← Book details Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 45

Sashe 22

Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gwaggo Sa'adatu ta shiga walawa Amrah in wadda ta ke kwance a aki. Jin iran da Amrah in ta ji Gwaggo Sa'adatu tana mata ne ya sanya ta fitowa daga cikin akin sanye da hijabi tana cewa. "Gwaggo gani". Da kallo Umar in ya bita domin kuwa shima sai a yau ya fuskanci ramar da Amrah in ta yi kallon ta yake sama da asa sannan ya juya ya dubi Gwaggo Sa'adatu tare da cewa "Gwaggo, Amrah ta yi rashin lafiya ne hala ko?". "Hmmm wallahi Umar Amrah ba ta yi rashin lafiya ba, kawai dai wata damuwa ta auka ta sanya a ranta marar tushe". Gwaggo Sa'adatu ta fa a tana ajiyar numfashi. Juyawa Umar ya yi ya dubi Amrah sannan yace. "Ki je Anwar yana waje yana jiran ki". Hasbunnallah shine abun da Amrah in ta fa a sannan ta juya ta fice da sauri ga idanu da suka yi jawur. A bakin motar ta tarar da Anwar tsaye ya kafe ofar gidan su Amrah in da ido. Tana fitowa idon su ya sar e da na juna in da suka kafe juna da ido kowa da abun da yake ayyana wa a ran shi. Sun auki tsawon lokaci a haka kafin a hankali Amrah ta fara takawa ta nufi wajen Anwar in cikin matsanancin tausayin shi ganin yadda idon shi suka yi jawur alamar kuka ya sha. "Amrah me yasa ki ke son jefa zuciyata cikin damuwa?,me yasa Amrah?, Kin san irin damuwar da ki ka sanya zuciyata a an wannan anin lokacin?, Amrah wallahi na damu sosai ganin halin da ki ka shiga azu". Amrah ta tsinkayi muryar Anwar yana magana cikin rawar murya irin ta wa anda suka yi kuka suka oshi. "To ka yi ha uri kaji". Amrah ta fa a cikin shagwa iyar murya tare da sanya yatsan ta aya a baki. "Me yasa zan yi ha urin to?". Anwar ya fa a shima yana kwaikwayon Muryar ta irin yadda ta yi magana. "To me yasa ba zaka ha ura baaaaaaa?". "Saboda baki sanar dani abun da ya saki kuka azu ba". Shiru Amrah ta yi tana jin a ranta ba zata iya fa a mishi damuwar ta ba, sai dai kuma wata zuciyar ta ce mata " _Ki fa a mishi kawai wata ila ki samu arin wani bayani daga gare shi, tun da wata ila an cigaba da tura mishi message in"_. Daramm gaban Amrah ya tsinke ya fa i jin abun da zuciyarta ta ta raya mata, a hankali ta aga kan ta ta dube shi sannan ta fara labarta mishi labarin message in da ta gani a wayar ta shi sannan ta ara da cewar. "Yaya Anwar wallahi ina tsoron kar a yi galaba a kan mu, ina tsoron kar a raba zuciyoyin mu, Ya Anwar nasan kana sona da gaske kuma a ko ina zan bugi irji na fa i hakan, amma ban san meyasa ba tun da naga wannan message in na ji hankali na ya tashi na kasa samun nutsuwa, na kasa danne zuciya ta, na rasa me yasa duk sanda na tuna da wannan message in sai na ji gabana ya tsananta fa uwa, ya Anwar wallahi ina tsoron anmatan wannan zamanin". Amrah ta arashe maganar idanun ta suna cikowa da hawaye. Wani matsanancin tausayin Amrah in ne ya kama Anwar in a lokaci guda kuma ya ji wani son ta ya ara mamaye shi, a hankali ya saki murmushi sannan ya dube ta yace. "Amrah yanzu a kan an wannan abun shine ki ka bi ki ka tayar da hankalin ki har kina arin ki sanya wa kan ki jinya, to ki sha kurimin ki ni Anwar mallakin ki ne kai ka ai, ba wata a da ta isa ta yi galaba a kai na,sannan kin da e da gina fada a cikin zuciyata wadda har abada ba za'a samu wata sarauniya da zata mallaki wannan fadar wadda ta wuce ki ko da kuwa ba kya numfashi a doron asa, fada ta ki ce mallakin ki ne ko kusa da ita sai wanda ki ka ga dama zai je". Duk da cewar Amrah ta ji da in kalaman Anwar in amma kuma sai ta ago ta ce. "Ya Anwar dole hankali na ya tashi, ya Anwar wallahi na tsorata da yawa,amma kuma yanzu kalaman ka sun kore duk wani tsoro da ya ke a zuciyar ta wa, ya Anwar ina son ka sosai". Amrah ta arashe maganar tana rufe idon ta. Murmushi Anwar ya yi sannan yace. "Matsoraciya kawai ni kuma bana son ki". Dukan wasa Amrah ta kaiwa Anwar in tare da an bubbuga afa a asa sannan suka yi sallama ya shiga motar shi ya tafi ita kuma ta shige gida. ***** Yau ta kama ranar da su Amrah za su koma makaranta, tun asubah Amrah ta gama duk wani shirin da zata yi. Malam Kabiru ma ya yi ari in da ya siya mata an abubuwan da ba za'a rasa ba duk kuwa da cewar Amrah in ta ce mishi tana da komai, amma bai ta kan ta ba ya mata abun da ya kamata. Sai da ya zaunar da ita