← Book details Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 45

Sashe 35

Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umar da ta nufa da kuma gwaggo Sa'adatu ta shiga tambayar su. "Dan Allah ina bu atar arin bayani dan Allah mai yake faruwa ne a gidan nan?, Sa'adatu wai mai ya samu Amrah in naji ana wani zance da har yanzu na kasa gane inda ya dosa. Umar ne ya samu damar da kuma arin bu e baki ya fara magana. "Amrah ta riga mu gidan gaskiya, Amrah ta tafi ta barmu cikin duniya cike da kewar ta, Amrah ta tafi ta bar duniya a dai-dai lokacin da muka fi bu atar ta, innalillahi wa'innailaihi rajiun tabbas da ana aryata mutuwa a yau da sai na aryata mutuwar tillon anwata wadda nake matu ar so nake kuma jin ta har a asan zuciyata,ban san yadda zan kwatanta muku irin ciwon da nake ji a asan zuciyata ba,ban san y..........". Kukan da ya taso mishi ne ya hana shi arasa maganar da yake in inda ya shiga raira shi kamar wani aramin yaro. Wani kuka Gwaggo Sa'adatu in itama ta fashe dashi mai bala'in cin rai har shi ewa take sannan ta fara magana. "Amrah meyasa?,Amrah meyasa?, Amrah kin san ko da kowa zai guje ki ni ba zan ta a guje miki ba, Amrah tun ranar da na samu labarin abin da aka ce kin aikata Amrah na aryata saboda nasan wallahi ata Amrah mai cikakkiyar kunya ba zata ta a aikata abun da aka ce ba,kullum idan nayi salla goshina baya ta agowa daga sujadda face na kai arar duk wa anda suka aikata miki wannan aika-aikar wajen mai kowa mai komai kuma mai duka,kullum cikin addu'ar Allah ya tona musu asiri nake Amrah amma kin tafi kin barni cike da kewar ki Amrah m..........". Sai kuma maganar tata ta katse sannan ta tafi luuu ta sume a wajen. "Innalillahi wa'innailaihi rajiun,la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minna zalumin,yanzu da gaske Amrah ta mutu?, Yanzu da gaske Wannan gawar Amrah ce?". Wannan shine abin da mahaifiyar Anwar ta shiga maimaitawa. ***** A can asibiti kuwa lokacin da likitoci suka du ufa akan Anwar wasu na'urori aka shiga jona mishi ta ko wane sashi na jikin nashi,hanci da bakin shi kuma an jona na'urar taimakawa wajen numfashi ya daidaita watau (OXYGEN). Likitoci ne sun fi arfin biyar a kan shi kowa da abin da yake yi manyan su da yaran su, arin kowa shine bai wuce a taimak rayuwar Anwar in ba. Amma sai dai tun suna yin abin iya arfin su har suka fara galabaita Anwar ko shurawa bai yi ba,nan fa hankalin su ya ara dugunzuma suka fara tunanin ko ya mutu ne. Sai dai kuma ganin cewar jijiyar shi tana harbawa sannan ga na'urar da aka jona mishi tana yi wannan shi ya tabbatar musu da cewar yana da rai. Wani abu suka akko kamar Iron sannan suka shiga danna mishi a jikin shi ana sawa ana cirewa sai ya zabura kamar zai mi e,duk sawa aya sai ya zubar da shi da haka dai suka samu ya an fara responding amma ba wani sosai ba. Ganin da suka yi numfashin ya fara daidaituwa ne suka arasa komai sannan suka fita suka bar shi. Sai dai alamu sun nuna yana cikin halin tsaka mai wuya halin ko a mutu ko a yi rai a kowane lokaci zai iya tashi sannan a kowane lokaci zai iya mutuwa duba da yadda zuciayar shi take bugawa da sauri da sauri. ***** Lokacin dana koma makaranta na tarar da Anisa da Afrah a bakin Hostel fuskokin su duk alamar tashin hankali ya bayyana. Ko kallon inda suke ban yi ba na fara arin shigewa cikin Hostel in sai dai da sauri Anisa ta tare ni tana ce mun ina Amrah. Wani malalacin kallo na wurga mata sannan na juyo na dube su kafin na fara magana. "Wacece Amrah a wajen ku?, A ina kuka santa?, Mecece ala ar ku da ita da har zaku tambaye ta?, Lalle na yarda cewar baku da kunya wallahi ko ka an, Anisa har kina da bakin da zaki tsaya a gabana kina tambayata ina Amrah cikin nuna damuwa?, Matar da a yanzu ko da mutuwa ta yi ku ne sila ko tantama bana yi. Hmmmm idan ba ku sani ba ku sani Amrah ta bar mu ku cikin makarantar nan sai ku zuba ruwa a asa ku sha,Anisa Afrah Azra wallahi ba zaku gama da duniya lafiya ba,wallahi wallahi mutuwar ku sai ta zama abar kallo,na rantse da Allah rayuwar ku sai ta wula anta fiye da yadda ta Amrah ta wula anta,domin kuwa ita a duniya ne kawai ta wula anta na tabbata a lahira zata samu kyakkyawan sakamako, amma ku kuwa ina tausayin ku a nan duniya da kuma abin da zaku tarar a lahira". an shiru na yi tare da sanya hannu na na goge hawayen da suka zubo mun sannan na tako a hankali na araso har gaban su na kalle su ido cikin ido bayan na sako wani murmushi mai cike da ma'anoni sannan na cigaba da