Sashe 21
Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yiwa Amrah ya sata ta an fara jin sau in damuwar da take ciki. Sai dai kuma kullum daren duniya fa Amrah da tunanin wannan message in ta ke kwana ta ke tashi, sai ta yi kamar zata yi Anwar zancen sai kuma ta fasa. Yau Anwar ya ira Amrah yake sanar da ita cewar zai zo shi. Wanka ta yi sannan ta an shafa powder da lipstick a bakin ta sai an kwalli da ta zizarawa idon ta. Kamar yadda ta saba shiryawa ta yi cikin doguwar riga da dogon hijab har asa, sai dai fa kana kallon fiskarta zaka fahimci ta rame sosai. arfe hu u dai-dai Anwar ya ira ta a waya ya sanar da ita arasowar shi. Tun da ta fito Anwar ya kafe ta ido yana mamakin ramar da ya gani a fuskar Amrah Da sallama auke a bakin ta ta arasa wajen Anwar in da yake tsaye a jikin motar shi, ita ma jingina ta yi a gefen motar tare da cewa. "Barka da isowa ranka ya da Ganin irin kallon da Anwar in ya ke mata ne ya sanya ta tsarguwa da kan ta in da ta shiga kallon kan ta tana duba ko wani ba on abu ya gani a jikin nata. "Amrah mai yake damun ki?". Anwar ya fa a fuskar shi da alamar damuwa. Duk yadda Amrah ta so ta oye damuwar ta ta abun ya gagara, in da kamar jira take kawai sai gani Anwar ya yi ta fashe da kuka. "Subhannallah Amrah meye haka kuma?, Mai yasa ki kuka, dan Allah ki sanar dani in har ba so ki ke nima na yi kukan ba, dan Allah kiyi shiru". Cikin kuka Amrah ta dubae shi sannan ta bu i baki tace. "Ya Anwar......". Sai kuma maganar ta katse sakamakon kukan da ya ci arfin ta. Anwar kam idan hankalin shi ya yi dubu to gaba aya ya dugunzuma, cikin tsananin tashin hankali ya kamo hannun ta abun da bai ta a yin attempting ba amma yau saboda yadda hankalin shi yake a tashe sai gashi ya kamo hannun ta, cikin rawar murya ya ce. "Amrah Dan girman Allah ki yi ha uri ki sanar da ni mai ya same ki?, Amrah ko ni na ata miki rai ban sani ba". "Ya Anwar dan Allah ko bayan raina ban yadda ka ci amana ta ba,ya Anwar ko da asa ta rufe idona dan Allah ya Anwar kar ka manta da soyayyar mu, kar ka manta da al awarin zukatan mu,ya Anwar ina jin wani irin abu a asan zuciyata, ya Anwar ina jin kamar ba zan yi tsawon rai da har zamu cika burin mu ba, ya an........". Kukan da ya ci arfin Amrah ne ya hanata arasa maganar da ta yi niyya in da gudu kuma ta wafce hannun ta daga na Anwar sannan ta shige cikin gidan su ta bar Anwar tsaye kamar mutum-mutumi. in irin tsananin tashin hankali da Anwar ya shiga a wannan lo kacin ata lokaci ne sakamakon jin kalaman Amrah Wayar shi ya aga ya shiga iran layin ta amma ba'a aga ba. Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine kawai abun da bakin Anwar ya shiga maimaitawa, da yar ya tattaro duk wani sauran arfin halin da ya rage mishi sannan ya bu e motar shi ya shiga tare da kifa kan shi akan sitiyarin motar, Anwar bai yi auni ba sai jin wasu hawaye masu umi ya yi sun shiga gangarowa ta kuncin shi. auki tsawon lokaci a cikin motar domin kuwa shi kan shi ba zai iya fa in iya lokacin da ya auka ba a zaune a motar yana kuka kamar mace. Kafin daga bisani ya zaro wayar shi ya ara dialing number in Amrah in sai dai a wannan karon ma bata auka ba. *MANGA* Comment Share Fisabillillahi. *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA*: _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk in da ku ke ina son ku fisabillillahi_. *Free book* --------------------------------------------- *Bissimillahir rahmani rahim* *016* ______________________________ Da gudu Amrah ta arasa shiga cikin gidan na su cikin kuka ta shige cikin aki ko ta kan Gwaggo Sa'adatu ba ta bi ba da take zaune a tsakar gida. "Subhannallah mai zan gani haka?, Amrah!, Amrah!" Gwaggo Sa'adatu ta shiga wala mata ira cikin tsananin tashin hankali. Shirun da ta ji Amrah in ta mata bata amsa ba ne ya sanya ta mi ewa da sauri ta bi bayan ta, tana cigaba da wala mata ira, amma shiru Amrah kamar bata jin ta. Shigar Gwaggo Sa'adatu akin ta tarar da Amrah a kwance a kan katifa ta yi ruf da ciki tana dirzar kuka kamar ran ta zai fita. "Amrah lafiya kuwa?, Mai zan gani haka wai?, Mai ya faru da Anwar in?, Ko wani ne ya mutu?". A lokaci guda Gwaggo Sa'adatu ta jefawa Amrah wa annan tambayoyin tana arasawa bakin katifar da