ta wajen samarin sannan ta dubi su Azra a tunanin ta ba da ita suke maganar ba, sai dai tana kallon su taga ita suke nunawa. "Azra kun ji abun da wa an can suke fa a kuwa?". "Wallahi na jisu amma share su neman maganane kawai". Azra ta fa a cikin son ta kawar da zancen. Haka dai suka arasa Hostel inda suna shiga suka ci karo da Fiddausi ta nufo su hankali tashe, tare da kama hannun Amrah tace. "Amrah Dan girman Allah idan kin arasa shiga cikin Hostel duk wanda kika ji ya miki wata maganar banza karki saurari kowa". "Fiddausi lafiya kuwa mai yake faruwa?". Amrah ta fa a fuska cike da mamaki. "Bakomai kede kawai kiyi abun da nace". Fiddausi tana kaiwa nan a zancen nata ta wuce su Amrah da sauri ta bar wajen. Shiru Amrah tayi cike da mamakin wa annan abubuwan. ***** A can gidan mu kuwa,cike gidan yake da mutane har a sannan gidan kamar yau aka yi mutuwar. Kun san yadda gidan mutuwa yake a wannan zamanin wanda ya mutu shine dai ya mutu sai kuma an uwan shi na jiki wanda mutuwar ta shafe su. To haka take a gidan namu ma inda wasu cin abinci ne ya kai su, wasu kuwa gulma ce ta kai su,kowa dai da abin da ya kai shi. "Ke awata kinga wani video da akayi posting azu a TikTok". Wata mata ta fa a tana nunawa ta gefen ta wayar tata. "Innalillahi wa'innailaihi rajiun awata wannan ai yarinyar da suka kwana a gidan nan ne jiya, awar Amira". Matar ta fa a tana asa- asa da murya wai gudun kar na jita,sai dai bata san ta makaro ba domin kuwa caraf naji dirar maganar tata a kunnuwan na. Haka kawai naji gaba ya shiga bugawa,inda naji a raina ina son naji akan abun da suke maganar. A hankali na tashi sannan na nufi inda suke zaune in na zauna a gefen su. Su kuwa ganin na dawo kusa da su sai suka fara arin sauya zancen da suke in, ni kuwa hannu na sanya na auki wayar da take kan cinyar matar sannan na cemata cikin dasasshiyar murya ta wacce kana ji kasan ta gaji da kuka. "Nuna mun videon da kuke magana a kai". Haka kawai matar taji na mata wani irin warjini take ta kar i wayar ta shiga TikTok in sannan ta kunna videon. Fuskar Amrah ce ta bayyana a jikin videon,inda ta shiga toilet sanye da towel sannan ta cire shi ta ajiye a gefe sai gata tsirara haihuwar uwar ta tana wanka. Wata irin sarawa kaina yayi take kuma wayar ta su uce mun a hannu inda na fara ganin dishi-dishi sai kuma cak numfashi na ya datse inda na zube a wajen a sume. Nan fa mutane aka yo caaaaa a kaina inda kowa ya shiga fa in albarkacin bakin shi, mahaifiya ta
Chapter 25 · 0% Book details