Sashe 9
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yanka guda hudu. Duk haduwan abincin bai wani ban shawa,awa ba don lokaci guda gidan naji ya fita min a raina badon komai ba sai fahintar da nayi cewa mazauna gidan ba zaman lafiya a tsakaninsu don har mu baki daga zuwan mu abin ya fara shafan mu. Saboda yanayin jikina na rashin sabo da mota ban ci wani abincin kirki ba sai halimatuce ta zauna ta kwashi abinta bandai da yunwar nama don zance gidan mu Alhamdullahi akan nama don har gobe baba na shiga kauye yayi kwanakinsa a can yana aikinsa mudai iyalinsane ya dawo damu cikin katsina inda gidansu yake muna zama don inganta rayuwan mu nan gaba da yan uwa suka inmasa yayi. Amma part din mu na can kauye yana nan indan yaje nan yake zama sunso su mamaye wajen amma dole suka barshi da abinsa tunda sunsan yana zuwa lokaci lokaci kusan shi yafi rayuwa ma a can din. Hakan yasa idan zai dawo zai dawo da nama man shanu nono da sauran tarkacen rugan dana kauye har sai inna tabawa mutanen arzikinta suma sun lakaci arziki a wajenta. Wanan yasa banda kwadayin irin abubuwan nan nan shigowan mai dakin yasa na dan muskuta ina gyara zama saita kallo mu kafin ta mayar da dubata kan abincin dake gaban mu din aje tana fadin.. Ya kuma bakici abincin ba ko har yanzu jikin ne dai cikin sanyin muryan ayadda take magana cikin yanayin sanyi da kamala tare da mutumta mutum. Naci gwaggo kalman ya fito min a baki don sanin cewa ita din alakar uba muka hada da ita don haka ta zamo gwaggona ke nan da ace ta uwace sai in kirata da mama ko wani lakanin daya danganta da uwa. Murmushi ta sauke a fuskanta kafin tace dani toko jikin nakine bai sake ba har yanzu zaki kara shan ruwan shayi a hada maki kada ki kwanta da yunwa a cikin ki ta tambayeni cikin tsureni da idanuwanta daga inda take tsaye din gefen gadonta. A,a nakoshi gwaggo na kara fada sai naji ta sauke ajiyan zuciya ta juya can kuma ta juyo tana kallon mu tace idan kun gama ga daki can a gyare kuje can ku kwant zakufi sakewa bisa ga nan din kema a nan zaki kwana ke nan ta tambayi halimatu din dake tattara dan kwaran shimkafan da suka zube a kasa. Ta dago tana fadin ehh a nan zamu kwana tare don can inda dada take naji sunce kada a bata masu daki da kazanta sai ta sake murmushi tace kayya ku kananan yarane da zaku bata waje kuje ku kwanta ku huta ta fada tana fita ganin hakan yasa na mike nabi bayanta. Dakine hadade mai kyau da katon gado da shimfida har da mirro a cikinsa tace kuyi zamanku nan abin ku har ranan da zaku koma kalman mun gode ya fito a bakina tace da akai maku me kuma gidan kune fa nan din . Har takai kofa ta juyo tana fadim idan fankan yayi yawa kunsan dai yadda zaku rageshi ai muka amsa da mun sani ta fice ta barmu a dakin lokacin halimatu ta kalloni tana fadin wai matar arziki inda wacan muka samu kawai a gidan nan da iyalinta yaya zamuyi ke nan ? Ya kuwa haka dai din zamu zauna a takure muma na fada ina bin dakin da kallo wai dakin baki ke nan kamar na wata mace don Allah halimatu ta fada nace wanan dakin ne na baki tace ehh,mana. Bakiga ko acan cikin irinsa aka sauke mu ba amma naji yarinyar na fadawa uwar da turanci ko ta dauka ban bokone wai in babansu ya dawo amai damu boys quarter. Allah ya kyauta yanzu damuwata shine inda zamu samu kayan canzawa tunda kayan mu suna wajen Dada mun barsu na fada ina dan dube dube gashi wanda na bata da amai bansan inda aka kai munshi ba. Haka muka kwanta duk yadda halimatu taso muyi hira na kasa sakin jiki inyi haka din saidata fahinci cewa nayi barci ta kyaleni sai dana falko da darene na samu an kashe muna fitilan dakin halimatu na tayar ta rakani zuwa bandaki na kewa bamu kara falkawa ba saida safe da mai shiyan ta tayar damu daga barci don muyi sallah bayan hakan namu kara jin duriyanta ba kuma again. Ban iya komawa barcin safe ba don haka dana gaji da kwanciya na mike na fito gidan tsit yake babu kowa ba wani motsin wani mahaluki kuma Allah ya taimaka naga tsintsiya a kofan dakunan na dauka na sharo ko ina na part din don zaka gane iyakar part din don a rabe suke falon gidan yana tsakiya daga sama kuma benene na maigidan a tsakiyansu sama. Tsab na gyaro ko ina kafin nafito har ta waje main falo dinsu shima na gyarashi tsab na dawo dakin har lokacin halimatu tanata kwasan barcinta wanka nashiga rashin sanin heater a ban dakin yasa na watsa ruwan sanyi a jikina. Na fito ba mai da zan shafa duk suna cikin jakata inna tayi min guzirinsu har kayan shafa na yan mata