Sashe 23
Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
asali,kaga laila da Majnun wadda soyayyar su ta zarce ta romio da Juliet,sannan ta kere ta Ram da Sita,irin wannan shan love haka,to gaskiya ya kamata a bar mana ita haka mu tafi Hostel domin kuwa muma mun yi missing in ta". Azra ta fa a suna arasa tsayawa a wajen daga yanayin da tayi maganar zaka fahimci cewa da biyu ta yi maganar, amma kuma kasancewar Amrah zuciyarta aya ce ya sanya bata kawo komai a ranta ba. Murmushi Amrah tayi sannan tace. "Ai yanzu kuwa zamu tafi dan daman tun azu na dame shi da sai munyi sallama shikuma ya i sai jana yake da surutu". "Gaskiya dai mu tafi, malam Anwar ya gida ko gaisawa ma bamu yi ba". Cewar Azra in tana kallon cikin idon Anwar A ta aice ya amsa mata sannan ya juya ya dubi Amrah ya mata sallama ya shige motar shi ya ja ya tafi domin kuwa shi wallahi bai san maiyasa bai son wa annan awayen Amrah in ba, musamman Azra mutum aya yake so kuma yake ganin mutuncin ta ita ce Amira. Ita kam Afrah tsananin mamakin Azra in ne ya hanata cewa ko kanzil domin kuwa abun ya matu ar bata mamaki. Sosai Azra ta sakewa Amrah fuska harda tambayar ta ya ta baro su Gwaggo Sa'adatu abun da kuma bata ta a yi ba. Haka suka kama hanya suka wuce Hostel,kayan su kuma suka nema aka shigo musu dashi. Tun daga ranar da suka dawo makaranta Azra bata sake nunawa Amrah wani abu mai kama da yashi ba kullum cikin janta a jiki take wata irin kulawa ta musamman take nuna mata. Tun abun yana bamu mamaki har ya dawo muka daina mamaki in da muka cigaba da harkokin mu. Cikin ikon Allah yau aka kafe mana result in exam in da muka yi na First semester wanda Amrah ce ta yi overall,sannan Azara ta biyo bayan ta sai ni sai Afrah sai kuma Anisa. Wannan abu ba aramin da i ya mana ba inda muka sha murna sosai wani abun mamaki yadda Azra ta nuna tafi kowa taya Amrah murna shine babban abun da ya aure mun kai,domin kuwa ni dai nasan cewa Azra tana da tsananin yashin taga wani ya wuce ta abu amma sai gashi wai yau Azra an kafe result wata ta fita amma ko a jikin ta. Abun da bamu sani ba shine ashe ta Ciki na ciki domin kuwa Azra inda zaka tsaga zuciyarta a wannan lokacin ba abun da zaka gani sai tsantsar wutar iyayyar Amrah da ta sake ruruwa a cikin zuciyar ta. Haka ta shiga toilet ta kulle kan ta ta sha kuka kamar ranta zai fita,ba wanda ya sani a tsakanin mu. ***** Yau ta kama weekend ne inda tun safe muka fita karatu kasancewar ni da Amrah muke karatu tare, sai ya zamana mun bar Anisa da Afra da kuma Azra a akin. Zaune suke a cikin akin in da suke tattaunawa akan yadda zasu ullowa lamarin Anwar Azrah ce ta dubi su Anisa sannan tace. "Afra ki ira Anwar a waya ki bayyana mishi abun da yake zuciyar ki a yanzu muji abun da zai ce". Kallon Azra Afrah ta yi da niyyar yin magana tare da fito da ido waje,sai dai da sauri Anisa ta dakatar da ita tare da cewa. "Wai Afrah wace irin matsoraciya ce?, Wallahi shiyasa wani lokacin ki ke bani haushi ni idan da nice da tunin an da e da wuce wannan zancen,da tunin wani zancen ake ba wannan ba,sai kace ba mace ba,haba dan Allah!". Anisa ta fa a cikin son ta arfafawa Afra in gwaiwa. A hankali Afrah ta sanya hannu ta akko wayarta da take gefe sannan ta cire sim card in ciki ta sanya wani sannan ta nemo number in Anwar ta shiga dialing tana jin zuciyarta kamar zata fito waje saboda tsoron abun da zai je ya dawo. Sai da ta yiwa Anwar ira uku ana hu u tukunna ya aga,bai yi magana ba ya yi shiru in da a hankali cikin sanyin murya ta furta. "Hello!". Daga aya angaren Anwar ya amsa bai jira abun da zata ce ba yace. "Da wa nake magana pls?". Shiru tayi bata amsa ba, jin da Anwar ya yi anyi shiru ne ya sanya shi katse wayar domin a tunanin shi mistake aka yi wajen iran. Sai dai ko dawowa daga zancen zucin da yake bai yi ba ya sake jin wani iran ya shigo mishi cikin wayar, yi yayi kamar ya share sai kuma dai ya aga. A wannan karon duk wani arfin gwaiwa Azra ta lalu o ta azawa kan ta sannan ta furta. "Anwar kana jina". Ta fa a tana ajiye wayar a tsakiyar su bayan ta sanya ta a handsfree. "Ina jin ki wacece bangane ba?". Anwar ya fa a kamar an mishi dole. "Anwar dan Allah ina son muyi magana idan ba damuwa mana?". Shiru Anwar in yayi kamar ba zai ce wani abu ba kafin kuma daga bisani yace. "Ok Ina jinki". Ya fa a a ta aice. "Anwar sunana Afrah shin ko zaka tuna wata number