← Book details Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 45

Sashe 14

Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zai sa ka danne ha in mai gaskiya har ka bawa marar gaskiya gaskiya, sannan addu'a kullum ina fa a ma addu'a ita ce jagaba a komai idan har ka ri e addu'a to tabbas ka ri e babban makami wanda zai kare ka daga dukkan wani sharri dan haka ka kula kaji". Sosai maganar mahaifiyar ta shi ta shige shi inda ya dube ta yace. "In sha Allah Ummu kamar yadda kika sanni a da to ba zan ta a sanjawa kuma addu'a ina kan yin ta zan kuma cigaba da yi in Allah yarda". Bayan sun gama cin abincin addu'a ta mishi sosai kafin kuma ya mi e ya mata sallama, lokacin arfe takwas da rabi sannan ya fita, duk da irin baccin da yake ji amma haka ya fita, kai tsaye gidan su Afrah ya fara nufa. A dai-dai bakin gate in gidan su Afrah in suka ci karo da mahaifin ta da kuma yayan ta Aliyu sun fito zasu tafi wajen aiki. Gaisawa suka yi da Inspector Rasheed in cikin sakin fuska kafin Inspector Rasheed in ya dubi mahaifin Afrah in ya fara mishi bayanin abun da yake tafe da shi an shiru suka yi daga mahaifin Afrah in har yayan nata kafin daga bisani kuma mahaifin Afrah in ya ago ya dubi Inspector Rasheed in yace. "To amma Inspector a ganina meye dalilin yarinyar na ganin dole sai a gaban mu zata sanar da komai?". "To Alhaji nima abun da na kasa fahimta Kennan amma ina ganin ku yi ha uri mu je idan ya so mu ji abun da yake tafe da ita in". "To Shikennan Inspector bari na shiga na sanar da mahaifiyar ta sai ta shirya mu wuce". "To ni dai yanzu idan kun shirya kwa same mu a can police station in domin kuwa yanzu haka ma zan wuce gidan sauran iyayen yaran ne". Inspector Rasheed ya fa a yana juya sannan ya shiga motar shi ya nufi gidan su Anwar bayan ya kar i address in shi a wajen Aliyu. Lokacin da ya je wajen Anwar in bai wani samu damuwa dashi ba, haka a angaren mahaifin Anisa ma inda shima yace zasu shirya su biyo su daga baya. Daga gidan su Anisa gidan su Azra ya nufa sai dai bai tarar da mahaifin ta a gida ba inda mai gadin gidan ya sheda mishi cewar ya tafi office, wayar shi ya ira amma bai aga ba dan haka kawai ya yanke shawarar ya je ya same shi a office Hakan kuwa aka yi inda ya nufi office in Justice Kabir in, bai wani samu matsala wajen ganin Justice Kabir in ba sai dai kuma inda gizo ke sa ar shine Justice Kabir ya daga tsallen aradu yace. "Ni ai daman na san wallahi makashin ata a cikin shegun yaran nan yake,watau sai da ta bisu aya bayan aya ta kashe su tukunna zata wani kai kan ta police station in ai cuta kam an riga an gama cutar mu, dan haka wallahi itama ta shiryawa kar ar nata hukuncin dan kar ta ga ta kai kan ta police station ta yi tunanin cewar hakan zai sa a sassauta mata hukunci, to ba zai yiwu ba wallahi sai ta tafi inda ta aika mun ata". Shi dai Inspector Rasheed ha uri ya bashi sannan ya lalla a shi suka tashi suka nufi police station A zazzaune suka tarar da kowa ya hallara a office in DPO in su kawai ake jira, ga Amira kuma a zaune a gefe ido yayi jawur tun da suka shiga cikin office in DPO in mahaifin Azra yake jefawa Amira mugun kallo ji yake kamar ya sha e ta ta mutu. Gyaran murya DPO yayi bayan kowa ya nemi waje ya zauna sannan yace. "To yanzu dai Alhamdulillahi mun hallara kamar yadda malama Amira ta bu ata dan haka muna sauraran ki shin mai yake tafe dake?, ga dai iyayen yaran da aka kashe nan a gefe suna sauran ki, ga kuma an jarida kamar yadda ki ka bu ata su ma sun zo, ga wasu daga cikin hukumar makarantar ku su ma sun samu damar halartar wannan wajen, kowa ya baza na zumaye da na mujiyar shi yana sauraran abun da zaki fa DPO ya fa a yana mai zuba idon shi a kan Amira. ago jajayen idanun ta ta yi tare da sanya hannu ta share hawayen da suka zubo mata sannan ta fara magana cikin kuka. A dai-dai sannan kuma an jarida suka saita camera in su da abun aukar sauti a dai-dai fuskar Amira *MANGA* _Comment_ _Share_ _Fisabillillahi_. *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ *SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA*: _Wannan book in gaba ayan Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ . *Free book* --------------------------------------------- *Bissimillahir rahmani rahim* *011* ____________________________ A hankali Amira ta ago fuskarta sannan ta fara magana. "Kamar yadda na fa a in sha Allah a yanzu zan sanar da duniya