← Book details Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 45

Sashe 36

Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kwance a cikin aki yana jin komai wasu hawaye ne masu zafi kawai suke zarya a kuncin shi. Daf da ana shirin fita da gawar su Amrah in ne aka ga Malam Kabiru ya fito daga cikin akin da yake kwance in kamar ba shine ya ta a wata jinya ba,sannan a hankali ya nufo wajen da gawar take lullu e a cikin likkafani,tsugunawa yayi dai-dai saitin fuskar ta sannan ya bu e fuskar a hankali ya bu i baki ya fara magana cikin rawar murya. "Ubangiji Allah ka ji an wannan baiwa taka,Ya Allah ka sa tayi kyakkyawan arshe,Allah nasan wacece ata Amrah na kuma san abin da zata yi da wanda ba zata yi ba ya rabbi samawati Wal ardi ka yafe mata duk wani abu da ta ta a aikatawa sananne da kuma oyayye,Allah ka ha a ta da mala'ikun Rahma,Allah ka fa a mata abarin ta ka yalwata mata shi,Amrah ina miki kyakkyawan zato da samun rahamar Allah domin kuwa ni na da e da sanin cewa baki aikata wannan mummunan abun da aka ce kin aikata ba,nasani wallahi ata Amrah ba zata ta a aikata haka ba,ina ma ace kina duniya Amrah ina ma ace sai da muka yi ganawar arshe kafin kika tafi amma ina! addara ta riga fata, Amrah in sha Allah ma iyan ki sai sun kunyata a idon duniya in sha Allah nan da an wani lokaci ani nasan gaskiya zata yi halin ta a lokacin da kowa zai so ina ma kina da rai gaskiya ta yi halin ta,wasu kuwa kuka zasu dinga yi da idanun su suna so su nemi yafiyar ki amma lokaci ya ure musu.". Daga haka ya dakata da maganar da yake in sannan ya tashi ya nufi inda gawar Hisham take shima addu'a ya masa sannan yace a zo a auke a je a sallace su. Duk wanda yake wajen sai da jikin shi yayi sanyi da jin maganganun Malam Kabiru in wasu kuwa har sun fara zubar da hawaye. Daman gidan har ya fara cika da mata da yawa sun zo gulma ne da kuma ganin irin mutuwar wula anci da Amrah ta yi a cewar su sai kuma gashi labari ya sha bambam domin kuwa abin da suka yi zato in ba haka bane. Sanda aka zo fita da gawar su Hisham da Amrah Gwaggo Sa'adatu sai da aka ri e ta domin kuwa wasu abubuwa ta dinga yi tana fisge-fisge kamar hauka sabon kamu. A haka aka fita da su aka je aka sallace su sannan aka mi a su gidan su na gaskiya,Malam Kabiru da kan shi ya sanya gawar Amrah a cikin abari sannan ya aga hannu sama ya shiga kwararo mata addu'a bayan ya gama ne aka binne ta sannan aka binne gawar Hisham ma daga gefen abarin Amrah. Lokacin da aka dawo daga binne gawar su Amrah in gidan na su tunin ya da e da cika aka shiga zaman makoki wanda rabi gulma ce da munafurci ya kawo su. ***** Yau kwana uku da mutuwar Amrah kuma har zuwa yanzu ban san da labarin mutuwar ba abun da na sani kawai shine tun da Amrah ta tafi gida bana samun wayar ta,gashi idan na ira wayar Anwar ma bata shiga haka an gidan su Amrah in ma kasancewar duk an gidan su inada number in wayar su, wannan abu ba aramin aga mun hankali yayi ba ya kuma sanya ni na shiga ru ani, sai dai na yanke shawarar kawai muna samun hutu idan mun gama exam zan shirya naje har garin Giwa in na gano a wane hali Amrah in take ciki kasancewar saura sati guda mu fara exams. Sai dai cikin an kwanaki biyun nan tun bayan tafiyar Amrah in ina yawan jin fa uwar gaba da ban san ta Meye ba, sannan kullum idan na kwanta bacci sai na yi mafarki da Amrah a cikin wani kogon rami sanye da farin mayafi amma da zarar na yi arin yi mata magana sai in nemeta in rasa ko kuma na farka. A ranar da ta cika kwana na uku da rasuwa ne na yi mafarki da ita inda har ta mun magana sai dai abu aya ta fa a mun na nemeta na rasa shine ta sanar dani cewa na sanarwa su Azra lokacin aukar Fansa yayi. Ban sanar da su mafarkin ba domin kuwa Tsakanina da su zuwa yanzu sai dai ido domin kuwa tunin na fita a harkar su duk yadda suka so su shiga harka ta hakan baya yiwuwa domin basa samun fuskar hakan, harakar gabana kawai nake yi na fita a ta su harkar. Yau tun da wuri na dawo aki na kwanta sakamakon kai na da yake mun ciwo sosai, ban da e da kwanciya ba bacci ya auke ni. Su Azrah sai wajen arfe sha biyu suka shigo akin sun tsaya group discussion sakamakon lokacin exam in mu ya kusa. Azra bata kwanta da wuri ba har arfe aya inda ta tsaya kallo a system in ta daman bata cika kwanciya bacci da wuri ba duk muna rigata yin bacci. Kallo take