da kwanakin baya ake ta tura maka message?". Shikam Anwar jin sunan da ta ambata in ko ka an bai kawo a ranshi cewar wai Afrah awar Amrah bace,domin kuwa bai ta a sanyawa a ranshi cewar hakan zata iya faruwa ba,gashi kuma ko muryar ma bai ji ta mishi kama da wacce ya sani ba,duk kuwa da cewar sau biyu ne ko sau uku suka ta a gaisawa. "Anwar kayi shiru,ko baka ji abun da na fa a bane?". Ya tsinkayi muryar Afrah daga aya angaren ta fa "Eh na tuna" "Amma kuma shine Anwar ko sau aya baka ta a mun reply ba?". Shi maganar ma dariya ta bashi inda har sai da ya dara. Jin muryar Anwar in yana mata dariya ne ya sanya ta kalli su Azra idanun ta suna cikowa da hawaye,sannan cikin rawar murya ta furta. "Anwar dariya ma na baka?". Sai da yayi dariya mai isar shi kafin yace. "Sosaima wallahi, saboda gaba aya maganar taki ne naji ta wani bambarakwai,kawai saboda nine wanda ban san ciwon kaina ba daga ganin message a wayata sai na hau yin reply,to an gayamiki Anwar irin mazan da kika saba turawa message ne marrasa aji irin ki, tukunna ma mai yasa kika irani?". Hawayen da Afrah ta ke ri ewa ne suka shiga sintiri ta kan kuncin ta,tun da take ba'a ta a fa a mata maganar da ta ona mata rai irin wannan ba,amma bakomai ko da zai zage ta yau dai zata bayyana mishi sirrin zuciyarta. "Amma Anwar ina so ka sani duk wanda zai so ka to ai da alkhairi ya nufeka,sannan soyayya bata ta a zama iyayya, wallahi Anwar ina son ka kuma da gaskiya,ban ta a ganin wani a namiji da naji son shi irin yadda naji naka ba, pls Anwar dan Allah ka so ni". Shikam Anwar mamaki ne ya mamaye shi lokaci guda jin wai a macece take requesting soyayya a wajen namiji,lalle duniya ta lalace. "Uhmmm wa kika ce ma sunan ki?". "Afrah" Ta maimaita a hankali. "Yawwa Afrah dan Allah zan ro e ki da girman Allah ki fita a rayuwata domin kuwa ni da kika gani ina da mata,dan haka tun muna cikin ganin darajar juna ki fita a rayuwata sannan kar ki ara garajen turamun message ko kuma ki irani saboda ranar na farko kin sanya matata a cikin damuwa dan haka idan kika ara yin na biyu wallahi zan wula anta ki duk kuwa da cewar wul anci ba abi'ata bace amma kuma idan kika kaini bango zaki sha mamaki dan akan matata Amrah ba abun da ba zan iya ba,kuskuren da zaki aikata wanda zai zamar miki damuwa a rayuwar ki shine sake iran wayata ko kuma ki turamun message". Anwar yana kaiwa nan a maganar shi ya katse wayar sannan ya danna number in Afrah in a blacklist. Wani mahaukacin kuka Afrah ta fashe dashi tare da dafe irjin ta da yake mata suya kamar wuta. "Innalillahi wa'innailaihi rajiun Azra kunji abun da yace!, Azra ni daman nasan wallahi Anwar ba zai ta a sona ba matu ar Amrah tana raye, Azra mutuwar zan yi wallahi matu ar ban mallaki Anwar ba, Azra dan Allah ku taimaka mun". Afrah ta fa a tana kuka wiwi harda majina. Sosai Anisa da Azra suka ji tausayin Afrah in da yar Azra suka rarrashe ta ta sassauta kukan nata, sannan Azra tace. "Afrah ki daina kuka in sha Allah Anwar zai dawo gareki kuma zaki mallake shi,kuma Amrah tana cikin duniyar nan,sannan in sha Allah ke ba zaki ta a shiga damuwa ba sai dai Amrah ta shiga, ina mai tabbatar miki nan da wasu kwanaki Anwar zai zama bashi da wata wadda ya tsana kamar Amrah, ke in ta aice miki labari ma sai Anwar ya dawo ko sunan Amrah baya bu atar ya ji an ambata balle ya ga fuskarta". Cikin sauri muka ago muka kalli Azra ni da Anisa cikin matsanancin mamakin maganganun nata. "Azra ta yaya hakan zata kasance?, Ina tunanin a duniya ba abun da zai sa Anwar ya tsani Amrah koda kuwa asiri aka musu". Wani murmushi Azra ta sake sannan tace. "Sanin hakan ne ma ya sanya ba zamu ta a amfani da asiri wajen yi musu farra u ba domin kuwa atawa kan mu lokaci kawai zamu yi saboda ba zai yi tasiri ba, amma wannan hanyar da zamu bi tabbas hanya ce da zamu yi nasara". "To fah! Azra wannan wace irin hanya ce?". Su Afrah suka tambayi Azra "Karki damu zan sanar daku in sha Allah yanzu dai mu bar maganar tun da kinga lokacin dawowar su daga karatu ya kusa, sannan Afrah ina son ki mannawa Anwar ki fita a harkar shi kar ki ara neman shi,bayan mun samu nasara a abun da muka sa a gaba sai kuma mu ora daga inda muka tsaya". Wani farin ciki ne ya kama Afra ji take kamar ta mallaki Anwar ta gama. *MANGA* _Comment_ _Share_ _Fisabillillahi_. *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA* : _Wannan book