Sashe 41
Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zauna inda Gwaggo Sa'adatu ta shimfi a musu tabarma sannan ta sake kawo musu ruwa a aton kofi da abinci a kwano. Sosai Justice Kabir ya ji da in irin karamcin mutanen duk da sun kasance basu da wani arziki amma akwai wadatar zuci,gashi dai basu san su ba amma kalla yadda suka karramma su. Usman ne suka shigo cikin gidan dashi da Umar da matayen su da alama Malam Kabiru ne ya ira su,waje suka nema suka zauna sannan suka gaishe da su Justice Kabir Sai da suka gama gaisawa sannan Malam Kabiru ya dubi su Justice Kabir yace. "Bayin Allah muna jin ku mai yake tafe da ku?". Shi kam Justice Kabir tun da ya ga yadda an uwan Amrah in suka taru sai gaba aya yaji wani tsoro ha e da fargaba sun rufe shi har yaji ya rasa warin gwaiwar da zai fara sanar da su abin da yake tafe dasu yar dai ganin duk sun zuba mishi ido ya sanya shi bu e baki sannan ya fara magana inda ya shiga sanar da su abin da yake tafe da su. ***** Daga Farida har iyayen ta kuka su ke shar a sakamakon labarin da Anwar in ya sanar da su na Amrah duk da daman sun riga sun san labarin a gidan Rediyo. Daman tuntuni mahaifin Farida ya yiwa Anwar iso har cikin gidan saboda tun lokacin da Anwar ya ira shi da wani suna jikin shi ya bashi cewar lokacin daina kukan shi ya iso. Kallon Anwar mahaifin Farida ya yi da idanun shi da suka yi jawur sannan yace. "Yanzu a ina kake ganin zan ha u da mahaifin Amrah?". Shiru Anwar yayi na an lokaci kafin daga bisani ya ce. "Eh to a gaskiya yanzu sun bar garin Giwa sai dai na samu labarin cewar suna jahar Yobe a wani gari wai Potiskum, sannan na samu labarin hakan ne ta wajen abokina Umar wanda har gobe muna tare sannan duk wani hali da su ke ciki ina samun labarin hakan ta wajen shi". "Idan ba damuwa ina son gobe ku shirya zamu tafi Yobe, idan har kai Anwar kana da wani uzuri to zaka iya tafiya amma mu dai gobe zamu tafi zamu yi sammako". Cewar mahaifin Farida in yana kawar da kan shi gefe sakamakon yadda yake jin zuciyar shi tana mishi zafi. "Ai ba wani uzuri Dad in sha Allah gobe dani za'a yi wannan tafiyar Ubangiji Allah ya kaimu kawai da rai da lafiya" Da Ameen suka amsa gaba aya kafin Anwar ya mi e tare da mu su sallama zai tafi. A hankali ya saci kallon gefen da Farida take inda take suka ha a ido ita ma shi take kallo. Follow my Whattpad account @shamsiyyamanga, Arewa books @ shamsiyyamanga Whatsapp number 07060943991 Phone number 09065779330. Don't forget to share and comment pls. *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA*: _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi._ *Free book* ------------------------------------------------ *Bissimillahir rahmani rahim* *36-37* _______________________________ Tiryan-tiryan Justice Kabir ya shiga bawa su Malam Kabiru labarin duk wani abu da ya faru da Amrah kamar yadda Amira ta sanar da su ba bu wani abu da ya oye musu,sai dai bisa mamakin shi a maimakon yaga tashin hankali ko acin rai a tattare da ahalin Amrah in sai ya ga sa anin haka domin kuwa kaf in su ba wanda ya nuna alamar damuwa a tatare dashi sai yaga alamar ma kamar labarin bai zama sabo a gare su ba. Wani murmushi irin na dattako Malam Kabiru ya sake kafin kuma ya aga hannu sama tare da furta. "Alhamdulillahi Ubangiji Allah na gode daka nuna mun zuwan wannan ranar dana da e ina tsunamayi Allah na gode ma daka bani ikon ganin wannan ranar ba tare da na koma gareka ba, dukkan godiya ta tabbata ga Ubangiji da ya tsamo gaskiya ya bayyana ta a idon duniya a lokacin da idon mutane ya rufe da ganin gaskiya!, A lokacin da mutane suka sanya afa suna ganin gaskiya suka take ta. Amrah ina ma kina duniya kiga wannan ranar!, Amrah Ubangiji Allah ya miki Rahama duk da cewar jikina yana bani kina cikin rahamar Ubangiji". Magana Malam Kabiru ya kasa cigaba da yi sakamakon zuciyar shi da ya ji tana mishi zafi,wasu hawaye ne masu zafi suka shiga arin zubo mishi sai dai tunin ya sanya hannu yayi saurin goge wa. Ita kuwa Gwaggo Sa'adatu duk yadda ta daure sai da abin ya gagare ta bata san sanda ta fashe da wani irin kuka mai ta a zuciya ba duba da yadda aka famo mata ciwon da yake zuciyarta wanda ya kasance anye bai gama warkewa ba. "Dan Allah alfarmar da nake nema a wajen ku shine ku taimaka ku yafewa ata abin