← Book details Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 45

Sashe 13

Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru Inspector Rasheed ya yi ina sauraran abun da ake fa a mishi a cikin wayar kafin daga bisani naji yace. "Ok to shikennan ku barta a wajen kar ku barta ta tafi ina zuwa nima akwai ar wata matsala ce da ta ta so in sha Allah idan na shawo bakin ta zan shigo zuwa nan da asubah, amma kasan DPO a wannan lokacin ko ka ira shi ba samun wayar shi zaka yi ba,so kar ka ira shi ka bari mu ga zuwa safiya". Inspector Rasheed ya fa a, ban ji abun da aka ce mishi a aya angaren ba sai ji nayi yace. "Ok to shikennan duk yadda zaku yi dai kar ku yale ta ta tafi". Yana kaiwa nan a zancen na shi ya katse wayar sannan ya juya ya dubi mahaifiyar Amira da har a wannan lokacin bata daina kukan da take in ba. "Uhmm Mama dan Allah ki daina wannan kukan kiyi ha uri in sha Allah daga yanzu zuwa safiya zamu yi duk arin da zamu yi domin ganin mun gano wanda yake da hannu a wajen atan Amira in". arashe maganar cikin sigar rarrashi. "Yalla ai ni wallahi a yanzu bu ata ta ko gawar Amira na kalla domin kuwa na tabbatar i zuwa yanzu sun da e da hallaka ta,na tabbata ba zasu yale ta ba itama kashe ta zasu yi kamar yadda suka kashe sauran an uwan ta, Allah ya ji anki Amira ya saka muku a kan duk wanda yake aikata muku wannan zaluncin". Mahaifiyar Amira ta fa a tana dur ushewa a wajen sakamakon kukan da yaci arfin ta. Shikam Inspector Rasheed rasa abun da yake mishi da i yayi wannan bala'in har yaushe, tabbas duk wanda suka kama da hannu a wannan aika-aikar ba zasu mishi da da i ba,har ya hango irin hukuncin da za'a zartar mishi. yar dai ya lalla a mahaifiyar Amira ta tashi daga wajen sannan suka sanya ta a mota suka mayar da ita gidan ta. ***** Lokacin da suka mayar da ita gidan nata har asubah ta kawo kai domin kuwa a lokacin har arfe biyar ta yi dan haka suna kai ta gidan nata suka dawo wani massallaci da yake an gaba da gidan ka an suka gabatar da sallar asubah kafin suka mi e suka nufi police station Shigar su cikin police station in ne suka yi arba da abun da ya yi matu ar ba su mamaki. Amira suka gani a zaune a bakin kanta ta kafe ofar shigowa cikin police station in da ido ko iftawa bata yi. Wata zabura Kofur Bala yayi ya ma ale a bayan Inspector Rasheed yana furta. "Yalla ai Fatalwa, innahu min sulaimanu wa innahu bissimillahir rahmani rahim ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba, yalla ai ka ga abun da idanuna suka gane mun kuwa". arashe maganar yana ara shigewa jikin Inspector Rasheed in domin kuwa shi har ran shi yayi tunanin Fatalwa ce kuma yayi tunanin shi ka ai yake ganin Amira Tsawar da Inspector Rasheed in ya buga mishi ne ta dawo dashi daga haukar da yake "Wai kai Kofur Bala mai yasa wani lokaci lamarin ka sai a hankali ne, yanzu fisabillillahi ina Fatalwar take a wannan wajen?, Ko kuma an ce maka ita wannan in gawa ce?, Kuma wai a hakan kana i irarin kai jami'in an sanda ne ko?, Dallah ni malam sakar mun kaya". Inspector Rasheed ya fa a yana are hannun Kofur Bala in daga jikin shi. A sannan ne kuma wa annan an sandan suka fito daga wani aki alamar salla suka yi. "Inspector Rasheed har kun iso kennan?". Da sauri Inspector Rasheed ya arasa wajen shi yana ri o hannun shi suka nufo wajen da Amira take raku e sannan ya fara magana fuskar shi da alamun mamaki. "Asp Sadiq a ina ku ka samo wannan yarinyar?". Murmushi Asp Sadiq yayi sannan ya nuna Inda Amira take yace. "Wannan ai ita ce yarinyar da na ira ka a kan ta wadda na sanar da kai cewar ta zo tana son ganin DPO". Wata doguwar ajiyar zuciya Inspector Rasheed ya sau e tare da furta godiya a Ubangiji a fili. Kllon shi Asp Sadiq ya yi fuskar shi da alamar tambaya sannan yace. "A'a ya naji kana sau e numfashi haka ko dai ka santa ne?". "Tabbas kuwa na santa, ina case in da yake hannu na na wa annan anmatan da aka kashe har guda uku a jami'ar Ahmadu Bello?". Inspector Rasheed ya fa a yana kafe Asp Sadiq da ido. warai kuwa na gane,kar fa kace mun wannan yarinyar tana da hannu a cikin wannan kisan da ake yi in?". arashe maganar cikin zaro ido waje. "Ko ka an ba hannun ta a ciki asali ma yanzu haka rayuwar ta tana cikin ha ari domin kuwa gaba aya wa anda aka kashe in tana da ala a ta kusanci sosai da su,idan ka yi