Sashe 2
Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
saura kwana uku biki an nemi amarya an rasa" Mom ta arashe maganar cikin karyewar murya. Shiru mahaifin Afrah yayi na wani lokaci kafin daga baya kuma yace. "Shikennan yanzu bara naje wajen an sanda na sanar da su". "Amma Alhaji ya kamata mu ira Anwar mu sanar da shi halin da ake ciki shima ya sani a matsayin shi na wanda zai auri Afrah in". Saurin dakatar da ita Mahaifin Afrah in yayi sannan yace "A'a ba za'a yi haka ba, yanzu ki bari muje wajen an sandan muji abun da zasu ce tukunna"ya fa a yana juyawa tare da nufar wajen motar shi, da sauri wani yayan Afrah wanda ake ira da Aliyu ya bi bayan shi. Gudun da Aliyu in yake a titin shi ya sanya basu wani auki tsawon lokaci ba suka isa police station Kai tsaye office in DPO suka nufa inda basu wani tsaya ata lokaci ba suka zayyane mishi abun da yake faruwa. Shima DPO in sosai atan Afrah in ya tsaya mishi a rai domin kuwa wannan abu da aure kai yake,a hankali ya ago kan shi yana juya biron da yake hannun shi sannan ya kalli su Aliyu in yace. "Amma ranka ya da e wannan auren da zaku yiwa arku da son ranta ne ko kuwa za in kune?". Wani murmushin takaici mahaifin Afrah in yayi sannan yace. "DPO meyasa kamun wannan tambayar?" "Ka fara bani amsar tambaya ta tukunna kafin ka jefa mun wata tambayar" Cewar DPO in yana kafe mahaifin su Afrah in da ido. "Tabbas da son ranta za'a yi wannan auren asali ma za in ta ne ba za in wani ba". Shiru DPO in ya sake yi kamar mai nazarin wani abu sannan ya dube su yace. "Shikennan Alhaji za ku iya tafiya mu kuma inshAllah zamu yi duk mai yiwuwa dan ganin mun nemo inda Afrah take,ina bu atar photon yarinyar taka idan kuna dashi ko a waya ne ku tura mun,sannan gidan ka ma ku kasance a cikin shiri domin kuwa a kowane lokaci binciken mu zai iya biyowa ta cikin gidan naku. Abu na arshe shine ina son ka bani address da kuma wasu information akan wanda Afrah zata aura shima zamu yi bincike a kanshi domin kuwa a halin yanzu ko kuma baku fice daga cikin suspect ba". Sosai mahaifin Afrah suka cika da mamakin maganar DPO in har ya bu i baki zai ce wani abu Aliyu ya dakatar dashi inda ya sanarwa da DPO in duk abun da ya bu ata game da Anwar Ranar gidan su Afrah kwanan zaune suka yi domin kuwa wa anda suka iya yin Bacci a cikin gidan alilan ne,kowa ka gani hankalin shi tashe yake. Washegari kuwa arfe takwas dai-dai iran wayar DPO ya shigo wayar mahaifin Afrah in a lokacin gaba aya an gidan suna hallare a cikin falon gidan sun yi tsumu-tsumu kamar an ji era a buta. Cikin sauri mahaifin Afrah in ya aga wayar gabanshi yana dukan uku -uku sannan yayi sallama. "DPO ya ake ciki fatan dai akwai wani sabon labari?". "Alhaji gamu a ofar gidan ka zamu iya shigowa".Fita Mahaifin Afrah in yayi sannan ya musu iso tun da ya isa inda suke fa uwar gaban shi ta tsanan ta sakamakon arba da wani abu da yayi an lullu e shi da wani farin yadi a ajiye a asa. "DPO ya ake ciki?" Mahaifin Afrah in ya jefawa DPO wannan tambayar cikin tsananin tashin hankali da rawar murya. "Alhaji mu shiga ciki tukunna domin kuwa maganar ba zata yiwu a nan wajen ba" Gaba mahaifin Afrah in yayi inda DPO ya umarci wasu an sanda guda uku da su akko wannan abun da yake lullu in sannan suka bi bayan shi suka shiga cikin gidan,a falon gidan suka yada zango inda suka ajiye wannan abun da ba wanda ya san meye a ciki. "Bisimillah DPO ga wajen zama" Mahaifin Afrah in ya fa a yana nuna musu kujera. "Alhaji ai zama bai kama mu ba tukunna, inspector jamil bu e musu wannan gawar su gani ko an dace" Daram gaban duk jama'ar cikin falon ya buga jin abun da DPO in ya fa a,ai basu ara tsinkewa da lamarin ba sai da suka yi arba da abun da yake cikin wannan zanin a lullu e,take wasu daga cikin mutanen falon suka dinga zubewa suna sumewa masu arfin halin cikin sune kawai suka tsaya a ihu kawai. *MANGA* _Comment_ _Share_ _Fisabillillahi_. *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ *SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION* *SADAUKARWA* : _Wannan book in gaba_ _ ayan shi Sadaukarwa_ _ne gareku Anty Hadiza D_ _Auta, Sis Adam Amira_ _Alkhairin Allah ya_ _kai muku a duk inda_ _ku ke ina son ku_ _fisabillillahi_ . *Free book* ---------------------------------------- *Bissimillahir rahmani* *rahim* *002* __________________________ Ba komai mutanen suka yi arba da shi ba wanda ya firgita su face arba da suka yi da gawar Afrah wadda idanunta duka biyu suke a ule, idan ban da shi babu wani abu da zaka kalla a jikin