Sashe 33
Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
haka ya dinga jifa da su yana son sai ya fice a cikin akin bakin shi kuwa bai daina iran sunan Amrah. Ganin cewa idan har aka kuskura aka bar Anwar in ya fita to tabbas za'a samu matsala gaggaruma. "Anwar ka yiwa girman Allah ka dakata da duk wannan abin da kake yi in, nasan wallahi arya ne da hankalin ka baka haukace ba". Turus Anwar in ya ja ya tsaya har ya kama handle ofar zai bu e sakamakon Muryar mahaifiyar shi da ya ji ta mishi magana cikin kuka. Wasu hawaye ne masu zafi suka shiga zarya a kan kumatun Anwar in a hankali kuma ya shiga sulalewa a jikin ofar har ya kai asa. Wani irin kuka mai cin rai ya fashe dashi sannan ya juya ya dubi mahaifiyar shi da arasowar ta wajen Kennan yace. "Mama da gaske ne wai videon tsaraicin Amrahn da zan aura na gani yana yawo a social media?, Mama dan Allah ki ce dani bacci nake Mama ki ce dani mafarki nake duk abun da nagani ba gaskiya bane?, Mama wallahi idan har ya tabbata Amrah ce wannan to wallahi mutuwa zan yi domin kuwa ba zan iya rayuwa a duniya ba a yanzu haka ina jin zuciyata kamar zata tarwatse saboda ba in cikin da nake ciki, Mama in.........". Maganar Anwar in ce ta katse sakamakon wani uban kuka da ya sha eshi, take kuma ya fara wani irin tari ba autawa,wani irin ba in jini ne ya shiga fitowa daga cikin bakin shi inda da gudu likitocin suka yo kan shi ganin idanun shi ya shiga afewa. Kafin su araso har ya tafi asa ko shurawa bai yi ba. Wata ara mahaifiyar Anwar in ta sake tare da rungumo Anwar in tana ihu. yar likitocin suka samu suka are Anwar in a jikin ta,kafin su du ufa a kan shi domin bashi agajin gaggawa cikin tsananin tausayin halin da Anwar in yake ciki a wani angaren kuma tausayin mahaifiyar ta shine da fargaba suka dirar mu su domin kuwa suna gudun kar mai afkuwa ta afku,tun da gashi dai rayuwar Anwar in tana cikin tsaka mai wuya Da gudu mahaifiyar Anwar in ta tashi tare da yin waje a matu ar gigice, a bakin ofa suka kusa yin karo da Nazir wanda arasowar shi asibitin Kennan. Cikin sauri ya ru ota ganin kamar mahaifiyar ta su bata hayyacin ta sannan ya shiga tambayar ta. "Mama ina zaki je kuma mai yake faruwa naga kamar hankalin ki a tashe ya jikin yaya Anwar in". Duk a lokaci guda Nazir ya jefawa mahaifiyar ta su wa annan tambayoyin. "Nazir gidan su wancan karuwar yarinyar zan je, tsinnanniya wadda take son taga mun Bayan yaro,na rantse da girman Allah ba abun da zai hana yau ban aika yarinyar nan lahira ba,daga ita har munafukan iyayen nata,matu ar kuwa Anwar ya mutu sai na arar da duk dangin su dan wallahi sai na sa an kulle kaf dangin ta a prison kullewa ta har abada". Mahaifiyar Anwar in tana kaiwa nan a zancen ta ta juya ta kwashi uban sauri ta nufi hanyar barin asibitin domin zuwa gidan su Amrah. Da sauri shima Nazir ya bi bayan ta cikin tashin hankali domin ya riga da ya san wacece mahaifiyar ta su matu ar fa ta fa i abu to tabbas sai ta aikata sannan kuma ba wanda ya isa ya dakatar da ita. *MANGA* Follow my account at Whattpad @Shamsiyyamanga, Arewa books@shamsiyyamanga. Comment Share Fisabillillahi. *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION* *SADAUKARWA*: _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_. *Free book* ------------------------------------------------ *Bissimillahir rahmani* *rahim* *025* _______________________________ Wasu Hawaye masu zafi ne suka shiga kwarara a kan kuncin Amrah in duk yadda ta so ta daure kar ta kayi kuka amma abun ya ci tura sakamakon jin kalaman Yaya Hisham ushewa Amrah tayi a bakin ofar gidan na su tare da fashewa da wani irin kuka mai sauti,zuciyarta ce taji tana mata barazanar fashewa,dafe irjin ta tayi sannan ta shiga wani irin tari ba autawa har tana shi ewa. A wannan lokacin duk yadda Yaya Hisham in ya so ya kawar da kan shi akan Amrah in abun ya gagara wani matsanancin tausayin ta ne ya rufe shi a take soyayyar anuwantaka ta motsa Allah sarki naka naka ne koda kuwa fa a ku ke kullum to in har zai shiga wani yanayi sai kaji a jikin ka. Ganin irin tarin da Amrah in take ne ya sanya Yaya Hisham saurin arasawa kan ta,tare da ru o ta yana iran sunan ta. ago da kumburarriyar fuskar ta Amrah ta yi sannan ta sakarwa Yaya Hisham in murmushi kafin kuma ta bu i baki da yar ta fara magana. "Yaya Hisham kaima ka yarda da abun da mutane suke zargin na aikata ko?, Yaya Hisham kaima baya zaka juya mun kamar yadda kowa ya