← Book details Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 45

Sashe 39

Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

abin da zaka ji sai Muryar Amira tana ba da labari da duk wani mai imani idan ya saurara sai jikin shi yayi sanyi. *GARIN GIWA* Samari ne sun fi ashirin zaune a teburin mai sai da shayi,wasu suna cikin rumfar wasu suna ta waje, wata atuwar Radio ce ajiye a tsakiyar su gaba aya hankalin su ya tafi kan Muryar da ake saurara a gidan radiyo in watau Muryar Amira da take bada labari a kan Amrah,duk wanda ka kalli fuskar shi a wannan lokacin ba abin da zaka gani face tsantsar damuwa da danasani ga wani gumi kuma da yake zubowa daga fuskokin wasu daga cikin mutanen wajen. Malam alha kuwa da yake zaune a gefe tunin hawaye sun gama wanke mishi fuskar shi sakamakon tunowa da abin da ya yiwa abokin na shi,gashi a halin yanzu bai san a wace duniyar abokin na shi yake ba gaskiya bai kyauta ba sannan bai cika aboki na gari ba da har ya bari zuciya ta yi tasari a kan shi ya manta da waye Malam Kabiru da kuma ahalin shi. Har aka gama jin labaran ba wanda ya iya motsawa daga inda yake sai can dai da yar wasu tsiraru daga cikin matasan wajen suka fara tashi aya bayan aya suna barin rumfar mai shayin cikin matsananciyar kunya ga kuma gwaiwowin su da suka da e da yin sanyi. Shi kuwa Malam alha har aka gama barin wajen aka bar shi ya kasa tashi domin kuwa kaf mutanen wajen sun watse sun bar shi a zaune a wajen kamar an dasa shi, shi kan shi mai shayin a ranar ha ura yayi da sana'ar shayin na shi tun da ba masu siya. yar dai Malam alha ya iya tashi gwaiwa duk ta gama sakewa sannan ya rarrafa ya shiga gida. Follow my Whattpad account @shamsiyamanga, Arewa books @shamsiyyamanga Whatsapp number 07060943991 Phone call 09065779330 Don't forget to share and comment pls. *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION* Kai jama'a Bari nima na ana yin wa . Rayuwa da masoyi a duniya babbar nasara ce an uwa . Ya Salam gaskiya masoyi yayi a rayuwa ni wallahi ban ta a sanin haka da in masoyi yake ba sai a kan ku masoyana . Tabbas naga ruwan auna sanadiyyar wannan jinyar da nayi . Jama'a ku bani tissue,wallahi some prayers sai da suka sanyani hawaye . I received a lots of messages from different places and different people,wasu mun yi magana via phones call, wasu sun tura mun message ta Whatsapp wasu ta direct message duk ana tambayar littafin FANSAR FATALWA . Ni kaina ban san haka littafin ya kar u a gare ku ba sai da na yi kwana biyu ban yi posting ba,and hakan ya faru ne sakamakon jinyar da na yi ciwon ido mura da kuma zazza .To Alhamdulillahi I'm getting much better and better know and Finally I'm back in sha Allah na dawo zamu aura daga inda muka tsaya godiya buhu-buhu gare ku masu yi mun addu'a wanda na sani da wanda ban sani ba,na fili da na oye Musamman ma an group ina na FANSAR FATALWA u people Ina son ku fisabillillahi because kun nuna mun zunzurutun auna wadda masoyan gaskiya ne kawai su ke nunawa ta hanyar yi mun addu'oi Lots of Love to u guys really appreciate ur concerned towards me . Yanzu dai jiki Alhamdulillahi amma ku yi ha uri saboda ba lalle na dinga yin dogon typing ba saboda idona an hanani kallon haske sosai,amma dai zamu lalla a a haka in sha Allah *SADAUKARWA* : _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk in da ku ke ina son ku fisabillillahi._ *Free book* ----------------------------------------------- *Bissimillahir rahmani rahim* *030* ________________________________ Kamar yadda Justice Kabir ya fa a washe gari kuwa sassafe ya buga sammako inda arfe bakwai a garin Giwa ta mishi sai dai ya bugi gurbi domin kuwa lokacin da ya isa garin yake samun labarin cewar ai iyayen Amrah in sun da e da barin garin. Wannan labari da Justice Kabir in ya tarar ba aramin aga mishi hankali yayi ba domin bai ta a kawowa a ran shi cewar labarin da zai tarar in ba kennnan. Haka Justice Kabir in ya kama hanyar komawa cikin Zaria zuciyar shi duk ba da i,sai dai kafin ya bar garin ya bu aci a taimaka mishi da hoton Malam Kabiru in domin kuwa ya uduri niyyar sai ya nemo inda su ke a fa in duniya domin ya nemarwa ar shi yafiya ko hakan zai sa ta samu sa'ida da salama a cikin abarin ta. Bayan ya isa gida zama yayi a cikin falon shi tare da ri e kan shi lokaci guda ya fara tunanin hanyar da zai bi domin neman inda Malam Kabiru in yake, mi ewa tsaye yayi sannan ya fara zagaye cikin akin yana