take kwance in, sannan ta ago kan ta ta aura a kan cinyar ta. Jin shiru Amrah bata da niyyar amsawa Gwaggo Sa'adatu tambayoyin da take mata in ne ya sa ta ara cigaba da magana. "Amrah ki bu e baki kimun magana wani abu ne ya faru da Anwar in?, Ko wani ne ya mutu?". Sai a sannan Amrah ta ago kan ta daga cinyar Gwaggo Sa'adatu in sannan cikin kuka ta bu i baki ta fara magana. "Gwaggo ko aya ba wanda ya mutu, sai dai ni kuma da alama lokacin mutuwa ta ya arato dan haka Gwaggo idan na mutu ku bini da addu'a kawai". Ta fa a tana ara fashewa da kuka. Hankalin Gwaggo Sa'adatu idan ya kai dubu to gaba aya ya tashi da sauri ta fara magana. "Subhannallah Amrah wannan wace irin magana ki ke fa a haka?, A duniya ai ba wani bawa da ya san lokacin mutuwar shi sannan duk wanda ki kaga ya mutu to lokacin mutuwar shine ya yi, dan haka kar na ara jin wannan maganar a bakin ki". "Gwaggo dole nace lokacin mutuwa ta ya zo tun da ana shirin raba ni da rayuwa ta, ana shirin rabani da farin ciki na, Gwaggo wallahi mutuwa zan yi idan aka rabani da Anwar domin kuwa shine rayuwa ta". Amrah ta fa a tana ara tsananta kukan ta. "Innalillahi wa'innailaihi rajiun, wai Amrah kan ki aya kuwa ki ke wa annan maganganun?, Tukunna ma waye zai rabaki da Anwar in?". Hannu Amrah ta sanya ta share hawayen idon ta kafin ta kwashe duk abun da ya faru a kwanaki biyun can na message in da ta ga an turowa Anwar in ta sanarwa da Gwaggo Sa'adatu sannan ta ara da cewar. "Kinga kuwa Gwaggo dole nace ana shirin rabani da rayuwa ta, Gwaggo nasan halin anmatan yanzu zuciyoyin su tsoron Allah yayi aranci a ciki, kan su kawai su ke so, dan haka ni nasan tun da har aka fara turowa Anwar irin wa annan sa onin to ana daf da shiga tsakani na da shi". Shiru Gwaggo Sa'adatu ta yi tana jin ta har ta dasa ayar tsayawa. "Yanzu Amrah saboda wannan dalilin ki ka bi ki ka aurawa kan ki damuwa, ki ka hana kan ki sukuni,to wallahi ni dai abun da zan fa a miki shine duk tsananin da zaki shiga a rayuwa kar ki manta da cewar Allah shi yake bayarwa kuma shi yake hanawa, a yau idan ki ka ga baki auri Anwar ba to daman tun fil'azal Allah ya addara cewar shi ba mijin ki bane ba, sannan idan har Allah ya addaro cewa zaku rayu da Anwar a matsayin mata da miji to ba wani rai a doron asa da ya isa ya zamo shamaki ga kasancewar ku ma'aurata, dan haka ki mi a lamuran ki ga Allah ki dage da addu'a kina fa a mishi bu atun ki a sannu bisa hankali zai amsa miki domin kuwa shi baya bacci". Da wa annan kalaman Gwaggo Sa'adatu ta samu ta rarrashi Amrah har ta ji zuciyar ta ta an mata sanyi amma kuma duk lokacin da ta tuna da wannan sa on da ta gani a wayar Anwar in sai ta ji gaban ta ya tsananta fa uwa, sai dai kuma kamar yadda Gwaggo Sa'adatu ta bata shawara haka Amrah ta mi a lamuran ta ga Allah ta mi e tsaye da addu'a ba dare ba rana. ***** angaren Anwar kuwa haka ya cigaba da iran wayar Amrah amma shiru ba amsa, ana cikin haka ne Umar ya ullo daga hanyar gidan shi ya zo zai shiga gidan na su ya ga motar Anwar a fake a ofar gidan. arasawa wajen motar ya yi tare da wasa glass in motar, abun mamaki mai Umar zai gani Anwar ya gani yana kuka ga hawaye sha e-sha e a idon kamar mace. "Subhannallah Anwar lafiya kuwa mai ya same ka haka?". Usman ya fa a yana bu e murfin motar Anwar Kallon Umar Anwar ya yi sannan ya sanya hannu ya share hawayen idon shi tare da cewa. "Umar dan Allah ka taimaka ka dubo mun a wana hali Amrah ta ke ciki, wallahi idan ban san a halin da take ba ba zan iya tafiya na bar ofar gidan nan ba, Umar dan Allah ka taimaka mun". Anwar ya arashe maganar cikin rawar murya. Kallon shi Umar in ya yi cikin tsananin mamakin maganganun na shi kafin ya ce. "Anwar mai ya faru da Amrah in?" "Wallahi Umar ban san mai ya faru da ita ba, ni dai muna cikin hira kawai na ga ta fashe da kuka sannan ta tashi da gudu ta shige cikin gidan, iran duniya na yiwa wayar ta amma ba ta agawa, dan Allah ka taimaka ka gano mun ita ma idan ni na mata wani laifin wallahi zan je har asa na dur usa na bata ha uri". Umar yana arasa jin abun da Anwar in ya fa a ya juya ya nufi cikin gidan na su dan gano halin da Amrah in ta ke ciki. A bakin murhu Umar ya tarar da Gwaggo Sa'adatu in da ya shiga tambayar ta ina Amrah ira