Sashe 37
Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya bani har sai da dariya ta so kufce mun na yi arin gumtse baki na, wai kiji wani ikon Allah wai Azrah ce take furta bata shirya mutuwa yanzu ba. "Azrah wai lafiya kike kuwa ki nutsu mana, wai mai yake damun ki ne,waye zai kashe ki?". Na jefawa Azrah wa annan tambayoyin a lokaci guda tare da ago kan ta muka fuskanci juna. Sai a sannan Azrah ta ago kan ta sannan ta fara waige-waige a cikin akin, bu e baki tayi da niyyar yi mun magana amma sai taji komai ya auke mata cak daga cikin walwar ta,duk yadda Azrah ta so ta tuna abin da ya faru da ita a daren jiyan abin ya gagara, walwar ta kamar an wanke mata ita ko kamar wadda ta ha u da cutar mantau. Bata ce komai ba sai ta fara arin tashi tana jin duk jikin ta ya mata tsami,sannan ta shiga toilet ta ha a ruwan wanka zata yi wanka,sai da ta gama ha a ruwan wankan ta cire kaya zata fara wankan kawai taga gaba aya ruwan ya koma jini. Wani mahaukacin ihu Azrah ta sake sannan yanki jiki ta zube a cikin toilet in gaba aya in banda rawa ba abun da jikin ta yake mata,wata irin zuffa ce ta shiga karyo mata,da rarrafe ta nufi hanyar fita daga cikin toilet in amma sai dai duk irin jan da ta yiwa ofar ta kasa bu e ta. Wannan dariya mai ha e da kukan aka shiga yi kafin kuma abubuwan cikin toilet in su shiga tashi suna kewaye Azrah duk abin da ya zo kewaye ta sai an buga mata kan a jikin shi ga maruka da aka shiga zabga mata ta kowane gefe na fuskar ta. Ihu Azrah ta shiga yi tana bugun ofar iya arfin ta tare da ura sunan mu amma abin da bata sani ba shine duk wannan ihun da take da buga ofar ba wanda yake jin ta a cikin mu balle a kawo mata auki. A ranar dai Azrah taji a jikin ta domin kuwa tashin hankali ba irin wanda bata gani ba a cikin toilet in azaba iri-iri haka ta shata ba wanda ya kawo mata taimako. Kuka kuwa ta yi shi har sai da hawaye ya daina fita daga idon ta, a lokacin gaba aya Azrah har ta fice a hayyacin ta sannan ta sadda ar da cewar watan mutuwar ta ne ya kama ,sai da aka auki tsawon lokaci kafin komai ya lafa,sannan ofar ma ta bu e da kan ta. Haka Azrah ta tashi da gudu ta fice daga cikin toilet tana mai da numfashi. Kallo muka bita dashi cike da mamaki tare da Zaro ido waje ganin ta fito da gudu sannan bata yi wankan ba,gashi ba towel in da ta shiga dashi "Azrah lafiya kuwa naga kin fito daga toilet da gudu sannan mai ya same ki a fuskar ki haka naga jini ya taru miki a gefen ido?". Cewar Anisa tana kawar da idon ta gefe. Duk yadda Azrah ta so ta tuna abin da ya faru Abu fa ya gagara gashi tana son yin magana amma komai duk wani abu ya auke mata,to mai yake shirin faruwa da ita haka?. Ta jefawa kan ta wannan tambayar sannan ta dube mu tace. "Mai kuka gani mai ya same ni?, Nima ban san abin da ya same ni ba, kawai na farka ne naga fuska ta a kumbure wata ila fa uwa ne jiya ina bacci". "Azrah da alamu baki san a yadda kika fito daga toilet in ba ko?, Ko dai adangare ne ya koro ki?" Afrah ta fa a tana unshe dariyar ta, Kallon kanta Azrah tayi wadda sai a sannan ta lura da yadda ta fito daga cikin toilet Da sauri ta nufi wajen kayan su ta bu e ta akko wasu kaya ta sanya. A ranar dai wankan da Azrah bata yi ba kennnan muka tafi lecture a haka. Tun daga wannan ranar kullum sai a Amrah ta zo wa Azrah da dare,daga zarar mun yi bacci to ita kuma fa Azrah watan cin uwar ta ya kama a wajen Amrah sannan da zarar safiya kuma ta yi to Shikennan Azrah zata nemi duk wani abu da ya faru ta rasa, bacci kuwa tayi arba dashi. Lokaci guda Azrah ta rame ta zabge ta fita a hayyacin ta gaba aya duk wanda ya san Azrah kallo aya zai mata ya fuskanci cewa akwai abin da yake damun ta. Yau ta kama ranar da zamu fara exams, Alhamdulillahi mun yi paper in farko lafiya mun fito sai dai a wajen Azrah fa ba wani abu da ta tsinana domin kuwa duk wani abu da ta karanta tana shiga akin jarrabawa take mantawa,kuma daman ba wani karatun ma take samu ta yi ba duba da cewar bata iya karatu da rana sai da dare, sai gashi daren kuma ya zama mata daren tashin hankali a gare ta. Yau muka gama exam lafiya kowa ka gani cikin farin ciki yake ana ta shirin tafiya gida, Ni kuwa farin ciki na bai wuce zan je naga Aminiya ta Amrah ba wadda na yi kewa. Kai tsaye ina komawa gida na fara shirin tafiya garin Giwa