magana. "Albishirin ku Amrah ta bani sa o tace na sanar da ku tana nan dawowa gare ku,ku tsoroci ha uwar ku da ita a karo na biyu, domin kuwa ha uwa ce da ba zata yi kyau ba,ha uwa ce tsakanin ma iya guda hu Kallo aya zaka yiwa su Anisa ka fahimci zallar tashin hankalin da ya ke shimfi e a kan fuskokin su sakamakon jin abun da na fa in domin kuwa ko da wasa Afrah da Anisa ba su ta a tunanin cewa na san abin da suka aikata in ba in ka cire Azra. ***** Wani tashin hankali da ya faru da su Usman a lokacin da suka je suka sanar a massallaci mutuwar Amrah in shine limamin massallacin ya dubi wayar idon Usman ido cikin ido sannan yace mishi sam su basu sallaci gawar fasi a ba wadda ta nesan ta kan ta daga rahamar Ubangiji dan haka suma kama hanya tun wuri su bar wajen,ai daman sun san cewa Allah ba zai ta a barin Amrah ba domin kuwa ba zai ta a barin ana arna a doron asa ba,har da siffanta Amrah da an wuta ba en maganganu dai haka wannan limamin yayi ta sukar Amrah da su hadda Malam Kabiru daman shi wannan limamin mai suna Malam alha abokin Malam Kabiru ne ba wanda bai san irin amintar da take tsakanin su ba domin kuwa tun amintar yarinta ne amma kuma a lokacin da wannan abun ya samu Amrah shine mutum na farko da ya fara sukar Malam Kabiru har ya juya mishi baya sannan ya dinga bi wajen mutane yana ara ata Malam Kabiru in da haka yayi nasarar cusa tsanar Malam Kabiru da kuma ahalin shi a zukatan mutanen garin,shi daman yana nunawa Malam Kabiru su ne kawai a baki amma a zuciyar shi ba shi da wani buri da ya wuce ya ga ya samu abin da zai dur usar da sunan Malam Kabiru asa ta yadda kowa zai juya mishi baya . Innalillahi wa'innailaihi rajiun tun da Usman yake a fa in duniya bai ta a ha uwa da cin fuska da kuma cin mutunci irin wannan ba. Wannan wana irin tashin hankaline daman haka duniya ta zama? Usman in ya fa a yana mai dafe kan shi da ya ji yana barazanar tsage mishi. *Kuyi ha uri na jina shiru da kuka yi jiya wallahi abubuwa ne suka mun yawa,amma dai gashi yau na yi arin yi muku* *typing, tun da ku ko kara ma ba zaku yiwa Amrah ba ku ce Shamsiyya ki bar typing in nan har sai an gama* *zaman makokin Amrah ku nuna mata auna* Follow my account Whattpad @shamsiyyamanga. Arewa books @shamsiyyamanga. Whatsapp number 07060943991 Phone call 09065779330. Comment Share fisabillillahi . *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ *Tsarawa/Rubutawa* SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA* : _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi._ *Free book* ----------------------------------------------- *Bissimillahir rahmani rahim* *027* _______________________________ Tsananin takaici da ba in cikin maganganun Malam alha in ne suka sanya Usman in fara ganin wani dishi-dishi duk irin dauriyar da Usman in ya so yayi a wannan karon abin ya gagara. wasu hawaye ne masu zafi suka fara zarya a kan kuncin nashi gilmawar wasu taurari ya gani a idon nashi kafin kuma daga bisani ya tafi luuu zai fa i, cikin sauri Wannan mutumin da suka zo tare ya tare shi ganin yana shirin kaiwa asa. iran sunan shi mutumin ya shiga yi amma ina! Usman bai san ma yana yi ba gashi dai idon shi biyu yana numfashi yana komai amma kuma ya bu i baki yayi magana ya kasa. Haka dai da taimakon wannan mutumin ya kama shi suka nufi hanyar komawa gida. Wani sabon tashin hankali na biyu da suka je suka tarar a gidan shine sun isa suka samu labari mummuna game da Ya Hisham inda ake sanar da su cewar an wata mota ta taka shi a bakin titi inda ko shurawa bai yi ba shi kuma mai motar da ya buge shi in ya tsare bai tsaya ba. Innalillahi wa'innailaihi rajiun gawa biyu a cikin gida aya a lokaci guda tsayawa kwatanta muku irin tashin hankalin da wannan ahalin suka shiga ata lokaci ne,domin kuwa Gwaggo Sa'adatu haka ta dinga suma tana farfa owa da an zuba mata ruwa da ta farfa o zata sake yankar jiki ta suma,ba wanda ya san adadin suman da tayi. Kaf cikin su daga Umar har Usman ba wani mai arfin hali kowanne ka ganshi kuka yake wiwi kamar ran sa zai fita. Nazir kuwa da mahaifiyar su gaba aya suma sai da suka shiga tashin hankali har sai da suka yi hawaye saboda tausayin wannan ahalin, ita kam mahaifiyar Anwar ji ta yi duniyar ma gaba aya ta ishe ta,wannan wace kalar mummunar addara ce. yar dai aka samu wasu tsirarun mutane da basu fi a irga ba a cikin garin suka zo aka gyara gawar Hisham data Amrah aka fara shirin sallatar su. Duk wannan abin da yake faruwa Malam Kabiru yana
Chapter 35 · 0% Book details