juya mu?, Yaya Hisham a makaranta kowa ya tsaneni,Yaya Hisham a makaranta kowa ya juya mun baya,ban isa na fita ba sai zagi sai hantara,Yaya Hisham ina jin zuciyata kamar zata fashe. A tunanina idan kowa ya juya mun baya Yaya Hisham ku bazaku juya mun ba,Yaya Hisham hannun ka ba zai ta a ru ewa ka yanke ka yasar ba". Shiru ta yi tare da sanya hannu ta goge jinin da yake fita ta bakin ta a fakaice ba tare da Yaya Hisham in ya lura ba,sannan ta kalle shi ido cikin ido kafin ta sakar mishi wani murmushi marar fassaruwa wanda ita ka ai ta san ma'anar shi kafin kuma ta cigaba da magana. "Hmmm Yaya Hisham bai kamata kayi saurin yanke hukunci a kaina ba domin kuwa nasan kafi kowa sanin halina da kuma abin da zan aikata da wanda ba zan aikata ba,Duk da cewar shi an Adam a kowane lokaci ya kan iya sanjawa sannan ya riki e amma wallahi Yaya Hisham wallahi arya su ke mun ban aikata ba,Yaya Hisham meyasa ka kasa mun adalci a yanzu rarrashi nake bu ata ba a ara ha amun wani zafin ba.Amma Bakomai Yaya Hisham kamar yadda ka bu ata zan tafi zan bar ku in sha Allah zan bar ku bari na har abada zan tafi ba zan sake waiwaiyar ku ba,ba zan shiga cikin gidan nan ba kamar yadda ka bu ata idan kuma kaga na shiga to sai dai idan gawata za'a shigar,Daga arshe zan ro i wata alfarma a wajen ka wadda nasan da wuya ka iya mun amma Yaya Hisham dan Allah ba dan ni ba ba kuma dan halina ba ka ro ar mun Abba ya yafe mun nasan ba lalle mu sake ha uwa ba wata ila sai dai a lahira,sannan dan Allah ka kuma sanar dashi cewar ban aikata abun da ake i irarin na aikata in ba wallahi sharri aka mun,dan Allah ku ma ku yaf..........". Kasa arasa maganar da take bakin nata tayi sakamakon wani tari da yaci arfin ta nan fa ta shiga yi ba autawa in da lokaci guda kuma wasu irin gudan jinnannaki suka shiga fitowa ta cikin bakin nata. A dai-dai wannan lokacin kuma Gwaggo Sa'adatu ta fito daga cikin gidan tare da Umar sakamakon Muryar Amrah in da suka ji da kuma tarin nata da ya i tsayawa. Fitowar su Gwaggo Sa'adatu in yayi dai-dai da tsayawar numfashin Amrah ci ak take duk wata jijiyar da take harbawa a jikin ta ta daina harbawa,sai dai har a sannan gudan jini bai bar fitowa ta bakin ta ba. Da gudu Gwaggo Sa'adatu ta arasa kan ta tare da rungumota tana fashewa da wani irin matsanancin kuka, Umar take ya shiga maimaita innalillahi wa'innailaihi rajiun. Shi kuwa Hisham ja da baya ya fara yi tare da fara jijjiga kan shi yana jin kan nashi kamar zai bar jikin wuyan shi,dur ushewa yayi a wajen tare da aura hannun shi a ka ya fasa wata ara. "Nooooooo Amrah,dan Allah ki taimaka ki tashi,wallahi arya nake miki ba zan iya juya miki baya ba,Amrah ki taimaka ki tashi kar ki tafi ki bar mu,Amrah wallahi muna son ki kawai d.........". Shima kasa arasa maganar da yake in yayi sakamakon wani kuka da yaci arfin shi,take kuma komai na jikin shi ya tsaya cak sai numfashin da yake ne ka ai zai tabbatar maka da cewar yana da rai. Umar ne kawai ya iya arfin halin sunkuyawa ya auki Amrah in tare nufar bakin titi da ita domin ya samu mota ya sanyata a ciki ya kaita asibiti ko akwai taimakon da za'a yi musu. Suma su Gwaggo Sa'adatu da Malam Kabiru haka suka bi bayan Umar in dukan su kamar wasu zarrarru. yar suka iya samun mota a bakin titin inda aka sanya Amrah a ciki aka nufi asibiti da ita. Suna barin wajen motar su Nazir da Mahaifiyar su tana shigowa cikin layin inda ko bari ba tayi Nazir in ya gama parking ba ta fito daga cikin motar saboda tsabar bala'in da yake cinta. Kai tsaye cikin gidan ta nufa tun daga zauren gidan ta fara surfa ruwan bala'i a tunanin ta gidan da mutane,sai dai shirun da taji ba wanda ya tanka mata ne ya bata tabbacin cewa gidan ba kowa. Kasancewar bata san Hisham ba shiyasa bata lura dashi ba da yake zaune a wajen da ya fadi tun azun ya kasa motsawa. Shi kuwa Malam Kabiru yana kwance a cikin aki yana jin duk tijarar da mahaifiyar Anwar in take yi,sai dai kasancewar tun bayan labarin da ya riske shi game da abun da Amrah in ta aikata ya zamana ya koma kamar mutum-mutumi komai nashi ya daina aiki sai dai a aga a tayar a kwantar,hatta wanka da alawla da duk wani abu da mai lafiya zai yi to shi sai dai a mishi,idon shi ne kawai yake aiki amma hatta magana ya daina yi,fitsari kuwa da bayan gari ba'a magana haka yake yi a jikin shi. Wannan yana daga cikin babban dalilin da ya sanya Hisham ya ara jin ya tsani Amrah saboda shi a ganin shi a sanadiyar Amrah