irin cin amanar da aka aikatawa Amrah, tabbas an ci amanar Amrah wadda duk wata mace da aka mata haka an jefa rayuwar ta a cikin tashin hankali inda za'a ja mata tsana da yara daga wajen al'umma, Azra, Afrah,da kuma Anisa sun kasance mutane da zamu iya iran su da green Sneak, su in azzalumai ne ma su bala'in son kan su, ina son kafin na fara baku labarin gaskiyar abun da ya faru ku auki kan ku ku sanya a matsayin Amrah shin idan ku ne wane irin hukunci zaku aikatawa wanda ya aikata muku irin wannan aika-aikar da aka aikatawa Amrah?, Kasancewar Amrah macece wadda bata iya oye sirrin ta ga wa anda suke tare ba wannan ya sanya babu abun da bamu sani ba game da labarin rayuwar Amrah hakan shi ya bawa su Azrah damar cutar da ita domin kuwa sun yi amfani da irin matsayin mahaifin ta da kuma yadda suka fahimci cewar kaf iyayen su sun fi na Amrah rufin asiri wannan ya sanya ba suji shayin su tarwatsa mata rayuwa ba.Da farko dai bari na fara sanar daku labarin wacece Amrah?, da kuma su waye Azra?, Da kuma irin zaluncin da aka aikata mata duk kuwa da cewar nima ina da kamasho a wajen lalacewar farin cikin Amrah duba da yadda na san gaskiya amma na kasa bayyana ta a lokacin da ya kamata har na bari azzalumai suka yi nasara a kanta, na tabbata idan ku ka ji abun da aka aikata mata daga haka zaku ara tabbatar da cewa an cuce ta cuta mafi girma da za'a yi duk wani an Adam. *FLASH BACK* *Wacece Amrah* *?* Asalin sunan ta Amrah Kabir ar asalin garin Giwa da ke aramar hukumar Zaria a jahar Kaduna, mahaifin Amrah babban malami ne da ba wanda bai san shi a cikin garin na Giwa ba har ma da wasu angare daga cikin jahar Kaduna an san shi, sai dai su in talakawa ne wanda rufin asirin Allah ne kawai yake ri e da su. Tun tasowar Amrah Allah ya sanya mata son karatun boko inda bata da wani buri wanda ya wuce ta ga ta zama cikakkiyar likita. Mahaifiyar Amrah ta rasu tun a wajen haihuwar Amrah in Allah ya mata rasuwa to sai Amrah ta ta so a wajen matar mahaifin ta mai suna Sa'adatu sai dai kuma Amrah ta yi dacen kishiyar mahaifiya domin kuwa gwaggo Sa'adatu macece mai kyakkyawar zuciya kuma ta ri e Amrah tsakani da Allah kamar ita ta haife ta a cikin ta,Amrah tana da yayu maza guda uku aya uwar su aya uban su aya sauran kuma an gwaggo Sa'adatu ne, Hashim,Umar, Sai kuma Usman su ne yayun Amrah in. Mahaifin Amrah mutum ne da mutane suke ganin mutuncin shi da girman shi a cikin garin Giwa in kasancewar shi malami babba kuma ga dattako, gashi shi mutum ne da baya iya danne ha an shi duk abun da an shi suka nuna suna so yana musu matu ar abun bai kaucewa Shari'a ba,sa anin wasu iyayen da zaku ga basa iya baiwa an su dukka ha in da ya rataya a wuyan su inda zaku ga wasu iyayen suna nuna ai kamar su ka ai su ke da ha i akan an wanda hakan kuma babban kuskure ne da wasu iyayen suke aikatawa dalilin haka sai kuga an zo an haifi a marar ido. Da gudu ta shigo cikin gidan fuskar ta kana gani kasan ba aramin farin ciki take ciki ba, tana shigowa ta fa a kan cinyar gwaggo Sa'adatu wadda take zaune a tsakar gida tana gyaran kayan miya. "To allani hankalin ki ya kwanta kin ji Amrah, ni wallahi ban san sai yaushe zaki girma ba,mutum yana girma kullum kamar ana mai da shi baya, ni aga ni dan Allah kar ki arasa ni". Gwaggo Sa'adatu ta fa a tana ture Amrah daga jikin nata. Shagwa e fuska Amrah ta yi sannan tace. "Gwaggo wallahi yau ina cikin farin da ban ta a shiga ba". Ta fa a tana ware wata paper da take hannun ta. "Gwaggo wannan result in mu ne na Waec and Neco ya fito duka na cinye ina da nine credit, yanzu saura na jamb zamu jira muga abun da Allah zai yi". Murmushi gwaggo Sa'adatu ta fa a fuskar ta dashi sannan tace. "Ai ni daman ban ta a kawo miki fa uwa ba Amrah kawai dai kece kike ta abun ki, Ubangiji ya sanyawa wannan sakamakon albarka". "Ameen ya Allah gwaggon mu kice mun kusa mu samu likita a gidan na mu". Yaya Hisham ya fa a da yake arasa shigowa gidan yanzu. "Wallahi kuwa Hisham ga dai result ya fito Alhamdulillahi sai kuma mu jira wancan ayan jan yake ko meye ma?". Gwaggo Sa'adatu ta fa a fuskarta tana fa a da Murmushi. Dariya muka yi gaba aya nida yaya Hisham kafin kuma nace. "Kai gwaggo Jamb fa ake cewa dan Allah meye kuma wani jan kamar a auye". Hira muka an ta a kafin kuma lokaci guda su lura da fuskata da ta sanja idanuna suka ciko da hawaye. "Subhannallah Amrah mai ye kuma
Chapter 14 · 0% Book details