Sashe 15
Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
haka muna hira zaki ata fuska?". Gwaggo Sa'adatu ta fa a tana janyo ni jikin ta itama fuskar ta da alamar damuwa. "Gwaggo a duk lokacin da aka fara maganar karatu na sai na dinga jin fa uwar gaba, a wani angaren kuma gwaggo ina tausayin Abba kasancewar na san bashi da arfin da zai biya mun ku i na yi karatu,sannan gwaggo kin san a wannan zamanin karatu ya zama sai an wane da wane musamman ni fannin da nake son karanta, sannan gashi a wannan garin na mu har yanzu ba'a auki ilimin mace da muhimmanci ba inda wasu suke yiwa abun kallo na daban,duk lokacin da na tuna abubuwan nan sai naji duk wani farin ciki na ya koma ciki". Amrah ta arashe maganar hawayen da take arin tare suna zubowa daga cikin idanun ta. Shiru gwaggo Sa'adatu suka yi da ita da Hisham cikin tausayin Amrah in,tabbas sun san cewar duk maganganun da ta fa a gaskiya ne to amma kuma a yanzu su ya kamata su kwantar mata da hankali su nuna mata cewar duk abun da Allah ya tsara a rayuwar bawa shi yake kasancewa da shi. Hisham ne yayi arfin halin duban Amrah in sannan ya fara magana cikin sigar rarrashi. "Amrah kinsan dai a rayuwa duk abun da Allah ya tsara shi yake kasancewa da bawa,to dan haka ki auka cewar idan har kin samu damar yin karatu to Allah yayi zaki yi ne, haka kuma idan har kika ga baki samu damar cika burin ki ba to Allah ne bai yi hakan zai tabbata ba,dan haka in sha Allah ki sa a ranki in dai muna raye burin ki zai cika kuma zaki zama likita da izinin Allah,kuma daga yau ki fara shiri Jamb in ki yana fita zaki wuce makaranta". Wannan kalaman da Yaya Hisham ya yiwa Amrah su suka sanya ta cikin farin ciki wanda har bata san sanda ta saki murmushi ba, sannan ta tashi da gudu ta yi cikin aki tana jin wani da i kamar an cemata gobe zata wuce makaranta. Da dare bayan malam Kabiru mahaifin Amrah ya dawo gwaggo Sa'adatu ta kawo mishi abinci da ruwa kamar yadda ta saba. Sai da Amrah ta bari ya ci abinci ya sha ruwa kafin ta fito daga cikin akin ta sannan ta zo ta zauna a kusa dashi tare da gaishe shi. "Mamana (kasancewar sunan mahaifiyar shi gare ta), ya dai yau naga bakin ki kamar gonar audiga ya i rufuwa ga dukkan alamu bakin akwai magana ko?". Cewar Malam Kabiru in, murmushi Amrah ta yi sannan tace. "Abba Albishirin ka". "Goro Mamana, goron ma fari tatass". Ya fa a yana fa a fuskar shi da murmushi. "Abba ga result in mu na Waec and Neco ya fito kuma Alhamdulillahi Abba na cinye duka nine credit". Ta fa a tana mi a mishi result in da yake hannun ta. "Ah ah ah Masha Allah Mamana wannan albishir dole a baki tukwaici". Ya fa a yana bu e result in da yake hannun na shi. Caraf gwaggo Sa'adatu ta yi tare da amshe zancen sannan tace. "Ai ba'a isa ba wannan tukwaicin a ni za'a bawa domin kuwa ni na fara maka albishir in ai". Dariya suka yi gaba aya sannan Amrah tace. "To ai gwaggo ko an bani tukwaicin ma kamar ke aka bawa ni da ke ai duk aya ne". "Uhmm kaji Sarkin wayo ko, zata rufe mun baki to Shikennan ai nayi shiru daman haka ki ke so". Albarka Sosai mahaifin Amrah ya sanyawa result in nata kafin daga bisani ya mata addu'a sannan ta tashi ta koma cikin aki. Bayan shigar Amrah aki ne Malam Kabiru yayi gyaran murya tare da duban Gwaggo Sa'adatu fuska da alamar damuwa ya bu i baki ya fara magana. "Wallahi Sa'adatu ranar da nake ta tunanin zuwan ta ne take ta aratowa,kullum da tunanin wannan ranar nake kwana nake tashi ranar da Amrah zata kammalla karatun ta na sani cewar Amrah tana son karatu sosai to amma gashi ni kuma bani da halin da zan sanya ta a makaranta domin cikar burin ta,kin fi kowa sanin halin babun da muke ciki tun da kina gani hakan zan fita yanzu na dawo gidannan hannu wayam wata ran ma sai ke kike taimaka mana,ga Hisham shima yanzu kasuwar ba wata kawo mishi take ba,ga awainiyar shi ga ta iyalan shi, shi kuma Usman karatun shi yanzu haka ya katse sakamakon ku in registration da bai biya ba har na semister biyu,mai dama-daman shine Umar to shima yanzu hidimar auren shi ta sako shi a gaba, sannan abu na gaba kin san yadda asar ta mu yanzu ta zama karatu sai kana da ku i,ga yadda tarbiyya ta ta are a manyan makatantu sai a hankali". Malam Kabiru ya arasa maganar fuska cike da damuwa. Saurin kallon shi gwaggo Sa'adatu ta yi sannan ta fara magana cikin son ta arfafa mishi gwaiwa. "Malma na sani duk abubuwan