← Book details Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 45

Sashe 10

Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a hankali har ta isa bakin tagar akin wadda take ta waje. Hannu ta sanya ta bu e a hankali sannan ta fara arin haura window Wani security ne taga ya motsa sakamakon wayar shi da tayi ara ai take hanyar cikin ta ta ka a, bata tsaya wata-wata ba ta dir a windon ba tare da ta duba inda ta fa in ba. Dafe hannun ta tayi da taji ya zogi alamar ta kuje amma duk da haka bata dakata da abun da tayi niyya ba, haka ta mi e tsaye ta runtuma a guje ba tare da ta san inda take jefa afar ta ba. Gudu ta shiga tsulawa akan titin wanda yake shiru ba alamar motsin wata hallita,ko tsoron daren bata ji ba burin ta kawai bai wuce ta samu ta isa inda take son isa in ba lafiya, sannan ba tare da kowa ya ganta ba. Haka ta cigaba da gudu tana yi tana waiwaye ko wani yana biye da ita cikin ikon Allah kuwa ba wanda ya ganta ma bare ya biyo ta kasancewar dare ya tsala sosai. Idan kaga gudun da Amira in take zaka iya cewa ba da afafu take gudun ba saboda yadda take gudun kamar zata tashi sama, tsabar gudun da take in ko gaban ta bata kallo balle ta san inda take jefa afar ta. Ita dai burin ta da damuwar ta bai wuce ta gan ta a inda take da burin zuwa ba, domin kuwa ko damuwa da duhun daren bata yi ba kai kayi tunanin da rana ne tsaka take wannan gudun. *Manage it pls yau bana jin da i sosai ban ma yi zaton zan muku typing* *ba wallahi* *MANGA* _Comment_ _Share_ _Fisabillillahi_. *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA*: _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ . *Free book* ------------------------------------------- *Bissimillahir rahmani rahim* *009* ____________________________ Duk irin gudun da Amira take bata ji ko alamar gajiya ba balle kuma ta ji a ran ta wai ko zata tsaya. Tayi Gudu mai nisa kasancewar makarantar ta su a bayan gari take ya sanya bata samu damar arasowa inda take so in ba sai da ta auki tsawon lokaci tana wannan gudun. A dai-dai bakin wani gini naga taja tunga ta tsaya, a hankali kuma ta shiga mayar da numfashi ka an-ka an sannan naga ta aga kai ta dubi ginin inda ta kai duban ta kan rubutun saman ginin ashe ma police station ne. Tafiya ta fara yi cikin sauri har ta arasa bakin police station in inda ta shiga bubbuga ofar police station in da sauri da sauri kamar an aiko ta. Jin irin bugun da ake yiwa wajen ne ya sanya an sandan da suke aikin kwana a wajen saurin mi ewa tare da ciro bindigogin su sannan suka nufi bakin ofar wajen aya daga cikin yana furta. "Waye a nan wajen". Ya fa a yana saita bindigar a saitin inda Amira take tsaye. "Dan Allah ku taimaka ku bu ofar na zo ne domin naga DPO". Amira ta fa a cikin rawar murya. Jin muryar mace da an sandan suka yi ya sanya su saurin nufar bakin ofar amma duk da haka ba su mayar da bindigogin na su ba. arasawa bakin ofar su ka yi sannan suka bu ofar, ai suna bu ewa kamar abun da Amira take jira kennan ta fara arin ture su dan shiga cikin police station in ko tsoron bindigar hannun su bata yi ba. Cikin sauri suma an sandan suka ri e ta tare da hanka o ta waje har sai da ta fa asa, cikin fushi aya daga cikin an sanda ya dube ta sama da asa sannan yace. "Ai ni sai yanzu na lura ashe da mahaukaciya mu ke magana ban san ni ba, Kofur Audu ka kalle ta fa afa ko takalmi ba bu wai take i irarin ta zo ganin DPO, to ke an gayamiki cewar DPO in mutumin banza ne da zaki ebo dattin afafuwan ki da wannan tsakiyar daren wai kin zo ganin DPO, ko an gayamiki haka kawai ake zuwa kai tsaye a ce za'a ga DPO in? ". Ya fa a yana nuna afar Amira yadda ta yi bututu kamar an tono ta daga rami tare da fashewa da dariya. Shima ayan an sandan dariya ya fara sannan ya tako ya iso har inda Amira take yashe wadda tun da suka cillo ta waje bata mi e ba. "Ke mahaukaciya mai ya kawo ki nan wajen?". Ya fa a da alamar izgilanci domin kuwa su har ran su sun auka mahaukaciyar ce da gaske. Wani abu ne ya taho ya tokare wutan Amira saboda takaici amma kuma ta sanyawa ran ta in sha Allah duk wani rashin mutunci da zasu mata zata jure shi har sai ta aiwatar da abun da ta ta yi niyya. ewa tsaye tayi tare da karka e jikin