← Book details Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 45

Sashe 27

Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta a cikin makarantar daga malamai har alibai burin kowa shine yayi mu'amala da Amrah saboda arin ta da kuma kewawan halayen ta,sunan clique in su Khadijah shine IRON LADIES ko Zafafa shida. A lokacin da clique in su Khadijah suka samu labarin abun da ya faru da Amrah sai da suka auki videon suka ara reposting a Instagram da Twitter sannan suka dinga jin kamar su zuba ruwa a asa su sha. ***** Allah Sarki a angaren Anwar kuwa bai san abin da yake faruwa ba kasancewar shi ba ma'abocin hawa social media sosai ba, domin kuwa shi Whatsapp ma kawai yafi yi Whatsapp in ma ba wani sosai ba. Hakan ya sanya ko Amrah bai barta ta bu e shafuka a social media ba iya Whatsapp itama ya amince mata take yi. Kuma daman itan ma ba wata ma'abociyar son chatting in bane sosai ba, yawanci idan ka ganta a Whatsapp to group in class in su ta shiga ko kuma irin suna da online class in nan haka, ko kuma Anwar ya ce ta hau su yi video call. Kwance yake a cikin akin shi yana danne-danne a cikin Computer in shi, akwai research in da yake yi. Bugo ofar akin nashi da aka yi aka shiga da arfi ne ya sanya shi saurin ago kai ya kalli wana mai anyen kan ne haka. anin shi ya gani tsaye mai suna Nazir yana ri e da waya jikin shi sai rawa yake. Kallo aya zaka mishi ka fahimci tsantsar tashin hankalin da yake ciki sannan ka gane cewa akwai wani babban al'amari da ya aga mishi hankali "Subhannallah Nazir lafiya kuwa?". Anwar ya fa a yana mi ewa tsaye tare da rufe Computer in sannan ya sa o daga kan gadon. A dai-dai wannan lokacin kuma mahaifiyar shi itama ta fa o cikin akin kamar an jeho ta. "Ina kuwa lafiya, Anwar kai daman ashe karuwa kake shirin auro mana ka kawo mana ita cikin gidan nan bamu sani ba?". Da sauri Anwar ya dubi mahaifiyar tashi cike da mamakin maganar tata sannan yace. "Mama bangane karuwa ba!, wacece karuwa in?". "Eh dole kace haka mana tun da an mana rufa-rufa ana arin aba mana karuwa a cikin zuri'a, to wallahi anyi wal iya mun gano halin kowa munafukai kawai, in dai ina numfashi a doron asa wallahi ba zaka ta a auren wannan tsinnanniyar yarinyar ba,karuwa wadda ta gama tallatawa duniya jikin ta, kai ko bayan raina ne ban amince daka auri wannan yarinyar ba". Wani irin sarawa Anwar yaji kan shi yayi lokaci guda ya dafe kan sannan ya fara takawa a hankali ya arasa wajen mahaifiyar tashi sannan ya dube ta yace. "Mama wallahi kin sanyani a duhu, gaba aya maganganun ki sun kulle mun kai, Mama dan Allah ku fitar dani haske". Kallon shi sama da asa mahaifiyar tashi tayi irin kallon ka raina mun hankali ma tukunna tare da jan tsaki sannan tace. "Kai Anwar ka kalleni da kyau shekaruna hamsin a duniya dan haka,kar kayi arin wasa da tunani na ka nuna mun cewar baka san abun da yake faruwa ba,to ni dai na fa a maka wallahi ba Amrah ba ko uwar ta ce, kai zuri'ar su Amrah ma baka isa ka nemi aure a cikin ta ba, shima uban nata ashe munafuki ne kwanta-kwanta ya yiwa mutane ya sanya ake masa kallon allaramma har yake jagorantar mutane ashe munafuki ne, to wallahi Allah ya tona musu asiri, kuma ku in mu da suka ci wallahi biyar ba zamu bar musu ba sai sun biya komai ko na maka su a kotu" Tana kaiwa nan a zancen ta ta fice a cikin akin tare da banko ofar kamar zata karyata,ta bar Anwar a tsaye cike da al'ajabin wannan ba on lamari. Bayan fitar mahaifiyar ta su daga cikin akin daga Anwar har anin nashi rasa wanda zai yi magana aka yi, sun auki tsawon lokaci a haka kafin dai Anwar ya tattaro duk wani arfin hali da ya rage mishi sannan ya taka a hankali har ya arasa gaban Nazir sannan ya fara magana cikin sanyin murya. "Nazir ka mun bayani mai yake faruwa?, Jikina ya riga da ya gama bani cewar ba lafiya ba". Wayar hannun shi kawai Nazir ya mi awa Anwar bayan yayi playing videon Amrah in yana jin zuciyar shi kamar zata fito waje dan yadda yaji ya tsani Amrah A lokacin da idanuwan Anwar suka sau a akan videon in kallo aya ya yiwa videon ya auke kan shi tare da furta. "Auzubillahi minna shai annir rajim" Ya fa a ba tare da ya lura da fuskar wacece a jikin videon ba, har ya bu i baki zai ce wani abu sai kuma maganganun mahaifiyar shi suka shiga mishi yawo a kunnuwa. " _Ina kuwa lafiya Anwar kai daman ashe karuwa kake arin auro mana ka kawo mana cikin_ _zuri'aaaaaa. Eh dole kace haka mana tun da an mana rufa-rufa ana_ _ arin aba mana karuwa a cikin zuri'a,_". Haka Anwar ya dinga