Sashe 11
Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
su Amira kuwa bacci mahaifiyar ta take ba ta san abun da yake faruwa ba sakamakon yadda baccin na ta ya yi nisa duba da yadda kwanakin biyun nan bata samun rintsawa, yau in ne kawai ta samu ta rintsa da yawa har haka. Can wajen arfe uku kamar wanda aka zabure ta, ta farka firgigit sakamakon wani mummunan mafarki da ta yi, inda taga Amira in a cikin wani mummunan yanayi. Wannan mafarkin ba aramin aga mata hankali ya yi ba inda ta farka cikin sauri tare da mi ewa zaune tana kai duban ta kan gadon da Amira in take kwance. Kasancewar wutar lantarkin akin a kunne take shi ya bata damar hango gadon da Amira in take kwance wanda yake wayam ba alamar mutum a kai. Daram gaban ta ya bada wani irin sauti mai ara lokaci guda kuma ta dafe irjin ta tare da mi ewa tsaye tana furta. "Innalillahi wa'innailaihi rajiun mai nake gani haka!, Ina Amira ta shiga kuma?". Ta fa a tana nufar hanyar toilet dan dubawa duk kuwa da cewar bata ga alamun cewar akwai mutum a cikin toilet in ba. Sai da ta fara wasa ofar sannan ta fara ira sunan Amira "Amira kina jina kuwa". Ta fa a tana kasa kunne a jikin ofar ko zata ji alamar motsin mutum, sai dai shiru ba alamar da mutum a cikin toilet Tura ofar tayi inda ta shiga cikin toilet in sai dai wayam ba alamar cewa ma wani ya shiga cikin toilet "Hasbunnallahu wa ni'imal wakil innalillahi wa'innailaihi rajiun" . Su ne kalmomin da suka shiga fitowa daga bakin mahaifiyar Amira in wadda hankalin ta ya yi masifar tashi, lokaci guda kuma ta ji wata irin hajijiya tana shirin kwasar ta, da sauri ta dafe jikin bangon toilet in sannan ta fara sulalewa a wajen tana yin zaman an bori. Wasu hawaye ne masu zafi suka shiga biyowa ta kuncin ta cikin kuka ta fara magana. "Shikennan abun da na da e ina gudu ya faru ya faru!, Shikennan Amira kema sun kashemin ke!, Ai ni daman tun da naga an kashe aminan ki jikina ya ban ba za'a yale mun ke ba, innalillahi wa'innailaihi rajiun, yanzu wannan wana irin tashin hankalin ne hak, yanzu wana la'annanne ne yake bibiyar ku aya bayan aya shin mai ku ka aikata mishi haka?". auki tsawon lokaci a zaune a bakin ofar toilet in kafin wata zuciyar ta ce mata. " _Kinga zama bai kama ki ba, kamata ya yi ki tashi ki fita ki duba waje ko Allah zai sa ki ganta_ ". Aikuwa tana kaiwa nan a zancen zucin nata ta mi e da sauri sannan ta fice daga cikin akin, Kasancewar dare ne ya sanya bata ha u da kowa ba a filin makarantar. Kai tsaye bakin gate ta nufa inda taje ta tarar da jami'an tsaro a tsaitsaye kamar masu jiran ko ta kwana. Tun da Inspector Rasheed ya hango mace ta nufo inda suke in cikin sauri kamar zata kifa da bakin ta jikin shi ya bashi ba lafiya ba. Gaba aya jami'an tsaron ido suka zuba mata suna jiran su ji da wacce ta zo. Tana isowa wajen ta fashe da kuka sannan ta bu i baki cikin rawar murya ta fara magana. "Yalla ai sun sace Amira na tabbatar da cewa a yanzu sun riga da sun hallaka ta kamar yadda suka hallaka sauran an uwan ta, yalla ai ku taimaka dan Allah nikam ko gawar ta a kawo mun na ganta kaf.......". Kasa arasa maganar ta yi sakamakon wani kuka da ya ci arfin ta. Dafe kan shi Inspector Rasheed yayi cikin tsananin tashin hankali, anya kuwa makashin an mata nan mutum ne?, Idan kuwa har mutum ne to tabbas a cikin makarantar nan yake rayuwa, domin kuwa abun shikam ya fara bashi tsoro ya za'a yi a ce suna tsaye a wajennan ko rintsawa ba su samu damar yi ba amma ace an shiga har cikin Clinic in an kashe yarinyar, to amma yanzu kana da tabbacin an kashe ta in ne?, Wata zuciyar ta jefa mishi wannan tambayar. Aikuwa cikin sauri ya kawar da tunanin da yake sannan ya juya ya dubi mahaifiyar Amira in da take dirzar kuka kamar ran ta zai fita yace. "Kin ga ki nutsu ki mun bayanin abun da ya faru da Amira in". Goge hawayen ta tayi tare da sanya bakin hijab in ta ta fyace majinar da ta zubo mata sannan ta fara mishi bayani tun daga farkawar da tayi bata ga Amira in ba har zuwa yanzun da take tsaye a gaban su. Hankalin jami'an tsaron wajen ba aramin tashi yayi ba, musamman Inspector Rasheed. Har ya bu i baki zai yi magana sai kuma ira ya shigo wayar ta shi, ganin wanda yake iran nashi ya sanya ya yi saurin aga wayar tare da karawa a kunnen shi. *MANGA* _Comment_ _Share_ _Fisabillillahi_ . *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ *SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA*: _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_. *Free book* ------------------------------------------- *Bissimillahir rahmani rahim*