← Book details Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 45

Sashe 24

Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ . *Free book* --------------------------------------------- *Bissimillahir rahmani rahim* *018* ______________________________ Sai dai abun da su Afrah basu sani ba shine duk wani abu da suke shiryawa ina sane da su,domin kuwa yanzu haka ma lokacin da suke wa annan zantukan ina tsaye a bakin ofa ina jin su,a lokacin na dawo zan aukar mana wani littafi kawai naji abun da suke tattaunawa Fasa shiga cikin akin namu na yi inda na tsaya na gama saurarar abun da suke fa Tsoro,fargaba,mamaki ne suka dirar mun a lokaci guda,jikina idan banda rawa ba abun da yake yi. Sai da nagama jin komai kafin na juya na koma wajen karatun namu ba tare da na shiga akin ba. Lokacin da nakoma wajen Amrah ta lura da yanayi na ba yadda na bar wajen ba,hakan ya sanya fara tambaya ta "Amira lafiya kuwa naga yanayin ki ya sanja ba kamar yadda ki ka bar nan wajen ba?". Murmushin arfin hali na aro sannan nace. "Bakomai Amrah wani abu kika gani?". Kallo na Amrah ta yi irin kallon ban yarda ba sannan tace. "Haba Amira ya zaki cemun bakomai bayan duk wanda ya ganki ya san yanayin ki ya sanja,kuma da alama ma kamar kuka kika yi?". Rasa abun da zancewa Amrah na yi inda wata zuciyar ta bani shawarar na sanar da ita kawai abun da naji,wata zuciyar kuma tace kul Amira kar ki fara ki bari muga iya gudun ruwan su. Da wannan shawarar na yi amfani inda na dube ta sannan nace. "Da gaske Amrah bakomai ki yarda dani ke kinsan da akwai abun da yake damuna da na sanar da ke,tun da kinsan bana oye miki komai,kawai dai kaina ne ya an fara mun ciwo". Ji na kawai Amrah ta yi amma alamun ta ya nuna bata yarda ba,kallo na tayi sannan tace. "Ina littafin da kike je akko mana to?". Sai a sannan Amira ta tuna da abun da taje yi Hostel in, an sosa kai ta yi alamar rashin gaskiya sannan tace. "Ai ban ma arasa Hostel in ba saboda ciwon kan yanzu mu ce miki zan yi mu koma kawai". arashe maganar ina mi ewa tsaye domin bana son Amrah ta cikani da tambaya gudun kar a zo a samu matsala ta fahimci halin da nake ciki. Fuskantar da Amrah ta yi cewar bana son maganar ya sanya ta mi e tsaye tare da cemun mu wuce,amma ba wai don ta gamsu da abun da nace in ba. Lokacin da muka Hostel mun tarar da su Afrah har sun shirya mana abinci sannan suka tare mu fuska faran-faran. Wani ullutun ba in ciki ne ya taso ya tokare mun zuciyata a lokacin da na tuna da maganganun da naji su suna yi azun, fisabillillahi kamar ba sune suke shirin tarwatsa farin cikin Amrah ba amma gashi yanzu suna nuna mata sun fi kowa sonta,alhalin kuma idan za'a tona abun da yake a zuciyar su ba za'a ga da kyau ba,lalle an Adam ba abun yarda bane,tabbas su Azra sun cika masu fuska biyu,na fa a a zuciyata ina kwanciya a kan gado,tare da juya musu baya domin kuwa a yadda nake jin zuciyata idan har zan zauna na cigaba da kallon su to tabbas za'a samu matsala zan iya zagin uwar su da uban su wanda kuma ba zan so hakan ba domin kuwa ba yanzu nake son na tona musu asiri ba. Sai dai rashin sani yafi dare duhu domin kuwa da nasan abun da zai faru a gaba da nayi gaggawar tonawa munafukan asiri Amrah ta san da su wa take zaune, wannan shine babban kuskuren dana yi wanda har ya sanya su Azra suka yi galaba akan Amrah kuma wanda har yanzu ina danasanin aikata shi. Muryar Azra da naji tana mun magana akan na tashi muci abinci ita ta dawo dani daga tunanin da na tafi Da sauri na runtse idona alamar bacci nake ina jin su suna ta mun magana amma na manna musu,kasancewar sun san halina da saurin bacci ya sanya suka yi tunanin ko nayi bacci ne. Tun daga wannan lokacin na daina sakewa su Azra fuska domin kuwa gaba aya haushin su nake ji, su kuma sun yi yin duniya na sanar da su damuwa ta amma sai dai nace musu Bakomai. Lokaci guda na zabge na rame duk na zama wata iri dani gashi ko hira na daina sakewa muyi dasu Azra, Amrah ce kawai ban sanja mata ba yadda muke mu'amalar mu ta da to haka muke yanzun ma. Sai dai fa na sawa su Azra ido sosai domin kuwa nayi al awarin sai na tarwatsa shirin su. Kasancewar Azra tana da mugun wayo ya sanya ta fara zargin ko na gano abin da suke shirin aikatawa ne ya sanya na sanja musu. Sai dai abun da ban sani ba shine yadda na sawa su Azra ido ashe itama Azra haka ta sanya mun ido sosai, duk wani takuna tana ankare dani. Wata ranar lahadi da ba zan manta ba, mun fita wajen saloon