← Book details Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 45

Sashe 5

Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

karo da wayar Azra a yashe a gefe,sunkuyawa tayi ta auki wayar gaban ta yana cigaba da bugawa sannan ta juya ta kalli Amira tace. "Tabbas ba lafiya ba, tabbas na yadda wani abu ya faru da Azra domin kuwa ni na tabbata Azra ba zata ta a fita ta bar wayar ta ba, duba da yadda Azra take da waya ko toilet bata yadda ta shiga ba tare da ita ba". "Innalillahi wa'innailaihi rajiun, to mai yake shirin faruwa haka?" Amira ta fa a ita ma cikin tashi n hankali. "Nifa wallahi daman tun ranar da aka ce an kashe Afrah jikina ya fara yin sanyi, ya Ubangiji kasa ba wani abu bane ya faru da Azra". Cewar Amira in tana zama a bakin gado tare da dafe kan ta. "Ameen ya Allah Amira yanzu mu bari zuwa safiya sai muje muyi repoting a School management domin a san matakin auka tun kafin wani abu ya faru, tun da kinga yanzu past twelve Kinga dare yayi ko". Ita dai Amira bata iya cewa komai ba sai juyawa da tayi ta kwanta tana jin zuciyarta kamar zata fito saboda tsoro fa tashin hankali da kuma firgicin da take ciki Haka dai su Anisa da Amira suka kwana cikin taraddaddi, ba wanda ya iya wani isasshen bacci a cikin su. ***** Yau tun asubar fari jami'ar Ahmadu Bello in aka tashi da wani mummunan tashin hankali wanda ya gigita duk wani mazaunin cikin makarantar,domin kuwa wannan sabon abu ne a tarihin makarantar shine tsintar gawar Azraa da aka yi cikin mummunan yanayi. Filin makarantar tunin ya fara cika da alibai inda duk wanda yayi arba da gawar Azra in sai ya zubar mata da hawaye, mata kuwa take wasu masu raunin zuciyar suka dinga zubewa a wajen domin kuwa kallo aya zaka yiwa gawar ta ta kaji a ranka baka sha'awar sake ganin ta. Da gudu Anisa da Amira suka araso wajen wa anda suka sami labari yanzu. Kutsawa suka fara yi ta tsakanin mutanen inda take aka shiga basu hanya sanin irin arfar ala ar da take tsakanin na su. Amira ce ta fara tozali da gawar Azra in cikin mummunan yanayi, tun daga kallon farko da ta yiwa gawar bata ara sanin inda kan ta yake ba. Ita kuwa Anisa dur ushe wa tayi a wajen ta daskare inda ta zama kamar mutum-mutumi harbawar da numfashin ta yake ne kawai zai tabbatar maka da cewar tana da rai amma duk wani magudanar aiki na jikin ta take suka daina aiki. Haka aka sure su ita da Amira aka yi asibiti da su. A dai-dai wannan lokacin ne kuma hukumar makarantar suka araso wajen tare da an sanda. Darewa mutane suka fara yi inda aka bawa jami'an tsaron hanya suka shiga inda gawar Azra in take. Saurin rintse idanuwan su suka yi sannan Inspector Rasheed (inspector in da case in Afrah yake hannun shi) yayi saurin cire rigar sanyin da take jikin shi kasancewar doguwa har gwaiwa ce inda yayi saurin lullu e jikin Azra da ita, sannan ya juya cikin acin rai ya dubi dandazon maza da matan da suke wajen. "Allah wadaran naka ya lalace, yanzu kaf cikin ku aka rasa wanda zai suturtawa wannan baiwar Allahn jikin ta, idan anwar ku ce zaku bar ta haka ne?, Ku duba halin da wannan yarinyar take ciki tsirara haihuwar uwar ta amma ba wanda yayi tunanin rufe mata jiki, Allah ya kyauta". Duk wajen shiru suka yi inda wasu suka fara arin Sunkuyar da kan su wai saboda kunya. A dai-dai wannan lokacin ne kuma jami'an lafiya suma suka iso, inda wani likita daga cikin su ya fara arin gwada Azra in duk da kuwa kallo aya zaka mata ka fuskanci ta da e da zama gawa. Sai da ya gama gwada ta sannan ya dubi inspector Rasheed yace. "Inspector wannan yarinyar fa ta da e da zama gawa". "Likita na riga da na sani dan haka ku auke ta ku wuce da ita zuwa Mutuary kafin zuwa mu kammalla investigation a kan ta". arasowa wajen ma'aikatan asibitin suka yi inda suka fara arin aukan ta, a lokacin kuwa tunin an jarida sun cika wajen inda suka shiga nasu aikin kowa bu atar shi shine ya auki hoton gawar domin ya samu abun ya awa yau. Har ma'aikatan asibitin sun fara arin aga Azra kawai suka tsinkayi muryar Inspector Rasheed yana cewa cikin araji. "Ku dakata!" Ya fa a yana kai duban shi zuwa dai-dai wuyan Azra Saurin kallon shi mutanen wajen suka yi kowa bu atar shi shine yaji dalilin da ya sanya Inspector Rasheed in ya dakatar da aukar gawar. Wasu daga cikin mutanen wajen ne suka kai duban su saitin inda suka ga Inspector Rasheed in yana kallo domin su ma su bawa idon su abinci. *MANGA* _Comment_ _Share_ _Fisabillillahi_ *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ *SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA*: _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D auta, Sis Amira Adam_ _Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke ina son ku fisabillillahi_ . *Free book* ------------------------------------------ *Bissimillahir rahmani rahim* *004* ___________________________ Kallon wani jami'in an sanda Inspector Rasheed in yayi sannan yace a bashi safan hannu (Hand gloves) sanyawa yayi a hannun shi sannan ya nufi kan gawar Azra usawa yayi dai-dai saitin wuyan ta. A hankali ya sanya hannu ya an sake janye rigar da ta an rufe mata wuya, wani atoton zanen tambari ne mai alamar tauraro (Star) ya bayyana a wuyan Azra Kafe wajen Inspector Rasheed yayi da ido sannan sannan ya fara tunanin inda ya ta a ganin wannan zanen. "Afrah!" Ya fa a da arfe sannan ya mi e tsaye ya juya ya dubi sauran jami'an tsaron yace su tafi asibitin da aka kai gawar Afrah yanzu. Aikuwa gaba aya mota suka shiga tare da ma'aikatan lafiyan da kuma hukumomin makarantar wasu daga ciki inda suka nufi asibitin da aka je aka adana gawar Afrah in, tare da tafiya da gawar Azra domin zuwa a adana tata gawar ita ma. Suna isa cikin asibitin kai tsaye akin da ake ajiye gawarwaki su Inspector Rasheed suka nufa. Babban aki ne mai girman gaske wanda tsayawa fa in girman akin ma ata lokaci ne. Akwatuna ne a jere a cikin akin sun fi guda hamsin da alamu sune akwatunan da ake ajiye gawarwaki a cikin sa. Wani akwati da yake can gefe aka wuce da gawar Azra aka sanya ta a ciki. Wajen wani akwati Inspector Rasheed ya nufa sannan ya bu aci ma'aikatan asibitin da su bu e mishi akwatin. Ana bu ewa kuwa sai ga Afrah a kwance a ciki kamar kace mata tashi ta tashi. Kallon ta ya fara yi tun daga sama har a asa take idon shi ya sau a akan wannan aton zanen na wuyan ta mai alamar tauraro irin wanda ya gani a wuyan Azra ya bayyana. auki tsawon lokaci yana nazarin wannan zanen kafin daga bisani ya sanya wayar shi yayi snapping wajen sannan ya juya suka fice a akin. Suma ma'aikatan asibitin juyawa suka yi suka fita. Ko gama rufe ofar akin ba su yi ba Amrah ta dira a cikin akin cikin mummunar suffa. Lokacin da inspector Rasheed suka fita daga cikin akin da aka adana gawarwakin motar su suka nufa sannan suka tayar da motar suka nufi komawa police station in na su. Sosai Inspector Rasheed ya shiga tunani da nazarin wannan zanen da ya gani a wuyan su, to mai hakan yake nufi?, Shin wannan zanen na meye ne?. Jami'in an sandan da yake gefen Inspector Rasheed ne ya juyo ya dube shi sannan ya lura da halin damuwar da shugaban nasu yake ciki. "Yalla ai akwai damuwa ne?". an sandan ya tambayi inspector Rasheed cikin girmamawa. e numfashi inspector Rasheed yayi kafin ya dube shi yace. "Kofur Bala wallahi wani abu ne ya fara aure mun kai game da wa annan gawarwaki biyun da aka tsinta". Shiru ya an yi kafin daga bisani ya cigaba da magana "Watau abun da yake aure mun kai wanda nasan ba lalle ku kun lura da shi ba shine, shin baku lura da cewar irin kisan da aka yiwa Afrah shi aka yiwa Azra ba?". an shiru Kofur Bala yayi kafin daga bisani yace. "Tabbas Yalla ai sai yanzu tunanina ya kai kan abun,to mai hakan yake nufi Kennan?". "Tabbas na fara zargin wani abu domin kuwa duba da irin kisan da aka musu ya zama iri aya sannan ga wani alama da makashin na su ya bari wadda dole za'a zargi cewar mutum aya ne yake kisan". Inspector Rasheed ya fa a yana kai kallon shi zuwa kan titi. "Kennan yalla ai kana nufin kace mun makashin wa annan ammatan mutum aya ne?". Cewar Kofur Bala in cike da mamaki. "Ina tunanin hakan amma koma mainene bincike zai tabbatar da gaskiyar lamarin". A dai-dai sannan ne kuma suka araso bakin ofishin na su. Lokacin da suka isa ne ake sanar dashi cewar mahaifin Afrah sun zo neman shi amma sun ce zasu dawo. Bai amsa ba sai wucewa cikin office in shi yayi domin kuwa yana bu atar ka aicewa shi aya domin yin nazari game da kisan wa annan ammatan. ***** A cikin gidan su Azra kuwa mahaifin ta ne zaune akan dining table suna breakfast da shi da mahaifiyar Azra in cikin farin ciki da annashuwa. Wayar shi ce da take gefe ta fara ruri alamar tana neman agaji. a hannu yayi sannan ya auki wayar inda ya ga ba uwar number ce, tsaki ya ja sannan yayi rejecting call in ya ajiye wayar a gefe. Kallon shi mahaifiyar Azra tayi da mamaki sannan tace. "Ranka ya da e lafiya kuwa?,tun da muka zauna a wajen nan naga ana ta iran wayar ka a jere a jere a alla an maka ira ya kusa goma amma kana rejecting, ka daure ka aga kaji wata ila iran gaggawa ne ". "Hmmm ba wani iran gaggawa fa,ke kin fi kowa sanin policy na bana aga iran ba uwar number dan haka ba wani ira da zan aga, duk masu bu atar magana dani su nemi ni da number in da na san su". Mahaifin
Chapter 5 · 0% Book details