Sashe 29
Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da kuma arin fahimtar da shuwagabannin makarantar cewar Amrah tana da kyakkyawan hali ba zata ta a aikata abun da ake zargin ta ba. Hayaniyar da VC in ya ji tayi yawa ne ya sanya shi yin gyaran murya sannan a karon farko ya bu i baki ya fara magana. "To da farko dai duk naji orafe- orafen ku dama duk shawarwarin da kuka bada daman amfanin meeting in Kennan shine domin aji opinion in kowa,Dr Gana bari in fara da maganar ka saboda naga kai ka ai ne wanda kake kare wannan yarinyar, da farko ina son ka gane wani abu guda aya shine wannan abun fa ba wai zargin yarinyar ake da aikatawa ba a'a hannu dumu-dumu aka kamata da wannan laifin dan haka ba bu atar a tsaya wani bincike akan lamarin, dalili kuwa shine na farko account in da ka yi posting Videon gaba aya username in ta ne a kai kaga kennnan tabbas tana da ala a da account in, abu na gaba shine a cikin toilet a ka auki videon wanda ni dai a iya sanina mutum aya yake shiga toilet yayi wanka dan haka wannan ya nuna cewar da sanin ta da kuma yardar ta aka shiga toilet in aka mata video ko kuma ta yiwa kanta zan ce wannan ya nuna cewa daman tuntuni yarinyar bata gari ba ce ba". ago kan shi Dr Gana yayi cikin sauri wasu hawaye masu zafi ne yaji suna arin fitowa daga idanun shi inda yayi saurin mayar da su sannan ya bu i baki tare da furta. "Amma Sir..........". aga mishi hannu VC in yayi sannan ya cigaba da magana. "Maganar gaskiya Dr Gana dole a zartarwa da wannan yarinyar hukunci, hukunci kuma mai tsauri ko dan hakan ya zama darasi ga an baya masu shawara aikata abu da makamancin nata, a yanzu haka maganar da nake maka manyan malaman addini sun shigo cikin maganar kuma sun bu aci a yi gaggawar aukar mataki a kan ta domin kuwa wannan abu ne da tun da aka kafa wannan makarantar ba'a ta a samun irin haka ba,yanzu dai taro zai tashi inda zamuyi zama na gaba a nan ne kuma za'a fa i hukuncin da aka yanke a kan yarinyar da kuma makomar karatun ta". VC yana kaiwa nan a zancen shi ya mi e tsaye tare da ficewa daga cikin akin taron,inda suma sauran Malaman aya bayan aya suka shiga ficewa daga cikin akin taron ya rage daga Dr Gana sai abokin shi Shahid. "Dr Gana wai mai yasa kake son aura damuwar wannan yarinyar a ranka ne?". Shahid ya fa a yana tasowa daga kan kujerar shi ya dawo kusa da Dr Gana ago idanun shi Dr Gana yayi wa anda suka mishi jawur sannan yace. "Haba Shahid mai yasa ba zan damu kaina ba, wallahi Shahid ina tausayin Amrah kuma wallahi na tabbatar Amrah bata aikata abun da ake zargin ta ba, Ni na tabbata wasu ne suke san ganin sun ata mata suna". Tun da ya fara maganar Shahid ya kafe shi da ido cikin tsananin mamakin kafiya irin ta abokin nashi. "Hmmm Dr Gana mai yasa zaka ji tausayin wadda bata tausayawa kanta ba, sannan maganar zargi ka daina cewar ana zargin ta domin kuwa ba maganar zargi a wannan lamarin,dan haka ni dai shawara zan baka a matsayina na abokin ka wallahi ka cire kan ka daga cikin case in wannan yarinyar domin kuwa na tabbata ba wanda ya isa ya sanya a hana zartar mata da hukuncin da aka yi niyya,dan haka idan zaka tashi mu tafi ma ka tashi mu wuce kawai". "Akwai,tabbas! Akwai abun da zai hana a zartar mata da hukunci". "Waye shi?". Shahid ya fa a yana unshe dariyar da yake ji in domin kuwa ya san abokin nashi zance kawai yake. "Gaskiya! Gaskiya idan ta bayyana zata hana a zartar da hukuncin". Dr Gana yana fa in haka ya tashi ya fice daga cikin Conference Hall in ya har Shahid a tsaye sake da baki,yana mamakin arfin hali irin na abokin nashi. ***** Haka aka jidi Anwar ranga-ranga rai a hannun Allah ko motsi ba yayi, ana isa da shi asibiti likitoci suka taho da gudu suka kar e shi suka shiga dashi Emergency room domin bashi Emergency Treatment. Likitoci sun shafe lokaci mai tsawo a kan Anwar in amma sun kasa ceto shi daga cikin halin ha'ula'in da yake ciki. Sun shafe tsawon awanni a kan shi kafin su samu numfashin shi ya daidaita amma kuma yana nan unconscious bai san wanda yake kan shi ba. aya daga cikin likitocin ne ya fito wanda da alama shine babban su yana sharce gumi inda ya tarar da mahaifiyar Anwar da anin shi Nazir a waje sai kaiwa da komowa suke hankali a matu ar tashe. Suna ganin fitowar likitan suka nufe shi da sauri suna tambayar shi ya jikin Anwar Kallon su yayi sannan yace su biyo shi office. Aikuwa ko gama rufe bakin shi baiyi ba suka bi bayan shi da mugun sauri kamar yadda ya bu ata Bayan sun shiga cikin office