gaba aya hankalin ta ya tafi i zuwa cikin system in,ji ta yi kamar arar abu ya gifta ta gefen kunnen ta, a hankali ta waiga sai dai bata ga komai ba. Juyowa tayi da niyyar cigaba da kallon sai dai abin mamaki shine system in tata ta gani tana yawo a saman akin,bata gama kallon wannan abin tashin hankalin ba ta fara jin wata irin iska mai arfi ta fara tashi a cikin akin inda ta shiga rufe ofa da windunan cikin akin tana bu e su da arfi a lokaci guda kuma wutar akin ma ta fara wata irin fafarniya tana kashe kanta tana kunnawa. Wani irin kuka ne kuma mai matu ar ban tsoro ya karra e cikin akin sannan kuma aka shiga yata wata irin dariya marar da in ji. Wata zuffa ce ta shiga karyowa Azra a kowane sashi na jikin ta tsoro firgici ha e da tashin hankali ne suka dirar mata fara ja da baya ta yi in da ta fara arin mi a hannun ta dan ta tayar da su Afrah,sai dai ba shiri tayi saurin janye hannun nata tare da sakin ihu a lokacin da ya sau a a jikin Afrah in sakamakon wasu irin ayoyi da taji sun caki hannun nata. Bata yi auni ba sai ji tayi an aga mata sama cak an fara hajijiya da ita a cikin akin inda aka shiga gwara kan ta ta kowane kusurwar akin. Ihu Azrah ta shiga yi tana wala iran sunan su Afrah amma ina ba wanda ya san tana yi balle ta sa ran za'a wace ta. Sai da aka gama galabaitar da ita kafin aka yi jifa da ita ta fa i can gefe guda tana mayar da numfashin wahala,sai dai har zuwa wannan lokacin iska da kuma wutar akin ba su tsaya ba ga wannan kuka da dariyar yana nan ba'a daina ba. Azrah kuwa wata irin azaba take ji a kowane iri sashi na jikin ta kamar ana zuba mata ruwan dalma wani ihu ta shiga yi tana birgima a asa saboda tsananin azabar da take ji Can zuwa wani lokaci wutar akin ta tsayar da kan ta kafin kuma komai ya tsaya, itama kuma Azrah ta daina jin wannan azabar. A hankali Azrah ta shiga bu e idanun ta sai dai abin da ta yi tozali da shi in ne ya sanyata sakin wata ara a lokaci guda kuma wani fitsari ya shiga biyowa ta tsakanin cinyoyin ta sai kuma ta tafi luuu ta sume a wajen saboda tsananin razanar da tayi. Ba komai Azra in tayi arba da shi ba da ya tsoratata face Amrah da ta gani a tsaye cikin fararen kaya da suka aci gaba aya da jini,harshen ta ya zazzago ga idanun ta da yake zubar da hawayen jini. Takowa Amrah ta fara yi har ta araso kan Azrah in sannan ta sanya hannu ta ago kan ta wasu zafafan maruka ta shiga kwashe ta da su ta ko ina wanda yayi sanadiyar farfa owar Azrah in daga suman da tayi Ihu take tana kururuwa tare da ro on Amrah a kan ta yi ha uri amma Amrah ko saurarar ta bata yi ba ba kuma ta da niyyar saurara mata Kan kace kwabo Amrah ta ha awa Azrah jini da majina ta kuma sanja mata gaba aya hallitar fuskar tata inda ta kumbura mata ita tayi suntum. A wannan daren dai gaba ayan shi Azrah bata yi bacci ba,saboda tsananin tashin hankalin da take ciki in suma kuwa tayi yafi sau a irga. Da asubah ni na fara tashi inda na nufi hanyar shiga toilet,sai dai turus nayi na ja na tsaya sakamakon tozali da nayi da Azrah a yashe a bakin ofar toilet kamar bata da rai ga fuska a kumbure suntum,gabana ne yayi ta mummunar fa uwa sakamakon tunowa da nayi da mafarkin da nayi a daren jiya na Amrah da Azrah *Wasan ya fara yanzu fa Azrah an fara girbar abin da aka shuka*. Follow my Whattpad account @shamsiyamanga. Arewa books @shamsiyyamanga Whatsapp number 07060943991 Phone call 09065779330 Comment Share fisabillillah. *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA*: _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D auta, Sis Amira Adam, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi._ *Free book* ------------------------------------------------ *Bissimillahir rahmani rahim* *028* ______________________________ Har na yi niyyar auke kaina na wuce sai kuma dai na nufi inda Azrah in take yashe sannan na fara an bubbuga ta ina iran sunan ta,shiru bata amsa ba hakan ya tabbatar mun da cewar a sume take. ewa na yi na nufi cikin toilet in namu inda na ebo ruwa mai sanyi na zo na watsa mata. Da wani kalar razannannen ihu Azrah in ta farka inda ta shiga cewa. "Dan girman Ubangiji kar ki kashe ni ki yiwa Allah ki yale ni wallahi ban shiryawa mutuwa yanzu ba". Azrah ta fa a tana ame mun hannu a tunanin ta Amrah ce cikin tsananin firgici. Ni kuwa abun nata ma dariya
Chapter 36 · 0% Book details