duba da irin zazzafan amintar da take tsakanin su ba wanda bai san irin awancen na su ba,yanzu haka maganar da nake maka mahaifiyar ta tana can hankali a tashe a tunanin ta an kashe mata a kamar yadda aka kashe sauran abokanan ta, to amma abun da ya bani mamaki shine mai ya kawo ta police station in?". Inspector Rasheed ya fa a yana kai duban shi inda Amira take raku e wadda har a wannan lokacin idanun ta ba su daina zabur da hawaye ba. "To gaskiya ni dai ban ba zance maka nasan takamaiman abun da ya kawo ta nan ba domin kuwa lokacin da ta zo ta sanar da mu kawai ita Dpo take son gani". Shiru gaba aya suka yi kafin a hankali Inspector Rasheed ya arasa wajen Amira da take ta rarraba idanu kamar a ce mata firit ta ruga da gudu. "Amira". Inspector Rasheed in ya ira sunan ta yana mai tsugunawa a kusa da ita. ago ido Amira ta yi ta kafe shi da ido ba tare da tace uffan ba. "Amira kina jin yunwa a kawo miki abinci". Saurin jijjiga mishi kai ta yi, wanda sai a wannan lokacin ta samu damar yin magana cikin rawar murya tace "A'a bana son in ci komai, dan Allah bu ata ta nidai kawai ku ha ani da DPO saboda nasan wallahi nima ta kusa kashe ni, nasan ba zata bar ni ba kashe ni zata yi dan haka tun kafin lokaci ya ure ku ha ani da DPO domin na bayyana mishi wata oyayyar gaskiya wadda burin ku shine ku gano ta". arashe maganar cikin sakin wani irin marayan kuka. "Kin ga Amira ki nutsu in sha Allah ba wadda zata kashe ki, yanzu ki nutsu ki sha ruwa sannan kimun bayanin abun da yake tafe da ke". Inspector Rasheed ya fa a yana tsiyayo ruwa a cikin wani kofi da Kofur Bala ya kawo mishi sannan ya mi a mata. ar ruwan Amira ta yi amma bata sha ba sai ma kafe ruwan da ta yi da ido sannan ta ago kai daga bisani tace. "Ina mahaifiya ta?". Kallon ta Inspector Rasheed yayi cike da mamaki kafin daga bisani yace. "Mahaifiyar ki tana nan cikin oshin lafiya tana gida". an shiru ta yi kafin tace. "Ina son kafin na sanar da ku abun da ya faru dan Allah ina son na nemi wata alfarma daga wajen ku". "Ok to shikennan ki fa a in sha Allah za'a miki ita". "Ina son dan Allah a ira iyayen su Afrah da Azra da Anisa da kuma Anwar domin a gaban su ne ka ai zan iya bayyana irin mummunar aika-aikar da an su suka aikata har yake bibiyar su". Kallon Asp Sadiq Inspector Rasheed yayi sannan kuma daga bisani ya mayar da kallon shi kan Amira yace. "Meyasa sai a gaban iyayen su zaki iya sanar da mu abun d a yake faruwa?". "Saboda hakan ne kawai zai wanke musu ra in kisan da aka yiwa an su, sannan kuma hakan zai sa su gane cewa kowane abu aka yiwa an su su suka janyo, kuma hakan zai sa su daina ganin laifin wanda yake kashe mu su an su daga haka sai su koma ganin laifin an su domin kuwa ko mai ne su suka janyo wa kan su, idan da hali ma ina bu atar a gayyato an jarida da kuma hukumar makarantar mu domin a samu a ya a labari a duniya ko hakan zai sa masu son zuciya irin ta su su shiga hankalin su". Mamaki ne ya kama su Inspector Rasheed inda suka shiga kallon-kallo da kuma mamakin kalaman Amira Duban agogon hannun shi Inspector Rasheed inda ya ga har afa shiga ta gota sannan ya dubi Asp Sadiq yace. "Asp bari naje gida na yi wanka daga can zan biya ta gidan iyayen yaran can dan na sanar da su ko zasu samu damar zuwa dan mu ji abun da yake tafe da wannan yarinyar". Inspector Rasheed ya fa a yana mikewa daga tsugunen da yayi da sauri Asp Sadiq ya dube shi yace. "Ai nima tare zamu wuce domin kuwa kaga jiya ban kwana a gida ba, wallahi wasu yara aka kawo wanda yasa dole aka irani na zo to kuma na zo kennan ban da e ba wannan yarinyar ta zo ta". Asp Sadiq ya fa a yana bin bayan Inspector Rasheed in inda su kuma sauran an sandan suka tsaya jiran ma su aikin safe su zo su kar e su suma su tafi. Sai da Inspector Rasheed ya fara biyawa ta gidan su kasancewar ba shi da aure, wanka ya fara yi kafin ya fito ya je part in mahaifiyar shi inda ya same ta zaune ta kammalla ha a breakfast. Waje ya nema ya zauna a gefen ta kafin ya shiga gaishe ta. Amsawa tayi sannan ta dube shi tace. "AbdulRasheed naga kwana biyu wannan case in da ka ke gaba aya ya sa ka fara fita a hayyacin ka, ni dai dan Allah abun da nake so da kai kuma wanda kullum na sha fa a maka shine ka kula kuma ka ri e gaskiya da amana kar a baka ku i ko wani abu wanda
Chapter 13 · 0% Book details