da ka fa a ba wanda ba dai-dai ba a cikin maganar ka, amma ina son ka san wani abu guda aya duk bakin da Allah ya tsaga ba zai hana shi abinci ba,dan haka kamar yadda Amrah ta kammalla makarantar ta Sakandire lafiya kuma ta samu ta fita da kyakkyawan sakamako to bi'izinillahi rabbi zata cigaba da karatu kai dai kawai yanzu mu mata addu'ar wannan result in da ya rage mata ya fito lafiya kuma ta ci shi,sannan a halin yanzu Amrah warin gwaiwar mu take bu ata dan Allah ka cire komai a ranka,ko ka manta duk sauran jarrabawar da ta rubuta da ku i ake rubutawa kuma an biya mata ta yi to in sha Allah wannan ma ba zai gagara ba". Sosai Malam Kabiru ya ji da in maganganun matar ta shi in da ya shiga sanya mata albarka ya kuma godewa Allah da ya azurta shi da mata mai halin kirki irin Sa'adatu Bayan wasu kwanaki result in Amrah ya fito na Jamb in da cikin ikon Allah ta ci maki fiye ma da yadda ake bu ata wannan dalilin ya sanya an gidan su Amrah suka ara zage damtse wajen ganin an cika mata burin ta. Yau gidan su Amrah an tashi ana bikin yayan ta Umar in da aka aura aure lafiya aka gama lafiya ba wani arya da aka yi a bikin kasancewar auren an malam Shehu ne daga amaryar har angon. A wannan bikin ne Amrah ta ha o da sanyin idaniyar ta Anwar wanda ya kasance abokin Umar Sai dai shi a garin Zaria yake da zama. Tun da Anwar ya yalla idon shi akan Amrah ya ji duk duniya ba wadda yake so sama da ita. Aikuwa ba tare da yayi asa a gwaiwa ba ya isar da sa on shi wajen Amrah in da bai wani sha wahala ba ta kar e shi hannu bibbiyu. Lokaci guda wata zazzafar soyayya ta ullua a tsakanin Amrah da Anwar,wanda Anwar ya mayar da Zaria da garin Giwa kamar unguwa, tun ba wanda ya fahimci abun da yake faruwa a tsakanin su har an gidan su Amrah in suka zo suka fahimta. Yau Amrah ta tashi da wani irin farin ciki sakamakon Anwar zai zo in da za su shiga cikin garin Zaria da Umar domin a mata siyayyar tafiya makaranta, duk da cewar tafiyar da an saura ba'a ma gama registration ba. A motar Anwar in suka tafi inda ya kai su wani babban Mall a garin Zaria Suna fitowa a cikin motar Umar ya tsaya yana arewa wajen kallo sannan ya dubi Anwar yace. "Malam kasuwa fa zaka kai mu ya naga ka kawo mu wannan wajen wanda kai ma kasan waje ne da yafi arfin talakawa irin mu,kaga dan Allah wuce mu tafi kasuwa". Umar ya fa a yana arin komawa cikin motar. Murmushi Anwar ya yi sannan ya dubi Umar yace. "Umar dan Allah ku zo ku shiga ka sani cewar ko ba wata ala a a tsakani na da Amrah ita in na auke ta kamar anwa ta ce,dan haka kar ka damu akwai enough ku i wanda zamu yi siyayya a anwar mu,ita ma ta je makaranta ta fantama". Ya fa a yana kamo hannun Umar in suka nufi cikin Mall in, siyayya ta gani ta fa a Anwar ya yiwa Amrah inda sai da Umar ya ce mishi ya dakata. Sosai suka yiwa Anwar godiya har sai da Amrah ta zubar da hawaye ganin irin lodin siyayyar da ya mata in, a ciki hadda waya mai bala'in tsada ya ha a mata da ita. *MANGA* _Comment_ _Share_ _Fisabillillahi_ . *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ * *SHAMSIYYA MANGA* *SADAUKARWA* : _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi._ *Free book* ------------------------------------------- *Bissimillahir rahmani rahim* *012* ____________________________ Lokacin da su Amrah suka koma gida Malam Kabiru bayannan sakamakon wata tafiya ta gaggawa da ta ta so mishi ya tafi cikin Kaduna. A tsakar gida suka zauna inda suka shiga fito da kayayyakin da suka zo da su in, ido waje gwaggo Sa'adatu ta shiga bin su da kallo tana mamakin yawan kayan, sannan ta bu i baki ta dubi Umar tace. "Umar wannan kayan fa haka,ko dai ido na ne?". Murmushi Umar ya yi sannan yace. "Gwaggo ba idon ki ba ne wannan kayan duka na Amrah ne,na tafiya makarantar ta". Kayan Gwaggo Sa'adatu ta shiga agawa aya bayan aya baki bu "Kai Umar a ina ku ka samu ku in siyo wa annan kayan haka?". "Wallahi Gwaggo Anwar ne ya yi duk wa annan siyayyar ku in da muka tafi da su ma ga su nan ko ta a su bamu yi ba mun dawo da su". Umar ya fa a yana ciro ku in a aljihun shi yana nuna wa Gwaggo Sa'adatu. Shiru Gwaggo Sa'adatu ta yi kamar mai nazarin wani abu kafin can ta ago tace "Amma Umar kana ganin hakan ba kuskure ba ne ba kuwa?". "Gwaggo kuskuren mai Kennan?". "Kafi kowa sanin halin mahaifin ku, kasan sarai idan har ya ga wa annan kayyayyakin ran mu ne gaba aya zai