don na shafa ba sai na nema a wajen su ba inna ta saka min akayana. Don inna irin mutanen nan ne masu kula da kansu suna rike kima da darajansu talaucin mu baisa ta zubar da kimanta ga kowa baka taba jin taje wajen wani yin karamin murya kan neman wani abin rayuwa daya shafi gidanta. Haka kuma bata da lokacin zama yin kananan magana da mata kan saka kansu kan abinda bai shafesu ba har su daukarwa kansu zunubi donshine ba zakace ga abokiyar fadan ta a shiya ba indai innace. Yaushema taje wani gidan balle ta saka ido ga abinda mutum keyi koda yaushe kake nemanta tana kofanta a zaune inda Allah ya ajeta dan dama kwana bibiyu zata shigata gaida Dada ta dan kumsa alheri takai mata shine kawai yawan fitanta a cikin shiya ita. Daga dakin da nake zaune nayi zaman tagumi ina tunanen duniya najiyo muryan mai shiya tana fadin yau wani dan albarka na samu yayi min wanan aikin haka ? Can na danji kara bude part din sai kuma ta dawo ta nufo dakin da muke din zaune ta turo da sallamanta nayi firgigit na juyo ina dagowa kamar mara gaskiya har kasa nakai ina mata ina kwana. Ta amsa tana saye da hijjab sky color har kasa a jikinta sai dogon rigan daga ciki dake baiyana kansa lokaci lokaci ga kamshi na dan busowa a jikinta har inda nake take fadin kardai ince duk ke kikayi wanan aikin haka tunda safen nan. Na dukar da kaina tace Allah yaiwa rayuwanki albarka da alaman tarbiyan da matar yaya ta baki ke nan kike nunawa ga halaiyanki ki kara tsare kanki kinji duk dan mutunci kallo daya zai maki yasan kin samu tarbiya yadda akeso. Ta juya zata fita lokacin nace gwaggo cikin sanyin murya sai ta dagata ta hanyar juyowa tana fuskantana nace dama mai nake son in shafa nayi wanka maina danazo dashi yana cikin kayana a wajen Dada. Au har wanka kinyi da safen nan injin dai kin kunna ruwan zafi na manta sam na kunna maku heater ai da nashigo jiyan ta fada tana kallon hanyar bandakin. A,a ruwan sanyin dai na watsa na fada lokacin halimatu dake kwasan barci duk abin nan da mukeyi ta motsa ta mike firgigit tana gaida ita da kwana ta amsa kan ta juya ta fice a dakin. Kizo ki karbi man ta fada bayan takai kofa halimatu kuma ta shiga bandaki na mike zuwa dakin nata na samu tana bincike abu a wardrobe din ta sai ga man shafi babban gora ta dauko tare da wani marron din dogon riga yar kanti material cikin irin kayan data kan tara idan sunyi tafiya rigan ya burgeta duk da bata da diya mace ita a rayuwanta. Diyanta mazane shidda cip a duniya biyar a wanan gidan ta haifesu dayan wanda shine babban mahaifinsa ya rasu tun tana da cikinsa shima din irin auren hadin da zurian mu sukeyi akai masu. Bayan ta gama wanka tana zaman zawarci saiga baba na kano kuma ya nuna yana sonta sai kuma aka kara dada auren gida a kansu din ashe rabon zuriane haka tsakaninsu sai gashi ta haifa mashi diya biyar duka maza. Wanda ya kara haddasa kiyayya a tsakaninsu da abokiyar zamanta hjy malka wace ita ma dai din a cikin dangi take duk auren zamane a tsakaninsu amma kuma tunda zaman kishi ya hada a yanzu sai aka kawar da zumuncin aka kama hanyar shedan ana fafata zaman kisantaka zallah a gidan wanda har hakan ya shafi yaransu. Bai tsaya a nan ba don har wasu dangi abin ya shafa ashe muma dai don muna yarane bamu san dawan gariba har muka yarda ta jamu zuwa sashenta wanda niko a lokacin kwadayin kiran yar uwar mahaifina take na kusa data furta min yasa na karkare yarda da komai nata. Wanda hakan ashe baiwa hjy marka da yayanta dadi ba a take suka dauke mu munafukan bakinsu kamar yadda suke daukan duk wani wanda yazo ya danganta da hjy kubra din. Wanan kuma shine dalilin zuwan Dada da wuri kafin buki don yana son aiwa abin tufka tun kan jama,an arzikinsa su taru su hautsana masa gida da kaidinsu na mata don yasan yan uwa da abokan arziki zasuzo sha,anin har wanda bai taba zuwa ba labari yakeji a yanzu zaizo yaga abinda ke wakana a gidan shima. Ashe a daren jiyan bayan fitan mu sun fara fafatawa don ya gabatar da zancen a gabansu gaban Dada din don ko muna fita tace ashe har da yara sun iya munafunci to an riga da an kulla masu tun a gida kan suzo ga inda zasu sauka mana. Lokacin ya juyo yana fadin wanan wani irin maganace kuma yaran nan me suka sani da zaki fara fadin haka akansu yarane fa wa yan nan kanana duka duka har yaushe suke wai ? Dada da sai lokacin tagane me ake nufi tace Allah sarki wai su Abu take zance dama in hakane ai laifinane da muka iso baku gidan yarinyar ta jirkita da yawa naji tsoro nace a kira