nazarin hanyar bi. auki tsawon lokaci yana kaiwa da komowa a cikin falon gidan nashi domin neman mafita kafin cikin ikon Allah wata zuciyar ta bashi shawarar kawai ya je gidan radiyo ya bayar da sanarwa sannan ya yi Albishirin tukwaici mai tsoka ga duk wanda ya gano inda Malam Kabiru da iyalin na shi su ke. Da wannan shawarar ya yi na'am sannan ya auki hoton Malam Kabiru in ya auka a wayar shi tare da iran wani layi ya sanar da mai layin abin da yake bu ata kafin kuma ya juya y a nufi hanyar barin falon domin zuwa gidan Radiyo Tafe yake a cikin motar shi duk tunanin duniya ya ishe shi dai-dai ya iso wajen danger ne aka tsayar da motar ta shi. Ganin cewa da goslow da yawa a gaban shi ya sanya shi kashe motar sannan ya kifa kan shi da sitiyarin motar. Har aka fara bayar da hannu motoci suka fara wucewa Justice Kabir bai san ana yi ba,nan fa motocin bayan shi suka shiga zabga mishi horn wasu cikin acin rai har sun fara fitowa daga cikin motocin su domin a tunanin su irin rainin hankali ne kawai irin na wasu masu motar. "Bawan Allah idan ba tafiya zaka yi ba ka kauce ka bamu hanya mu wuce?, Haba tun azu ka kasa gaba ka kasa baya ka tsaya mana a kan titi!". Muryar da Justice Kabir ya ji ta daki dodon kunnen shi ne ta sanya shi saurin ago wa tare da bu e baki da niyyar yin magana sai dai yin arba da mutumin da yake mishi maganar ta sanya ta shi maganar ma alewa inda ya kafe mutumin da ido cikin wani irin yanayi mai wuyar ganewa. Kallon da mutumi ya ga Justice Kabir in yana bin shi da shine ya sanya shi cika da mamaki kafin kuma ya jijjiga kai ya koma cikin motar shi yana ganin cewar kamar Justice Kabir ba mai lafiya ba. Saurin jan motar shi Justice Kabir ya yi tare da komawa gefe sannan ya sanya hannu ya akko hoton Malam Kabiru ya duba nan fa ya bu e motar da sauri ya shiga duban inda ya ga wannan mutumin ya nufa sai dai ya tarar har mutumin ya shiga motar shi ya tayar yana arin barin wajen , da sauri shima Justice Kabir ya koma cikin motar shi tare da bin bayan motar mutumin amma kuma sai dai sama ko asa ya nemi motar ya rasa ta ace mishi. Hankali tashe Justice Kabir ya shiga bin bayan motoci da gudu amma ko mai kalar motar mutumin bai gani ba. Hankali tashe Justice Kabir ya koma cikin motar shi sannan ya tayar tare da barin wajen ya na nufar gidan Rediyo in,shi kam duk da a hoto ya ga fuskar Malam Kabiru ko shakka ba ya yi wanna mutumin shine mahaifin Amrah. To amma ta ya hakan ta kasance tun da ya san a labarin da Amira ta bayar na Amrah ta sanar da su cewar iyayen Amrah talakawa ne to amma ya akayi yanzu kuma ya ga Malam Kabiru cikin shiga ta alfarma?. Amsar da Justice Kabir ya kasa samarwa kan shi Kennan har ya isa gidan rediyon zuciyar shi cike da tunani iri-iri. Yana isa gidan Rediyon ya sanar da su abin da yake tafe da su sannan ya basu hoton Malam Kabiru in tare da cewar duk wanda ya gano inda Malam Kabiru da iyalan shi su ke ya masa al awarin kyautar ku i har Naira Miliyan guda. Bayan ya gama komai ne ya fito daga cikin gidan rediyon sannan ya nufi motar shi da niyyar shiga sai dai kuma iran da ya shigo wayar shine ya sanya shi dakatawa tare da aukar number "Hello ya ake ciki ?". "Ranka ya da e na samo labarin inda mutumin yake yanzu haka yana Jahar Yobe a cikin garin Potiskum,a wata unguwa da ake cewa Tsohuwar kasuwa,dan haka duk sanda ka shirya sai ka mun magana na raka ka". Shine bayanin da aka yiwa Justice Kabir a cikin wayar aikuwa cikin zumu i da murna ya ce gobe za su wuce garin. Sai dai abin bada ya bashi mamaki to shi kuma wancan da ya gani azu fa waye?. Tambayar da ya kasa bawa kanshi amsa kennan. ***** Anwar tafe yake a cikin motar shi baka jin sautin komai a cikin motar face karatun Alkur'ani da yake tashi cikin zazza ar Muryar Sheikh Sudes cikin ira'ar sa mai sanyaya zuciya. Tun daga nesa yake zabga horn sakamakon kallon mace da yayi a tsakiyar titin tana tafiya cikin wanciyar hankali kamar ta samu cikin akin ta. Wani abin arin haushi da takaici shine bai wuce yadda Anwar yaga ta manna mishi ba duk irin Horn in da yake zabgawa in ta i barin kan titin ko a jikin ta balle ta nuna mishi ta san ma da wanzuwar hallitar shi a wajen. Sai da Anwar ya iso daf da ita kafin ya ja wani mahaukacin burki ko kashe motar bai yi ba ya bu e murfin motar ya fito a fusace ya fara magana. "Ke wace irin ar gadara ce kina tafiya a kan titi kamar kin samu titin gidan ku,ko an gayamiki cewar titi
Chapter 39 · 0% Book details