da ta aikata wa ar ku saboda ba ita ka ai ta cutar ta sanya a cikin matsala ba harda ku ma ta auki ha in ku,amma dan girman Allah ta ci albarkaci na ku yafe mata. Na sani cewar abin da wahala sosai domin kuwa ko kun ce ba zaku yafewa Azrah ba ba zan ta a ganin laifin ku ba dalili kuwa shine an cutar da ku an muku tabon da ba zaku ta a mantawa dashi ba sannan Azrah bata cancanci yafiya ko tausayawa daga gare ku ba,amma ku yi ha uri ba dan halin ta ba ba kuma dan ni ba dan Allah nake neman wannan alfarmar a wajen ku". Justice Kabir ya fa a yana ha e hannayen shi waje guda alamar neman afuwa tare da Sunkuyar da kai asa. Wani irin kallo Umar ya watsawa Justice Kabir wanda na kasa fahimtar na menene kafin daga bisani yace. "Kai ko kunyar ha a ido da mu baka yi ba da sunan kana nemawa azzalumar arka yafiya?, Kar ka manta irin cin amanar da arka ta aikatawa Amrah wadda ko a lokacin jahiliyya sai an tona kafin a samu wanda zai iya aikata abin da arka ta aikata. A sanadiyyar arka muka rasa ar uwar mu mafi soyuwa a gare mu!, A dalilin ar ka muka zo mu ka rasa an uwan mu wanda mu ke so!, A dalilin ar ka mu ka rasa martaba, ima, mutunci da duk wata daraja da mahaifin mu yake da ita har ta kai ta kawo mun yi nisa da garin da mu ke so mu ke jin da in zama a cikin shi,lokaci guda masoyan mu suka riki e suka koma ma iyan mu duk ta dalilin ar ka, ta ya kake tunanin zamu manta da wannan azzalumar? ta ya ka ke tunanin zamu iya yafewa wadda ta cutar da mu tare da sanya mu a cikin irin wa annan matsalolin dana ambata?, To bari kaji har abada idan nace har abada ina nufin har gaba da abada ba zan ta a yafewa ar ka ba ko da kowa ya yafe mata to nikam ba zan yafe mata ba,kai in ta aice maka labari ma ko da Amrah zata dawo duniya idan har ta yi niyyar yafe maka sai na hana". Umar yana kaiwa nan a zancen na shi ya mi e da niyyar barin gidan saboda yadda yake jin zuciyar shi tsaf zai iya ma ure wa Justice Kabir wuya saboda kallon shi yake kamar Azrah ce a gaban su take zaune tana neman su yafe mata. Muryar Malam Kabiru da yaji ya ira sunan shi ne ya dakatar da shi daga shirin ficewa daga gidan da yake yi "Umar dawo ka zauna". Shine kawai abin da Malam Kabiru in ya furta. A hankali Umar in ya juyo ya dawo ya zauna a gefen Usman wanda shi kam har a wannan lokacin bai ce ala ba. "Umar ka yi ha uri ka sassauta zuciyar ka kasani Ubangiji Allah yana son bayin shi masu ha uri da yafiya,dan haka mu yi ha uri wannan yarinyar ta ci albarkaci mahaifin ta da ya taso takanas ya zo har garin nan domin neman yafiyar mu,sai kaga dalilin yafiyar da muka mu su Allah ya kawo mana wani abin alkhairin, sannan ita rayuwa da ka ke gani kullum nasha fa a muku duk wanda zai zo neman alfarma a wajen to ku yi ari ku mishi wannan alfarmar idan har kuna da halin yi domin kuwa shi Alkhairi da ku ke gani dan o ne baya fa uwa asa banza,yau idan ka taimaki wani to kai ma baka sani ba wata ila gobe shi zai taimake ka". an shiru ya yi kafin daga bisani ya Juya ya ya dubi gefen da Justice Kabir in su ke zaune sannan ya cigaba da magana. "Bakomai kamar yadda ka taso ka zo nemar wa ar ka yafiya mun yafe mata Ubangiji Allah ya yafe mana gaba aya,yanzu zaku iya tashi mu tafi massallaci tun da kun ga magariba ta gabato". Allah Sarki Justice Kabir in jin kalaman Malam Kabiru in bai san lokacin da ya zube duka gwaiwowin shi a asa ba tare da fashewa da wani irin kuka na nadama. Tabbas Malam Kabiru ya cika mutum sannan samun irin shi a duniyar mu a yau sai an tona domin kuwa ya tabbata yau idan da shine a matsayin Malam Kabiru aka yiwa ar shi Azrah haka sannan mutumin da ar shi ta aikata musu haka yazo neman yafiya wajen shi to wallahi sai ya sanya karnuka sun yi mishi yaga-yaga da naman mutumin. Amma yanzu duba ikon Allah yadda Malam Kabiru ya tarbe shi sannan ko musu bai yi ba yace ya yafewa Azrah. Haka suka tashi duk suka yi alawla suka nufi masallaci itama Gwaggo Sa'adatu tashi ta yi sannan ta ha a musu abinci dare wanda ta gama tun azu ta ajiye mu su tana jiran su dawo. ***** Kamar yadda Mahaifin Farida ya fa a yau tun asubar fari suka gama duk shirin su na tafiya garin Yobe in, daman daren ranar gaba aya mahaifin Farida bai iya wani isasshen bacci ba gani yake daren ya mishi tsawo da yawa ya kasa wayewa gashi ya rasa wani irin hali yake