ta kace gawa ce domin kuwa babu ta inda aka bar alama ko shedar irin kisan da aka mata Ihu ne ya cigaba da tashi a cikin falon nan da nan kafin kace mai masu raunin zuciyar cikin su har sun fara yanakar jiki suna zubewa a asa suna sumewa, ciki kuwa har da mahaifiyar Afrah, masu dauriya da arfin halin su ne wa anda suka tsaya a kuka kawai, gaba aya falon ya hautsine baka jin komai sai iface-ifacen mutane. Duk yadda wannan Dpo in ya su ya sa mutanen falon su yi shiru abun ya gagara,da yar dai wasu suka an tsagaita inda Dpo in ya dubi mahaifin Afrah mai suna Alhaji Shareef yace. "Alhaji kuyi ha uri da abun da ya faru ku auki hakan a matsayin addarar ku,domin kuwa ita addara bama iya hanata aukuwa,duk yadda muka so mu kauce mata hakan ba zai ta a yiwuwa ba,sai dai mu rungume ta hannu bibbiyu ko da kuwa bata zo mana da da i ba" Dpo in ya arashe maganar cikin son ya kwantarwa da mahaifin Afrah hankali duk da kuwa ya san abu ne da kamar wuya. ago kai mahaifin Afrah yayi wanda idon shi suka ka a suka yi jawur sannan cikin sheshe ar kuka ya fara magana. "Yanzu Dpo da gaske ata ce Afrah a kwance a gabana?, innalillahi wa'innailaihi rajiun,wannan wace kalar BA ADDARA ce haka?, fisabillillahi mai Afrah ta aikata wanda ta cancanci wannan hukuncin?, Wallahi duk wanda ya aikata mana wannan mummunan aikin ba zamu ta a yafe mishi ba". Ya arashe maganar yana fashewa da kuka kamar wani aramin yaro. "Ahhh Alhaji Shareef abun da nake so da kai shine dan Allah kuyi ha uri a halin yanzu Afrah addu'ar ku kawai tafi bu ata, shi kuma duk wanda yake da hannu a cikin wannan aika-aikar inshAllah zamu yi iya bakin arin dan ganin mun gano ko waye kuma mun bi mata ha in ta". "Wallahi duk wanda ya aikatawa ar uwar mu wannan aikin zaluncin ba zamu ta a yafe masa ba, sannan ko waya sai mun yi Shari'a da shi matu ar aka gano shi" Cewar Aliyu yayan Afrah. A dai-dai wannan lokacin ne kuma Anwar saurayin Afrah da zata aura ya fa o cikin falon kamar an jaho shi,kallo aya zaka yiwa fuskar shi ka hango tsantsar tashin hankalin da yake kwance a kanta. Da gudu ya arasa kan gawar Afrah in da take shimfi e a tsakar falon inda ya zuba duka gwaiwowin shi a saitin ta,kamar wani zauttace haka ya fara magana. "Afrah wana marar imani da tausayin ne ya aikata miki wannan anyen aikin?, Afrah meyasa za'a raba mu?, Afrah meyasa zaki tafi ki barni?, Kai! arya ne Afrah ki tashi nasan kina jina kuma nasan baki mutu ba, Afrah dan Allah ki tashi ki gayamana wanda ya aikata miki wannan aika-aikar" Anwar ya arashe maganar cikin sakin wani kuka mai ratsa zuciya ga fuskar shi duk ta aci da hawaye da majina. DPO in ne ya arasa inda Anwar yake tsugune sannan ya dube shi cikin tausayawa ya fara magana. "Haba mana aboki na be a man mana,ya zaka zauna kana kuka kamar wata mace, common share hawayen ka dan Allah,ka sani kamar yadda na muku al awari inshAllah zamu yi iya bakin arin mu dan gano wanda yake da hannu a cikin wannan kisan". DPO in ya arashe maganar cikin arfafa gwaiwa. Hannu Anwar ya sanya ya share hawayen da suka ata mishi fuska sannan ya dubi DPO in yace. "DPO dole nayi kuka domin kuwa an cuce ni matu ar cutarwa, DPO wannan wana irin zalunci ne ace sai ana saura kwana uku aure na a kashe mun mata,ai kuwa kaga kuka ya zama dole, Allah ya ji anki Afrah, Allah ya tona asirin duk wanda ya miki wannan aika-aikar". A dai-dai wannan lokacin ne kuma mahaifiyar Afrah ta farka daga suman da tayi in,inda ta farka da wani razannannen ihu ta koma kamar wata ta iya ta dinga wani irin fisge-fisge tana wasu irin surutai marrassa kan gado. "Ku yale ni in je wajen ata wallahi arya kuke mun ata bata mutu ba bacci take", Haka ta dinga fa a inda daga baya sai ta koma daga ta yi kuka sai kuma tazo ta kwashe da wata irin dariya irin dai ta mahaukata sabon kamu,da yar aka shiga ri e ta tana fisgewa duk wanda yake cikin falon sai da ta bashi tausayi, da yawa sai suka daina kukan mutuwar Afrah suka koma kukan tausayawa mahaifiyar ta. Waya DPO ya aga inda ya ira ma'aikatan asibiti akan su zo su wuce da gawar Afrah mutuary har sai an kammalla bincike, lokacin da ma'aikatan lafiyar suka araso sai da likita ya ara duba Afrah inda ya ara tabbatar mu su da cewar Afrah fa ta riga mu gidan gaskiya. Ita kuwa mahaifiyar Afrah sai da aka mata allurar bacci wai dan ta yi bacci amma kamar wanda aka ara kunnata haka wannan allurar ta maidata.wani tashin hankali ma sai da aka zo fita da gawar Afrah a nan ne fa aka kafa sabuwar sumewa daga wajen anne da yayun Afrah in ita kuwa mahaifiyar ta