in bayan na sanar da Mahaifiyata duk wani abu da ya faru da Amrah in domin kuwa bana oye mata komai. Sosai Mahaifiyata ta tausayawa Amrah in sannan tayi Allah wadai da halin su Azrah,sannan ta ce na shirya zamu je tare da ita. Hakan kuwa aka yi muka shirya Ni da mahaifiyata driver ya auke mu sai garin Giwa. Allah sarki mun isa garin lafiya sai dai mun tarar da labarin da yayi mugun aga mana hankali, in da muka tarar da cewar Malam Kabiru da iyalin shi sun tattara sun bar garin Giwa in sannan kuma ba wanda ya san inda suka nufa, daman kuma su ba an asalin Kaduna bane kasuwanci ne ya kawo mahaifin Amrah in har ya hayyayafa a garin. Babban labarin da ya fi girgizani ya kuma aga mun hankali bai wuce labarin mutuwar Amrah da na samu ba. Wannan abun ya gigita ni fiye da tunanin mai tunani. Wallahi ni dai ban san yadda aka yi ba sai bu ar ido na yi na ganni a cikin gidan mu a kan cinyar mahaifiyata tana mun fifita inda nikuma nasan cewar mun je garin Giwa ne. Abubuwa ne suka shiga dawo mun aya bayan aya,da gaske Amrah ta mutu?, Ita ce tambayar da ta fara fitowa a bakina zuwa kunnuwan mahaifiyata. uri mahaifiyata ta bani sannan ta mun nasiha sosai tare da mun kashedin cewar na fita a harkar su Azrah tun da su ba mutanen kirki bane sannan kuma na yi gaggawar neman duk wata hanya domin na fito na bayyana gaskiyar da ni ka ai na santa ko dan na wanke Amrah a idon duniya. Na amince da abin da Mahaifiyata ta ce sai dai kuma ta yaya zan fara fitowa na shaidawa duniya wannan OYAYYEN SIRRIN da ni ka ai na san dashi?, Tabbas akwai aiki a gabana amma fa sai na shirya na kuma yi taka tsantsan. Haka rayuwa ta cigaba abubuwa sun shu e ba adadi, na so na fita daga cikin rayuwar su Azrah gaba aya kamar yadda Mahaifiyata ta bu ata sai dai samuna da Azrah tayi tana kuka ta nuna mun cewar ta yi danasanin komai ya sanya na an ji tausayin ta sannan muka cigaba da rayuwa ,amma fa ina baya-baya da su ba kamar yadda mu ke da ba, domin a da kan ma har aki na so sanjawa sai kuma na fasa. Kwanaki sun shu e,Satikai sun zo sun biyo bayan su, watanni sun zo sun shu e yau wata uku mu ke dosa da mutuwar Amrah, kuma i zuwa yanzu komai ya lafa na daga tsoratarwar da take yiwa Azrah har Azrah in ta fara dawowa hayyacin ta,sai dai ashe a wannan karon mai gaba aya zata musu. Ban san yadda aka yi ba da rayuwar Anwar domin kuwa tun bayan da na samu labarin mutuwar Amrah ta daina zuwa mun a bacci ta daina sanar dani komai ban kuma san dalilin hakan ba. Ban san yadda aka yi ba kawai sai wayar gari nayi na tarar da Afrah sun fara soyayya da Anwar kamar za su ha iye juna. Wannan abin ba aramin mamaki ya bani ba har sai da na tari Anwar in da maganar sai dai abin da ya sanar dani shi yafi komai aga mun hankali inda yake cemun ai ko da Amrah tana da rai ba haramun bane dan ya so Afrah balle kuma Amrah ta mutu, kuma ko da tana da rai mai zai yi da karuwa wadda ta gama tallatawa duniya kan ta,Allah ya tsari Gatari da saran shuka. Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine kawai abun da na iya fa a domin kuwa a lokacin in da wani ne yace mun Anwar zai aikata haka a Amrah wallahi arya tawa zan yi amma da idona da kunne na ji, ya Subhannallah. A ranar na yi kuka sosai irin kukan da rabon da na yi shi tun bayan mutuwar Amrah,na ji na tsani awance fiye da tunanin mutum,na tsani Afrah fiye da yadda na tsani Azrah da Anisa domin kuwa Afrah ita ce silar komai. A kwana a tashi har magana ta yi nisa tsakanin Anwar da Afrah inda cikin lokaci ani aka tsaida ranar biki, sai dai a ranar da za'a aura mu su aure komai ya lalace domin kuwa a ranar Amrah ta kashe Afrah. Follow my Whattpad account @shamsiyamanga Arewa books @Shamsiyyamanga Whatsapp number 07060943991 Phone number 09065779330. Comment Share fisabillillahi. *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ *Tsarawa/Rubutawa* *SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA*: _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ . *Free book* ----------------------------------------------- *Bissimillahir rahmani rahim* *029* ____________________________ Shiru Amira ta yi tare da Sunkuyar da kan ta asa wasu hawaye masu umi ne suka shiga zubo mata tana jin zuciyarta kamar zata faso irjin ta ta fito,ji take kamar a yanzu komai yake faruwa bada labarin da