Sashe 7
Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yayi daga akin sannan ya dubi Justice Kabir zai yi magana sai dai cikin sauri Justice Kabir in ya riga shi inda ya fara magana cikin tashin hankali. "Likita ya ake ciki dan Allah kar sanar dani labari mai da i game da matata, likita dan Allah ka cemun matata ta farka". Duk a lokaci guda Justice Kabir ya jefawa Likitan wa annan tambayoyin. Zare glass in shi likitan yayi sannan ya dubi Justice Kabir cikin tsananin tausayawa kafin yace. "Justice Kabir sai dai ha uri Allahn da ya baka ita ya kar i abin shi". Saurin ri o hannun shi Justice Kabir in yayi yana zaro ido waje kamar zasu fa asa sannan yace. "Likita bangane ba?, Mai kake shirin fa a mun?". "Justice Kabir Allah ya yiwa matar ka rasuwa kasan duk wani mai rai mamaci ne ba wanda ya zo duniya domin yayi gadin ta dan haka ay........". Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine abun da mutanen wajen suka fara fa a cikin tsananin tausayin halin da Justice Kabir in zai shiga. Sai a wannan lokacin inspector Rasheed ya an ji wani tausayin Justice Kabir in ya kama shi. Tabbas tsayawa fa in irin tashin hankalin da Justice Kabir ya shiga ata lokaci ne domin kuwa a take ya fara wasu irin surutai marrassa kan gado wasu ma sa o kawai yake dan arawa. Mutanen wajen ne suka kama shi ganin abun nashi yana neman wuce gona da iri sannan aka nufi motar shi da shi, inda wasu kuma suka je suka akko gawar Hajiya Ikilima aka sanya ta a mota domin a je a mata sutura. Tabbas duk wani mai zuciyar imani sai ya tausayawa halin da Justice Kabir in ya shiga domin kuwa zan iya cewa shima mutuwar ne kawai bai yi ba. Mutane da yawa sun mishi uzuri domin kuwa mutuwar da aka mishi mutuwa ce dai sai mai arfin imani ne zai iya tawakkali,ga a ga mata duk a kwance ba rai. Su kuwa wasu daga cikin talakawan da suka san halin shi musamman ma'aikatan da suke ashin shi take su ka rin a Allah ya ara duba da yadda daman ba wani kyautata mu su yake ba. Shiyasa a rayuwa duk abun da zaka aikata ka zama ka aikata mai kyau ko dan gudun goben ka. Allah ka kar ka sanya mu daga cikin masu wula anta na asa damu Ameen. An je an sallaci Hajiya Ikilima inda aka dangana ta da gidan ta na gaskiya. Har aka je aka kai Hajiya Ikilima Justice Kabir bai bar surutai ba, domin kuwa wasu ma cewa suke walwar shi ta ta ***** A can asibitin da aka kai su Anisa da Amira kuwa sai da suka kwana suka yini ba tare da sun san duniyar da suke ba. A hankali Anisa ta fara bu e idanunta da suka mata nauyi tare da jin kan ta kamar zai rabe gida biyu saboda yadda yake mata ciwo. Wata irin fa uwa gaban ta yayi sakamakon jin abu kamar ruwa ya iso mata a fuska. Hannu ta sanya ta gogo wajen da taji isar abun, innalillahi wa'innailaihi rajiun mai Anisa zata gani! Jini ta gani a hannun nata. Saitin wajen da abun ya zubo mata tabi da kallo duk da irin matsanancin fa uwar gaban da take ji. Jini ta gani yana biyowa ta jikin silin akin da suke kwance Gaba aya saitin wajen da take kwance in jini ne yake ullowa har ya bada shape in Star, kafin kuma ya fara isowa is akan fuskar ta. Jikin Anisa idan ban da rawa ba abun da yake yi, wani gigitaccen ihu ta sake wanda ya sanya ma'aikatan asibitin saurin shigowa cikin akin da gudu hankali tashe. Suna shigowa suka ganta kwance a gadon illahirin jikinta idan banda rawa ba abun da yake ga jini da suka gani a fuskar ta kamar an mata feshi. Hannun ta ta aga tana arin nuna musu sama sai kuma ta tafi luuuu ta sume. ***** angaren Anwar kuwa tun da ya ji labarin mutuwar Azra hankalin shi ya ara tashi, take mutuwar Afrah da ta fara bin jikin shi ta sake dawo mishi sabuwa. Gashi kullum sai Amrah ta zo mishi watarana a fili watarana a cikin bacci, sannan kullum cikin kuka taka zuwar mishi ya rasa dalilin hakan. Duk ranar da tazo mishi a farke ba'a bacci ba to sai ya suma idan ya farfa o kuma to a take zai manta duk wani abu da ya faru Idan kuwa a mafarki ta zo mishi to idan ya farka yana iya tunawa da mafarkin sai dai bai ta a yun urin sanarwa wani ba, shidai kullum cikin addu'a yake. Yau ma kamar kullum kwance yake akan gadon shi yana bacci lokacin arfe aya na dare ne. Mafarki ya fara yi wai gashi a wani atoton fili inda ba gida gaba bare baya. Wata iska ce take ka awa arar ta mai cike da abun tsoro, suuuuuiii ka ke jin ta tana wucewa. A can nesa dashi ya hango ta zaune a asa ta ha a kan ta da gwaiwa. Sannu bisa hankali