jin Kalmar Karuwa tana masa yawo a cikin kunnuwa. Lokaci guda yayi saurin zubura tare da ara kai duban shi a kan wannan videon a karo na biyu. Wani irin sarawa kan Anwar yayi a lokaci guda tare da jin wata irin hajijiya tana arin kayar dashi, ga wani irin gumi da ya shigar karyo mishi tun daga tafin afa har tsakar kan shi. Nazir bai yi auni ba sai ganin Anwar yayi ya zube yashe a asa ko waran motsi bai yi ba. Da gudu Nazir ya nufi kan shi yana iran sunan shi amma shiru, nan fa ya ruga waje da gudu yana walawa mahaifiyar shi ira cikin tsananin ru ani da tashin hankali. ***** *GARIN GIWA* Ba wanda ya san abun da yake faruwa da Amrah in a can gidan nasu, sai dai kafin wani lokaci wasu daga cikin tsirarun an garin sun fara cin karo da videon inda kan kace kwabo har video ya fara yawo a cikin garin tunin rabin an garin sun samu ganin wannan videon rashin kunyar na Amrah domin kuwa har wa anda basu da waya ma sai da suka ga videon wannan nunawa wannan wannan nunawa wancan haka aka rin a fasin-fasin da videon inda magana ta shiga tashi a cikin garin irin ananan maganar nan,da yawa take suka shiga yin Allah wadai da wannan halin da Amrah in ta akko,inda wasu kuma suka shiga yin Allah ya ara daman ai shi Malam Kabiru laifin shine ba ya dage sai ar shi tayi karatu ba,to ai ga irin ta nan tun ba a je ko ina ba ta janyo mishi abun kunya. Wasu kuma cewa suka yi daman kwa ayin abun duniya ne da kuma son duniya ya sanya shi har ya kai ar shi makaranta wata uwa duniya, cikin wa anda suke wa annan maganganun hadda manyan abokanan Malam Kabiru in,wa anda lokacin da suka samu labarin cewar Malam Kabiru zai tura ar shi karatu jami'a sun same shi sun bashi shawara akan kar ya kaita in inda suka nuna mishi illar hakan amma sai baiyi amfani da shawarar ta su ba,abun da ba a fiye yi a garin ba shine a kai yarinya makarantar gaba da secondary, yawancin yara daga secondary school an musu aure. Da yawa daga cikin masu maganar sun fi ganin laifin Malam Kabiru akan laifin Amrah domin kuwa cewa suke da ace bai kai Amrah in makarantar ba da duk haka bata faru ba, sai dai bakin al alami ya riga da ya bushe addara ta riga fata!. Haka dai kowa ya dinga tofa albarkacin bakinsa kan kace mai duk wani alkhairin Malam Kabiru ya disashe a idon mutane inda aka shiga jifan shi da munanan maganganu sa anin da da duk wanda zai bu i baki ya fa i magana a kan Malam Kabiru in to alkhairi ne zai biyo ba, daga shi har iyalan shi ba wanda yake da wani mummunan aibu a idon mutane, amma gashi yau an wayi gari mutane sun bu awa idon su toka sun manta da waye Malam Kabiru a wajen mutanen garin dalilin abun kunyar da aka ci karo dashi na ar shi. Hmmmm an Adam Kennan!. *MANGA* _Comment_ _Share_ _Fisabillillahi_ . *FANSAR FATALWA*! ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA*: _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_. *Free book* ---------------------------------------------- *Bissimillahir rahmani rahim* *021* ______________________________ Malam Kabiru ne ya fito daga cikin rumfar ofar akin nashi,sanye yake cikin babbar riga wanda kana gani shi ka san mutum ne mai cike da dattako da kamala. Buta ya auka a wajen randa inda ya nufi bayi domin kama ruwa kasancewar lokacin sallahr Azhar ya arato. Bayan ya fito daga bayin ne ya tarar da Gwaggo Sa'adatu tsaye a bakin rumfa tana jiran shi hannun ta ri e da asuwaki, tana ganin fitowar tashi tayi saurin arasawa ta kar i butar hannun shi sannan ta kai mishi wajen alawla sai da ta mi a mishi asuwakin ya fara yi domin kuwa hakan yana daga cikin al'adar shi in dai zai alawla to sai yayi asuwaki haka bayan ya kammalla ma. an rusunawa Gwaggo Sa'adatu tayi in kafin daga bisani tace. "Malam dan Allah ko zan iya cewa wani abu?". Zama Malam Kabiru yayi akan dutsen da yake alawlar kafin ya dube ta yace. "To Shikennan kiyi maganar ki Allah dai ya sa ba doguwar magana bace ba". "Malam yau in ne naga kamar wani abu yana an damun ka?, Allah dai yasa lafiya". Dogon numfashi Malam Kabiru in ya ja sannan yace. "Bakomai, amma idan na dawo daga massallaci zamu yi magana". Ya fa a sannan ya cigaba da yin asuwakin. Bayan ya kammalla asuwakin ne ya fara gabatar da alawlar cikin nutsuwa ya idar da alawlar sannan ya yi addu'ar bayan idar da alawla tare da aga hannun sama yayi addu'a sannan ya tashi tare da duban Gwaggo Sa'adatu yace. "To ni zan fita sai kuma Allah yayi dawowar mu". "To Shikennan Malam a dawo lafiya". Sa kai yayi tare da ficewa a cikin
Chapter 27 · 0% Book details