← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 61

Sashe 52

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nan su dauka koka fara bita zauzaune tun yanzu nafisa ta rada masa a kunnensa. Wani haushi da takaici ya kara rufesa wajen wai ana nufin mata biyu daddy ya aura masa lokaci guda koko dayan daya saninece data zamo mashi alkakai a yanzu ? Nan yaji tururuwan jama,a suna shigowa da guda da ihu abinda yayi hating duk mata sun ruda gidan ga koke koken yaransu yana tashi duk da ya rufe dakin amma yana iya jiyo muryansu a nan din. Sai bayan wani lokaci ya daina jin muryoyinsu tare da jin tashin motocinsu suna barin gidan duk da hakan bai fito ba sai sha daya da wani abu yazo ya rufe gidan ga baki daya yana jan tsoki. Yar gatan amarya yar lele itace angonne ke zuwa sayen bakinta don nikan bayan wucewan yan uwa mikewa nayi na nufi kofa na saka key na dawo na rage kayan jikina na shiga bandakin na dan watsa ruwa tare da dauro alwala. Na dade zaune ina addua kafin na mike na hau gadon saboda zuwa lokacin zuciyana ya dake ya bushe ina jin kaina kamar bani bace kamar ban iya kai safe lokacin. Allah da ikonsa ina gama addua na kwanta bansan lokacin da barci ya daukeni ba sai falkowa nayi na ganni kwance cikin hasake sai kuma lokacin na tuna da inda nake kwance din. Zabura nayi ina salati nakai duba ga kofa na tuna nayi masa key kafin in kwanta na samu na mike da kyar na koma bandakin na sake dauro alwala nazo na sake tayar da sallah. Hannu sama ina kuka nake rokon Allah daya hausheni kan duk wani mugun nufin da hafiz kedashi a kaina na zama matanshi danayi yanzu din. In nayi adda in tsaya inyi kuka in kara kuma daga hannu ina rokon Allah in kuma koma tunanen duniya a haka wani barcin yayi gaba dani ba tare dana sani har gari ya waye sosai kafin na zabura na mike ina sallati na sake shigewa bandakin na dauro alwala. Haka na koma kamar zautata a ranan ni kadai a daki gashi ba motsinkowa a gidan koshi azzalumin banji motsinsa ba na kuma kasa bude dakina ina jin tsoro don bansan da wace zaizo min ba lokacin kuma . Ga ba waya a hannuna wayata na dakin mum saman akwati na aje lokacin da zan saka abayan zuwa wajen walima tun lokacin ban kara bita kanta ba wayan samirace a hannuna kuma karama ita nake ta jagula tunda nazo. Sai wajajen karfe daya naji anata dukan kofa hakan yasa na daure na bude wata gwaggon mune yar mum ce ita take fadin tun dazun ake zuwa ana fadin kofa a rufe. Uwarki nacan ta rude dole ta taso damu muzo mu dubaki ko wani abune ya sameki gashi yanzun muke jin wai mijin naki ya koma tunda safe inda yake aikinsa. Wani dadi naji duk da ban cikin yanayi mai dadi a lokacin amma jin hakan yasa zuciyana sanyi lokaci guda nace Allah sarki mum nasan ta damu sosai ga wayana na barshi a dakinta tun jiya din. Gwaggo Rahinatu tace ai mun gani tun jiyan ta dauka ta boye maki shine ga abinci can a falo tace zuwa yamma zata lekoki ta ganki ai yanzu ma munzo duba ko lafiyane anata zuwa kofanki yana rufe. Basu tsaya suke fada min ai an wuce da amare tun safe yanzu ai kila sunkai don gobe zasu dawo masu kai amaren nikan duk sama sama nake jinsu. Saida suka wuce naga abincin ganin kayan abincin yasa nagane daga hjy mum suka fito ba part din mummy da yanzu ita keda alhakin ban abunci don ina karkashin danta da zama yanzu. Sai lokacin na samu daga kai na kalli tsarin gidan gidane mai kyau nagani na fada don ba inda wanan gidan yake da maraina gaskiya a wajena nikan. Abincin na bude na dan tsankwara nace bakina ba dadi don haka banci wani abin kirki ba na aje cokalin na zauna nan ina tubane hakan yafi mun na fada a raina. Da zaman dan cin mutuncin da baisan daraja iyayyenmu ai gara yayi gaba hankalina yafi kwanciya da hakan da zamansa don bansan iya abinda zai iya min ba idan yana nan. Allahne ya karbi addua na dana kwanayi a dakin ya iza min shi gaba na fada a zuciya shigowan su Samira ya kara dauke min hankali nan suke min hiran abubuwan daya faru bayan bari na gida din. A bakinsu nake jin wai yace next week zai dawo ba dadewa zaiyi ba dama bai samu hutu ba yadai zone kawai ayi buki dashi ya koma. Ni dai ban tsuka ba shigowan su mum dina ya dauke min hankali saidai mum din a yarda na ganta ranan duk ta zabge tarame kamar wace tayi ciwo a dare daya. Abubuwa sin ma rayuwanta yawa don bata saba hakan ba sai gashi da zaizo mata yazo mata da tashin hankali kowa najin abinda ke damunsa har daddy uban gaiyan. Sunyi min nasiha