← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 61

Sashe 28

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kan mashi ya kwashe komai ya rabar. Wanan kalman ya harzuka daddy din da ita har yace ke malka kije dai yau na sakeki tunda nagane badon Allah kike zaune dani ba dai. Dama kowa yasani an fada kuma tunda kika aureni cewa don dukiyana kika aureni tunda da farko aida banda komai kina kikayi sai daga baya dana dan fara dagowa kuka shiga kuka fita har na aureki keda iyayyenki. Ita kuma tace dashi dadin abin dai ba ita kadaice iyayyenta suka iya shige da fice ba wajen malamai shima nasa iyayyen ai sun iya don suna mata kuma tasan komai kan hakan. Yanzu ma mommy dince ta shigo gidan ta tayar da zancen tana surfawa daddy din zagi shi da yan uwa da mugun kalamai wanda ran Dada din ya baci na yadda tazo tana aibanta mata zuria har yakai ta tunzura ta biyewa kalaman nata sun rikice. Ban shiga ba ina ajewa na juya zuwa part dinmu koda naje ban fada ba sai da ta jiyo hayaniya ta fito ta samesu ida Dada ke fadin ko an raba an baki kason nawa zaki samu marka ? Mai yaya maza a gida ta kyale taja bakinta tayi shiru saike mai gayar yaya mata saboda kwadayi zakice sai an raba dukiya anbaki kar ya kare. Su yaya matan ba mutane bane Dada diyan suka fada nan dai suka tararwa Dada din da yake ta iya ta biye masu suna maida kalamai a tsakaninsu din. Anty Nafisa ta fito da tsohon cikinta daga daki tana fadin haba mummy wanan abin kunya da kike ja muna fa daddy fa hakkin zumunci yake kokarin fitarwa yan uwansa . Ina dai kudin nan nasane shiya nemi abinsa don haka ki kyaleshi kisa masa ido ko duka zai raba masu kudinsane ai mommy. Kuma ya fada min cewa kwangila yayi mai tsoka ya samu alheri ya roki Allah ya yayi mai mafita dasu har dabaran yin hakan yazo masa. Don Allah mommy ke ba mai taimaka masa bane wajen yada wanan manufan nasa na alheri a garesu tunda kema harda yan uwanki aikaiwa alherin nan bafa nasa kadai yabawa ba kudin nan har naki yan uwan. Don daddy yaiwa yan uwansa hidama da dukiyarsa a yanzu shine zai rage dukiyansa kome har kuke wanan abin kunyan kuma a yanzu bakuyi saki a tsakanin kuba a da sai yanzu yanzun ma din ace akan alheri mum kada abinda yan uwa ke fada a kanki ya zamo gaskiya fa. To uwata imun fada keda kika san gaskiya har kike fada ni kinsan bansan wanan ba ai saikin fada a yanzu zan sani tunda dama yan uwana fadi a kaina . Ayai kiyi hakkuri mommy ban fada don ranki ya baci ba ai don Allah ku bar wanan abin na zauna yau da safe da daddy akan yayi hakkuri ya barki ki dawo dakinki ki zauna yanzu kuma ki shigo kina wanan masifan ai kinsan ba zaiji dadin hakan ba har ya hakkura din. Kallon hjy mum tayi datake tsaye yar ke wanan kalamin a gabata sataji haushin hakan nan take ranta ya kara baci ita ko Nafisa din ganinta bai hanata fadan abinda take fadawa uwar ba don hakane uwar taji mugun haushi tayi cikin diyan da zumar dukanta sai muryan danta mukaji yana fadin kada ki tabata mana mommy. Kinsan dai anty Nafisa ba zata fada maki karya akan daddy ba nima na sameshi ya fada min sun zauna da ita don shi kikaji na kyale zancen hakan . Alokacin hjy mum ke bawa Dada hakkuri ta fita part din ta koma nata don Allah abar zancen a sasanta a tsakani tunda yara har sunsa baki a zancen. Wani juyowa da yayi ya watso muna harara hakan yasa da sauri na labe a bayan hjy mum dake kusa dani tsaye ina satan kallonshi ta bayanta. Ku,kuma me kuka tsaya saurare ya fada a cikin tsawa yana zare idanunsa garemu hakan yasa hjy mum fadin kubar wurin nan na juya da sauri na riga kowan mu fita daga part din ni dai har nakai ina jin muryan mommy a lokacin . Barcine ya daukeni a fslon hjy mum din ban sani ba wanda har suka shigo suna dan hayani hakan ya tayar dani daga barcin dana samu inayi din a lokacin. Saidai ban motsa ba illa ido dana bude yayin da nake gane da yaranta take wanan zancen a lokacin don muryoyin su da nake ji na gane hakan tana fadin lalai yanzu na yarda hjy malka akwai jahilci a lamarinta sosai. Mum ki daina biyewa wanan macen kin dai ji yau metake fada da bakinta yau din ma ni sai naga kamar bata cikin hankalinta babban ya fada yana kallonsu. Ba dole ta koma haka ba tunda tana ganin hakan ba zai taba faruwa ba kuma ya faru yanzu zata karasa halaka kanta wajen yan bori da yan tsubu tana ganin wani ya saka hakan ya faru gareta. Ba,abinda zai sameki mum tunda baki mata ba ya fada yana mikewa lokacin