nida Amrah, mun gama komai lafiya har muka tsaya a kasuwa muka yi siyayya sannan muka kamo hanyar dawowa Hostel a lokacin ma Anwar ne ya kawo mu. Tafe muke a cikin motar in da Anwar da Amrah suke hira sosai,duk da sun so su sanya ni a cikin hirar tasu amma hakan ya gagara domin kuwa nikam gaba aya hankali na ma baya kan su. Anwar ne yake tambayar Amrah shin ko lafiya nake kuwa. Amrah amsa ta bashi inda take ce mishi wallahi itama ta kasa gane meye yake damuna cikin an kwanaki biyun nan. Tambaya ta Anwar in ya shiga yi amma ba wata amsa sabuwa. Duk wata tambayar duniya sun mun amma amsar dai itace bakomai, ganin da suka yi bani da niyya ya sanya suka yale ni. A haka muka iso makaranta inda na fita daga cikin motar bayan na yiwa Anwar sallama ciki-ciki. A mota na yale Anwar da Amrah suna hira inda nikuma na nufo Hostel da kayan da muka siyo. Har na kama handle ofar zan mur a na bu e kawai naji maganganun su Azra wanda suka kusa sanya ni sumewa a wajen. Muryar Azra naji tana cewa. "Kamar yadda na sanar daku a baya cewar akwai hanyar da zamu bi dan mu tarwatsa ala ar da take tsakanin Anwar da Amrah cikin sau i, shine kun ga wannan wayar ta da e a ajiye a jakata ina jiran zuwan ranar amfanin ta,kuma Alhamdulillahi gashi ya zo". an shiru tayi sannan ta dubi Afrah ta cigaba da magana tare da akko wata aramar Camera. "Wannan Camera in da kuke gani zamu sanya ta a toilet, kun san cewar Amrah itace sarkin yin wankan dare,a rana tana wanka sau hu u ne, to zamu daidaice lokacin da zata shiga toilet sai mu sanya wannan Camera in,inda zata mana video in Amrah tsirara daga nan kuma sauran bayanan zan muku shi daga baya". Saurin zaro ido waje Afrah ta yi duk da cewar tana son a raba Anwar da Amrah amma wannan karon sai taji ba zata iya goyon bayan a auki videon tsaraicin Amrah ba,da yar ta alo kuzari sannan ta dubi Azra tace. "Azra nikam gaskiya a sanja shawara domin kuwa wannan abun ai da cutarwa sosai a cikin sa,ni wallahi ba zan so a auki videon tsaraicin aruwata mace ba,ke ko ma iyiyata ce ba zan so ba,balle Amrah yadda muke da ita, dan Allah mu sake wata hanyar dan.......". "Idan har ba wannan hanyar ba to ki shirya ha ura da Anwar domin kuwa in dai baki bi wannan hanyar ba,to ba wata hanya da zamu bi domin ki mallaki Anwar ,ruwan ki ne ki amince ruwan ki ne ki i amincewa,sai dai kuma rashin amincewar ki yana nufin kin rasa Anwar har abada, domin kuwa ba zaki ta a mallakar shi ba". Itama Anisa take ta dubi Afra tace. "Ni a ganina Afra wannan itace kawai mafita idan har kina son ki mallaki Anwar,amma kuma idan kin shirya rasa shi to shikennan ba zamu miki dole ba sai mu yale ki,daman saboda ke zamu yi komai domin mallakar farin cikin ki". Shiru Afrah ta yi tana nazari ita kam gaskiya zuciyarta bata aminta da wannan shawarar ba. Kallon Azra tayi sannan tace. "To Amma mai zamu da videon tsaraicin Amrah in?". "Sanin abun da zamu yi dashi ba wani abun damuwa bane kede kawai ki amince da abun da na ce miki, koma meye daga baya zaki ji". Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine abun da Afrah ta shiga furtawa,wannan shi ake ira ga oshi ga kwanan yunwa. Tabbas tana son Anwar amma kuma wannan hanyar ba hanya bace wadda ta dace ba, domin kuwa babu komai a cikin ta sai zallar tozarci,anya kuwa zata amince?. Afrah ta tambayi kanta, gaskiya abun da kamar wuya domin wallahi zunubin da yawa, ha in Amrah ba zai ta a barin su ba idan har suka tozarta sannan Allah ma ba zai yale su ba,tun daga duniya za su fara ganin sakamako. Nikuwa da nake tsaye a bakin ofa,take afafuwa na suka shiga wata irin karkarwa ban san sanda na zube a wajen ba wani irin gumi ya shiga tsatstsafowa ta kowanne sashi na jiki na,ashe Azra bata da imani har haka?, Ashe Azra zuciyarta ba ar zuciya ce?, Ashe Azra azzaluma ce?, Ashe Azra bata kishin ar uwar ta mace?, Yanzu videon tsaraicin ar uwar ta mace take son auka?, To mai zata yi dashi, innalillahi wa'innailaihi rajiun wannan wace irin rayuwa ce haka,mai Amrah ta tarewa Azra har haka?. Tambayoyin da nashiga jerowa kaina Kennan sai dai bani da wanda zai bani amsar su. Wasu hawaye masu matu ar zafi ne suka shiga kwaranyowa ta kumatun na, a take wani irin zazzafan zazza i ya rufe ni , wata irin tsanar Azra ce ta kamani take nayi danasanin saninta da nayi. Saurin arfin da ya rage mun na tattaro sannan na fara arin mi ewa tsaye duk kuwa da wata irin juya da take arin kayar dani. A
Chapter 24 · 0% Book details