a wannan karon ma ya mata nasiha mai ratsa zuciya kamar yadda ya yi a ranar farkon tafiyar ta. A wannan karon ma Anwar ne ya zo ya auke ta ya mayar da ita, shima sai da ya mata siyayya ta gani a fa a, amma bai bari mahaifin Amrah ya san da maganar siyayyar ba don ya san zai iya cewa a mayar mishi da kayan,ita kan ta Amrah bata san da maganar siyayyar ba sai da suka isa makaranta ta ga yana fito da wasu kayan daban ba wanda ta sani ba. Suna cikin fitowa da kayan motar gidan su Afrah ta iso wajen ta yi parking a gefen ta Anwar. Haka kawai Afrah ta ji wani irin abu ya taso tun daga ma oshin ta ya tokare ta dalilin ganin Amrah da Anwar in da ta yi a tsaye cikin shau auna. Afrah bata yi auni ba sai jin wasu hawaye masu umi ta yi suna gangarowa ta kuncin ta. e murfin motar ta yi a hankali ta fito daga cikin ta sannan ta fara takawa ta nufi wajen da su Amrah in su ke tsaye, zuciyar ta kamar zata fito. *MANGA* _Comment_ _Share_ _Fisabillillahi_ . *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA*: _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_. *Free book* ------------------------------------------- *Bissimillahir rahmani rahim* *017* ____________________________ Daf da Afrah ta kusa isa inda su Amrah su ke tsaye taji an sanya hannu an janye ta da arfe har tana shirin kifawa da bakin ta. Cikin sauri Afrah ta juyo da niyyar yin magana sannan taga wana mai arfin halin ne ya dakatar da ita daga abun da tayi niyyar aikatawa. Azrah ta gani tsaye ta kafeta da idanu cikin kallon ashe baki da hankali. "Afrah mai kike shirin aikatawa haka?, Ko kin samu kuncewar kaine bamu sani ba?". Cikin hawaye Afrah ta juya ta dubi inda su Amrah suke tsaye wa anda basu lura da ita ba har zuwa yanzun dai suna tsaye a inda ya gansu,kana ganin su zaka tabbatar da cewa masoyane na gaskiya. "Azrah mai yasa kika dakatar dani?, Azrah da kin barni naje na bayyana kaina a wajen Anwar kuma a gaban Amrah idan yaso ayi duk wacce za'a yi". Afrah ta arashe maganar cikin sheshe ar kuka ga wani suya da taji zuciyarta tana mata. Wani irin kallo Azrah tabi Afrah da shi tun daga sama har asa sannan tace. "Tabbas na yarda Afrah soyayya ta rufe miki ido tun da gashi har kina shirin allo mana ruwa,to wallahi tun wuri kar ki fara wannan gangancin kin ji na fa a miki in dai ba so kike kiyi biyu babu ba,ba Anwar sannan Amrah kuma ta fara kallon ki a matsayin maci amana". Sai a sannan Afrah ta fara dawowa hankalin ta in da ta sau e wani nannauyyan numfashi tare da furta. "Amma yanzu Azra haka zan zuba ido kullum ina ganin su cikin son juna sannan kullum kamar ara musu arfin soyayyar ake, nikuma ina nan ina ta fama da ciwon zuciya da dakon so". Shiru Azra ta yi bata ce komai ba sannan ta ciro tissue a Jakarta ta mi awa Afrah tace. "Kar i ki share hawayen ki,idan kin gama kukan mayi magana tun da naga yanzu kamar hankalin ki ya gushe". Cikin sauri Afrah ta kamo hannun Azra sannan tace . "A'a Azra dan Allah ki sanar dani wallahi ina cikin hankalina". Ta fa a tana sanya tissue in tare da share hawayen nata. Kallon su Amrah Azra tayi wa anda sai a sannan suke shirin yin sallama,juyowa tayi ta dubi Afrah wadda itama su Amrah in take kallo sannan tace. "Afrah da alamu kin manta maganar da muka yi daku a gidan ku,karki manta fa na sanar dake cewar idan mun dawo school zamu yi magana,sannan ni na miki al awarin cewar zan nemo miki mafita ki yarda dani kamar yadda na fa a wallahi Afrah na miki al awarin ciki nan da wasu kwanaki alilan za'a shafe babin soyayyar Amrah da Anwar inda za'a kafa naku babin soyayyar,nan da wasu kwanaki alilan za'a koma cewa Anwar in Afrah inda zai tashi daga Anwar in Amrah,amma kuma ki sani komai ba zai tafi yadda muke so sai da ha in kanki keda Anisa da kuma Amira,sai dai nasan abu ne mai wahalar gaske ace Amira ta yarda da abun da zamu zo dashi in,amma ba damuwa nasan ta yanda zan ullo mata". "Wallahi Azra na miki al awarin ko mainene zan amince kuma zan baki ha in kai matu ar hakan zai kaine ga mallakar abun da nake so". Wani murmushi Azra ta sake sannan ta kamo hannun Afrah in suka fito daga inda suke la in,sannan suka nufi wajen da Amrah suke tsaye da Anwar suna sallama. Da sallama auke a bakin Azra in suka arasa wajen sannan ta dubi Amrah tace. "A'a kaga masoyan
Chapter 22 · 0% Book details