wayana yayi kara na mika hannu ina dauka duk suka kalloni danna dauka nayi ina fadin inna ina wuni ta amsa min sai kuma na sake fadan gata na mike ina mikawa hjy mum din wayana. Ke ki kawo min abinci ya Nasir ya fada a lokacin da nake shirin mike tsaye daga gefe ya Addel ke fadin baka san sunan ta bane yau kuma zaka kirata da Ke. Baidaiyi magana ba nima ban iya amsa mai ba na shige ciki bandaki na shiga na kewaya kafin na hada mashi abinci nakai mashi wayan nawa har lokacin tana hannun mum tana bincike a cikinsa. Nasan tana dubane kona saka wani abinda bai dace ba da shekaruna baikai dauka ba a lokacin wanan bashine karon farko da hjy mum takan dauki wayana ba kusan ko yaushe tana dauka tayi bincke a cikinsa. Alhalin banda komai a ciki sai yan cartoon da film din hausa irin na ibro yan gajeru na ban dariya number kuma baifi na mutum goma bama a lokacin da nake dashi na iyayyena sai nasu mum din dana kawayena shima ba mai yawa ba dai hakana. Zama nayi ina fadin wallahi wancan mugun ya firgitani mum na dauka dukan mu zaiyi ai yadda ya kallomu din nan tace hauka yayi da zai dukeki kawai bacin raine suma yake damunsu a yau yadda uwar keyi din nan. Koda yake shi dama yana yarda da haukanta ba kamar Nafisa yake ba don ita tun tana karama bata yarda da wanan shirmen nasu dan dama shi haka kawai yakan dauki fushi dani wani lokaci kamar ba namiji ba. Ya Nasir daya fara cin abincinsa ya dago yana fadin wai Hafiz take zance dama ai dama ya bal,balaku tunda gulma kuka iya da kunji kyasham ba,a rigaku zuwa kallo. Dan marairaicewa nayi ina fadin hai ya Nasir ni yaushe nake irin wanan da har kake mun fatan wanan gabjejen katon ya dake shifa yana da saurin hannu hakan yasa nagudu tunkan ya karasa rufe bakinshi. Suka kwashe da dariya Mum tace wai kin ko san wanan ya mari mutum ai sai jinya nace nima tsorona ke nan yasani shan maganin dole ban shirya ba. Motsaraciyar banza watau mukika raina dama ko ince ni da bakya tsoro nace kaima ai ina tsoronka yaya na daifi tsoronsu su biyun nan shida ya Addel don ko yaushe fuskansu a daure yakesu. Ni dai ban kara jin zancen mummy ba gashi har yaranta sun fara ba mutane tausayi a gidan don yadda kallo daya zakai masu kasan suna cikin damu da kewar uwarsu. Zuwan su baba gidan ranan sun dade da daddy a falonsa ina ta dakon jin yashigo part din amma har yamma saina gane sun gama ganawa da daddy sun tafi don haka na debe rai ga ganinsa a ranan . Sam mum bata koya min zuwa gidan mu wurin iyayyena ba koda zamuma a tare muke zuwa mu dan dade kan mu dawo gida da tare da ita kuma don haka ban ma samun wani sakewa a yanzu da iyayyena din. Hjy Mum gaskiya tana kokari matuka dani wajen nuna min kauna da sakani hanya ta yadda ba zan wahala a rayuwa ba nan gaba. Ma,ana dai ta mayar dani tankar yar cikinta data haifa hakama diyanta sun daukeni kanwarsu sosai ko don ganin yadda uwar ke min ne son basu son suga ko hjy mum din ta bata min rai balle wani a gidan nasu yace zai saba min sai inda karfin su ya kare a kaina. Muna hutune don haka ba fita muke ko yaushe ba muna gida sai islamiya da yanzu ni kadai keda kokarin zuwa ko yaushe sauran sai sunga dama suke zuwa tunda daddy ba mazaunin gida bane shi . Ranan na dawo daga islamiya na samu mum bata gida nayi mamaki don haka naje part din su ina tambaya suke fada min sun kai anty Nafisa asibiti wai zata haihu. Nayi murnan jin hakan da suka fada din sosai don haka na samu waje na zauna a nan din tunda Dada ma bata nan tare suka tafi da ita donshi na zauna a nan din ina mai mata adduan sauka lafiya a zuciya. Don nasan hakan tun ina karama a kauye da baffa Ado yayi aure wajen haihuwan farko amaryan nasa mai kyau da ita ta mutu abin ya tsaya min azuciyana don na kasa mantawa da hakan. Ajiyan zuciya na sauke kafin na mike na fada dakin anty Nafisa anty Nafisa badai kazanta ba kan na fada a raina don dakin ga komai nan a yashe kasa ko ina ka duba kayane datayi amfani dasu ta kasa daukewa zuwa muhallinsu. Tsab na gyaro dakin har bandaki da ko ina sau daya Asiya ta dan lekoni don jin motsina datayi a dakin taga ko waye a ciki take fadin au kece ashe kina da aiki kuwa indai dakin nan ne . Don har pant sai kinci karo dashi a dakin nan indai Anty Nafisace zaki ganta a waje tsab amma a gida kuma kazan kazan da ita bata daga hammata ki shaka wanan ya san ban dariya ta fita tana tabe baki wai kazanta ance gwano baya jin warin kansa tunda
Chapter 28 · 0% Book details