sosai wanda duk cikin nasihan hakkuri da biyayyan aure shine kan gaba duk wani kalami na kowa da zai fada shine inyi hakkuri wata rana sai labari insha Allahu. Ta ban wayana tare da fadin duk da nasan baki da kawayen banza amma zan kara ja maki kunne don Allah ki kula akwai hakkin aure akanki yanzu mamana kada ki yarda ki canza rayuwan ki nan gaba don Allah. Da kuka muka rabu yan uwa suna bata hakkuri take fada min su samira zasu kwana tare dani in Dada ta dawo kai amarya daga bauchi zatazo ta zauna dani a gidan. Muka rabu cikin rashin dadin rai ranan tare dasu samira muka kwana wanda tun karfe takwas da wani abu na kwanta barci saboda barcin gajiya dake idona. Washegari bamu jira an kawo muna breakfast daga gida ba mu muka girka abinda mukeso tunda akwai komai da aka kawo min nagara na dauka ya Addil zasu ratso kafin su tafi . Sai gashi samira na fada min ai sun wuce tun safe yazo ya sallami mum cewa yana da aiki zai koma a raina nace kowani al,lazi da nasa amanun shi kuma yaya matarsace nasa matsalan rayuwan. Don nasan itace zata matsa mashi su koma a ranan bawai son ransa bane zaisa ya koma dama shi ya Nasir bai samu zuwa ba yana wajen course din aikin daya samu na world bank. Ranan ma dasu Samira din muka wuni muka kwana gashi washegri zasuyi sammako su koma don su Dada sai dare sosai suka dawo kuma bata da lafiya koda suka iso. Haka washegari tunda safe aka turo su samira suka fit suka barni ni kadai a gidan kamar manya sai gidan ya dan fara ban tsoro ganin ni kadaice a ciki. Sai maigadi dake can ta wajen gidan yana aikin gadinsa ba ruwana dashi kuma haka na kwana don mum data kirani tana sheda min Dada jiki yaki har ssibiti aka kaita da sunyi shawara a turo min halimatu ko ya nagani nace su barta zan iya kwana ai saboda karfin hali. Tun daga wanan rana na kama kwana ni daya a gidan tsoron haka kuma ya fice min a raina zansha barcina da safe tunda muna hutun boko a lokacin. Saina gaji zan tashi indanyi abinda zanci daga nan kuma sai dare zan dan nemi abin da zanci in kwanta sai hankan ya fara kwantar min da hankali. Kwatsam saiga mummy da kawayenta wani safiya wai sunzo ganin amarya don basu samu zuwa ba saboda gajiyan buki suna wani dan yatsune yatsune da mede baki kamar sunga kashi. A cikin ladabi na taresu na kawo masu ruwa don shi ke gareni gidan lokacin to ba maigidan balle ya sawo min wani abu ko ruwan nice naba maigadi kudi ya sayo min bag biyar na ruwan don masu zuwa ganin amarya duk daba wasu jama,a ke zuwa ba sai in wuni ma wani bai shigo gidan ba ranan. Yo ga tsiya mune zaki tara da ruwan leda ko haka uwar naki kikaga tana taron baki inda kika baro ? Koda yake ba mamaki hudubar da tayi maki ke nan kike gwadawa a yanzu ai in ba rashin tarbiya ba munyi maki kama da masu shan ruwan yaku bayine a nan. Sai naji dayan matar tace ki barta muko takawo ba zamu shaba ai ruwa na gida mun bari ke dai yarinya dauke ruwanki a nan dama mu ganin gidan dan mu mukazo muyi ba wani abu ba. A take idona ya kawo kwalla dakyar na iy furta kuyi hakkuri mummy shi kadai nake dashi a gidan nan bansan zakuzo ba danayi maku tanadi ai. Lah yar nan ke kuma da sherin da kikazo ke nan batawa dan mu suna kan bai kula dake kome ? Rudewa nayi lokaci guda ina basu hakkuri daba haka nake nufi ba iya gaskiyata na fada amma suyi hakkuri don Allah sai naji mummy din taja wani uban tsuki ta mike tana fadin. Kunga irin abinda nake fada maku ko dama nasan yarinyar nan ba karamin makirci aka kulla mata ba da zatazo tayiwa mutane gashi ko tun ba,aje ko ina ba har ta fara. Don Allah ku tashi muje da wanan abin haushin da muke gani a,a hjy malka ba,a hakana yanzu me yarinyar nan tayi kuma wata daga cikinsu ta fada . Ku tashi muje don Allah da wanan bakin takaicin da muke gani a nan din dama abinda Alh ke so ke nan inga bakin ciki ya dauko wanan yar tsiyar ya mannawa hafiz don bakin ciki ya kasheni gashi kuwa . Ai hafiz din zai dawo koshi yaji wanan rainin wayau da kikai muna ba zai kyale ba ai mune zaki wani tara da ruwan leda kamar kinga gayyan yan kauye. Da kuka na kira mum ina fada mata ashe lokacin suna tare dasu Dada har da anty Nafisa hakkuri mum din ta ban tace wanan shine auren ai mama. Mun fada maki sai kinyi hakkuri ina jin muryan anty Nafisa tana tambaya meya ya faru mum din tace ba komai ta dai ban magana muka kashe waya . Halan mummy ko don naji suna waya dasu hjy Ramatu yau zasuje gidan suga gida na mantane
Chapter 52 · 0% Book details