ta sannan ta share hawayen takaicin da suka zubo mata tare da ara runtuma a guje ta hanka e su ta shige cikin police station in tana cewa. "Wallahi ni ba mahaukaciya ba ce, DPO dan Allah ka fito kana ina wallahi kai nake son gani". Amira ta fa a tana arasa shigewa cikin police station in tare da fara olawa Dpo ira. Wani an sanda ne ya fito daga cikin wani office sanye da Kayan an sanda sakamakon hayaniyar da ya ke ji in ya sa ya farka daga baccin da yake A dai-dai wannan lokacin ne kuma wa annan an sanda guda biyun suka araso wajen kamar an jefo su inda suka fara arin kama Amira za su sake fitar da ita. Ai Amira tana ganin haka ta nufi wannan an sandan da yake tsaye tare da ru ume shi tana cewa. "Yalla ai wallahi ni ba mahaukaciya ba ce, wallahi DPO na zo gani dan Allah ka taimaka kar ka bar su su fita da ni, idan kuma kai ne DPO in ka sanar dani na ganka". Amira ta arasa maganar tana ara ame shi domin kuwa ji take kamar wa annan an sandan za su fitar da ita waje. "Yalla ai ka gani ko wallahi wannan yarinyar mahaukaciya ce dan bana tantama cewar ba daga dawanau ta tsinko ta gudo ba". Cewar Kofur Audu in yana arin arasawa wajen Amira domin ya kamo ta ya fito da ita daga wajen. Hannu wannan an sandan ya sanya ya are Amira daga jikin shi wadda tun daga yanayin yadda ya ganta ya tabbatar da cewar ba a hayyacin ta take ba. Ai Amira tana ganin ya are ta daga jikin shi ta fashe da wani irin kuka sannan ta fara magana. "Dan Allah ka taimaka mun wallahi matu ar ban ga DPO a yau ba,rayuwa ta tana cikin matsala, dan Allah kar ka karo ni na rantse maka da Allah ina da hankali, wallahi mai hankali ce ni, dan Allah ka ha ani da DPO". Amira ta fa a tana zubewa a wajen tare da ame afafuwan wannan an sandan. Da sauri ya ago ta sannan ya kamo hannun ta tare da kai ta kan wata kujera ya zaunar da ita sannan yace. "Kin ga anmata ki nutsu, ki dawo hankalin ki sannan ki sanar da ni mai ke tafe da ke". Shiru Amira ta yi tare da kafe gefe guda da ido sannan ta fara arin yin magana amma sai gani aka yi jikin ta ya shiga rawa,inda ta shiga nuna musu wani dungu a cikin police station in tana zaro ido waje lokaci guda kuma ta sulale asa ta sume a wajen. Murmushi Amrah ta yi wadda take tsaye a dungun da Amira in ta nuna cikin wata irin mummunar siffa, ha oran ta za o-za o ga wani gashi da ya fito a duk wani sashi na jikin ta, hawaye take amma kuma hawayen jini kamar yadda ta saba kullum, cikin wata iriyar murya mai matu ar tsoro tace. "Kash!! Amira ban zo wannan wajen da niyyar cutar da ke ba, domin kuwa da kina daga cikin wa anda zan auki Fansa a kan su da ba zan bar ki har ki kawo wannan lokacin ba, ai ke baki cutar da ni ba kawai laifin ki aya da ki ka kasa fitowa ki yiwa duniya bayani a lokacin da aka cutar da ni aka jefa rayuwa ta cikin tashin hankali wannan shine kawai laifin da ki ka mun, dan haka ni ba zan cutar da ke ba sai dai nasan dole daman idan kin yi arba da ni ki tsorata". Amrah ta na kaiwa nan a zancen da take in wanda ita ka ai ta san mai take fa a ta yi wata irin girgiza sannan ta bi ta jikin ginin police station in ta fice daga wajen. Ganin wannan halin da Amira in ta shiga ya sanya wannan an sandan umurtar Kofur Audu da ya mi o mishi ruwa da gaggawa. Aikuwa ana kawo mishi ruwan ya eba a hannun shi tare da watsawa Amira a fuskarta. A firgice Amira ta farka tana sakin wani irin gigitaccen ihu tare da mi ewa da gudu zata fice daga wajen tana cewa. "Wallahi idan har ba ku yi gaggawar ha a ni da DPO ba ku ka bari har ta yi nasarar hallaka ni kamar yadda ta hallaka an uwana to tabbas alhakin mutuwa ta ya rataya a kan ku". Da sauri an sanda biyu nan suka kamo ta tare da zaunar da ita ganin da gaske fa ta fice a hayyacin ta. A wannan lokacin duk wani mai rai da yake kusa da cikin police station in sai da ya farka hatta wa anda suke cikin cell a rufe sai da suka farka suka tashi suka zazzaua, sakamakon ihun da Amira in take ba na wasa bane, inda wasu suka shiga le owa dan bawa idon su abinci gashi lokacin arfe uku har ta yi. Wayar shi wannan an sandan ya zaro sannan ya shiga contact in shi ya binciko wata number tare da yin dialing in ta. ***** A can Clinic in makarantar
Chapter 10 · 0% Book details