ya fara tafiya har ya arasa inda take Isar shi wajen yayi dai-dai da ago kan ta, tare da kafe shi da ido. Murmushi ta fara mishi kafin kuma daga bisani ta fashe da wani irin kuka mai sauti. A maimakon ya ga hawaye yana fitowa a idanun ta sai ya ga jini hadda guda-guda suna fitowa daga cikin idanun nata. "Amrah!". ira sunan ta cikin tsananin ru ani. "Anwar sun cuce ni!, Anwar sun kashe ni da rai na!, Anwar shin zaka ga laifi na dan na dawo aukar fansa". Shikam tun da Amrah ta fara magana ya kasa fahimtar inda maganar tata ta dosa, bu e baki yayi da niyyar tambayar ta su waye suka cuce ta in sai dai kuma take ya fara ganin asar wajen da Amrah in take zaune ta fara zaizayewa, a hankali sai ga wani rami ya bayyana a wajen take kuma Amrah ta shige cikin ramin, shigewar ta keda wuya asar wajen ta koma tare da ha e kan ta. A dai-dai wannan lokacin kuma Anwar ya farka daga wannan mafarkin da yake gaba aya jikin shi ya ji e sharkkaf da gumi. ewa yayi zaune cike da umbin mamakin wannan mafarkin da yayi Shin mai yake shirin faruwa ne dashi?, Shin mai yasa Amrah take yawan zuwar mishi a cikin bacci?, Shin su waye suka cuce ta haka har take i irarin aukar fansa. Ganin bashi da amsar tambayar tashi ko aya ne ya sanya ya tashi tsaye tare da shigewa toilet ya auro alawla sannan ya fito. Sallah ya zo ya tayar kafin kuma daga bisani bayan ya idar ya aga hannun shi ya fara addu'a, sai da ya yiwa Afrah addu'a sosai kafin kuma daga bisani ya tashi ya koma ya kwanta zuciyar shi cike da zulumi. *MANGA* _Comment_ _Share_ _Fisabillillahi_. *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ *SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA*: _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke ina son ku fisabillillahi_ . *Free book* ------------------------------------------- *Bissimillahir rahmani rahim* *006* ____________________________ Yau kwanan su Anisa da Amira uku a gadon asibiti kuma a yau ne likita ya sallame su suka koma Hostel. Sai dai har zuwa yanzu mutuwar Azra tana nan a cikin zukatan su ta kasa goguwa duk da kuwa mutuwar daman ba wani lokaci ta auka ba. A cikin kwana biyu in da suka yi a asibiti babu wani abun tsoro da ya sake razana Anisa in tun na ranar da taga wannan jinin, sai dai kuma kullum zuciyarta cike take da fargaba da tsoro. Gashi sai tayi niyyar sanarwar da Amira abun da ya faru ranar can in sai taji bakin ta kamar an sanya zare an ulle shi. Komawar su Hostel in da kwana biyu aka kafe musu time table in exam wanda hakan ya sanya Suka du ufa wajen karatu ba kama hannun yaro. Rana bata arya sai dai uwar iya taji kunya,kamar yadda aka kafewa su Anisa circular in exam in to yau ta kama ita ce ranar da zasu fara exam. Babban abun da yafi aurewa Anisa kai kuma ya tsorata ta,bai wuce karatu da idan sun yi tana shiga akin jarrabawa zata ji ta nemi komai ta rasa kamar ma ba'a ta a koya mata ba. Wannan abun ba aramin tsorata ta yake ba domin kuwa tun tana ganin abun kamar wasa har ta zo ta fara tsorata da lamarin. Yau ma kamar kullum zaune suke ita da Amira suna karatu, ago kai Anisa tayi ta kalli Amira sannan tace. "Amira nikam akwai wani abu da yake aure mun kai wanda na rasa yadda zan yi". Ajiye littafin hannun ta Amira tayi sannan tace "Anisa wannan wane abu ne haka?, kar ki manta lokacin da muke, wannan lokacin ba lokacin da zaki na sanya abu a ranki bane domin kuwa kin fi kowa sanin cewa daga wannan jarrabawar da muke rubutawa sai ta kammalla makarantar mu". Ajiyar zuciya Anisa ta sau e sannan tace "Hmmm Amira kennan!, wallahi a wannan halin da nake ciki jarrabawar ma ba lalle na ci ba, domin kuwa kullum da kike ganina ina karatu ne kawai amma da zarar na shiga akin jarrabawa komai yake wace mun na rasa mainene dalili". Anisa ta arashe maganar kamar zata yi kuka. "Subhannallah Anisa mai nake jin kina fa a haka!, dan Allah ki bar wannan maganar ma yanzu ba wasa ne ya kamace mu ba". Amira ta fa a tana kawar da kai gefe domin kuwa duk a tunanin ta Anisa kawai wasa take mata kasancewar ta san wacece Anisa a kaf cikin awayen su tafi kowa nacin karatu, idan har za'a yi exam to ba wanda yake finta ci daga Azra sai ita sune warin mate in nasu wanda kowa ya san arin na su duk da kuwa ita ma Amira ba baya ba wajen ari. "Amira kennan kina aukan wannan lamarin kamar wasa ko?,wallahi ba wasa nake miki ba amma koma mainene result zai nuna" Ta fa a tana mai mi ewa ta shige toilet ganin