in kujera likitan ya nuna musu alamar su zauna sannan ya janyo folder in Anwar in tare da fara rubuce-rubuce a ciki. auki an tsawon lokaci yana rubutun kafin ya ago ya dubi mahaifiyar Anwar yace. "Sannu Hajiya, pls ko zan iya sanin maiye ala ar ku da wannan yaron?". "Likita ana ne nice mahaifiyar shi wannan kuma anin shi ne". Mahaifiyar Anwar ta fa a cikin rawar murya. "Ina mahaifin shi fa?". Da sauri Nazir ya kalle shi sannan yace. "Kaga Dr duk abun da zaka fa a ka fa a da mu da mahaifin shi duk aya ne, dan Allah kayi gaggawar sanar damu abun da yake damun shi". an shiru likitan yayi kafin kuma ya sanya hannu ya gyara zaman glass in idon shi kafin kuma ya fara magana. "To a zahirin gaskiya dai zan iya cewa kuyi ha uri domin kuwa mun yi duk iya arin mu dan ganin mun ceto rayuwar wannan yaron sai dai abun yana so ya gagare mu sakamakon ya shiga shock ne dalilin gani ko jin wani mummunan abu,yanzu dai Alhamdulillahi mun yi nasarar samu mun daidaita numfashin shi amma kuma har yanzu yaron ku yana bu atar addu'a, domin kuwa mu dai mun yi iya abun da zamu iya sauran kuma mun barwa Allah,kuyi ha uri ku cigaba da mishi addu'a Allah ya tashi kafa un shi". Wani irin kuka mai ta a zuciya mahaifiyar Anwar in ta fashe dashi inda da yar Nazir ya janyo ta suka baro office in likitan,sai kuka take kamar ranta zai fita. Rarrashin duniya Nazir ya yiwa mahaifiyar tashi amma kamar wadda yake ara tunzura ta. ***** Yau ta kama Monday tun safe na tashi da shirin komawa makaranta kasancewar yau in mahaifina har yayi sati biyu da rasuwa kuma gashi saura sati aya mu fara exams wannan dalilin yasa zan koma makarantar domin yin karatu gudun kar a zo a kafe result na samu matsala. arfe bakwai na safe na fito cikin shirina na tafiya inda na tarar da mahaifiyata har ta tashi ta kammalla ha a breakfast. Gaishe ta nayi inda na nufi dining table in a tsaitsaye na ci abincin ina ta sauri domin ina son naje na samu lecture gashi duk hankalina yayi kan Amrah so nake kawai naje makarantar naga a wane hali take ciki. Ina kammalla cin abinci na yiwa Mahaifiyata sallama sannan na fito harabar gidan mu inda na tarar da driver yana tsaye a jikin mota yana jirana. Shiga motar nayi inda drivern ya tayar da motar muka fice a cikin gidan muka auki hanyar ABU Bamu yi wata doguwar tafiya ba muka arasa makarantar tamu a parking lot drivern ya sau e ni inda nikuma na zari jakata na nufi Hostel. Da sallama auke a bakina na shiga cikin akin namu wata mummunar fa uwar gabane ta dirar mun a lokaci guda sakamakon arba da nayi da Amrah. Kwance take a kan gado ta rame tayi ba i domin idan har ba kyakkyawan sani ka mata ba to ba lalle ka gane ta ba a yanzun. Cikin sauri na arasa shiga cikin akin tare da yasar da jakata a tsakiyar akin,a bakin gadon na zauna tare da rungumota ina ambatar sunanta. "Ya subhannallah Amrah mai zan gani haka!?". Sai a sannan Amrah ta samu damar bu e idanunta wadda bata ma san da shigowata cikin akin ba sai da taji sau ar muryata a dodon kunnenta. Wasu zafaffan hawaye ne suka shiga zarya a idanun Amrah in wanda da alama har sunyi sabo da kuncin nata. Lokaci guda nima naji wani kuka ya wace mun cikin kuka na fara magana. "Amrah dan Allah kiyi ha uri ki yafe mun, Amrah nasan ban kyauta miki amma dan girman Allah kiyi ha uri naso na dakatar da faruwar wannan abun amma kuma rasuwar mahaifina ita ta dakatar da komai, amma ki sani na dawo a yanzu kuma in sha Allah zan.......". Maganar tawa ce ta katse sakamakon turo ofar da akayi. Su Azra ne suka shigo cikin akin wani mugun kallo na watsawa Azrah in kafin na bu i baki da niyyar cigaba da magana domin kuwa na udiri aniyar cewar a yau sai na tona musu asiri a wajen Amrah koma meye zai faru sai dai ya faru sai dai kafin na fara maganar tunin Azra tayi saurin dakatar dani ta hanyar fara magana. "Lah Amira sau ar yaushe irin wannan zuwa haka ko sanarwa babu". Ban kulata ba sai ma juyawa da nayi na kalli inda Amrah take kwance sannan nace. "Amrah ki sani cewar a wannan zamanin da muke ciki amana tayi aranci,hassada ta cika zukatan al'umma,wanda baka zaton zai ci amanar ka shi yake jefaka a bala'i, Amrah mutane sun zama ba abun yarda ba yanzu dan haka ki bar ganin mutanen da kike tare dasu suna nuna damuwa a kan ki dan abu ya sameki to wallahi kar kisha mamaki sune wa anda sukayi silar shigar ki wannan damuwar,domin kuwa munafukin ka tabarmar ka sannan makashin ka yana tare da kai sa........". "Haba Amira a kan wana dalili zaki zauna kina sanar