← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 61

Sashe 4

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yawan shigowa gidan Dada din hira da samun abin tabawa don baka raba gidanta da dan abinda diyanta suke aiko mata. Wanan yasa yanzu da bakowa a gidan mu kona dawo daga school ina gida zaune ina dan aiyukan gida sai suka fara dan shigowa gidan namu wurina muna hira a nan ina aiyukana kuma. Zasu girme min sa,adatuce sai Nabila amma haka muke kawancen namu dasu har yakai ko islamiya ko boko tare dasu muke jerawa mu tafi a wajen su nake jin komai daya shafi family wanda ni ban ma gama sanin yan uwa ba sai yanzune nake sanin wasu. Nan nake jin ashe yawa garemu akwai wa yanda basu zaune a garin amma sukanzo gida jefi jefi tare da iyalansu lokacin sallah ko wani buki haka idan ya taso a family. Zaman mu a nan cikinsu yanzu bazance zaman dadi bane yadda nake fadin su a,a zama daine yanzu wanda yafi muna na baya cikin yanci da sallama babu tsana babu tsangwaman kowa akan mu. Zama na kasanni na sanka zama na cin gashin kan kai abinda kowa ya samu bakinsa saidai babu saka ido irin na kauye na lungun su wance kaza akeci ko kaza aka dafa yau. Ko saka ido akan mu,amulan miji da mata don zaman babban gida irin wanda muka baro a baya zamane na kai mutum wuta idan bawa baiyi taka tsatsan da duniya ba a wanan zaman . Gashi zamane na shagala kamar ba gobe sam ba mai kawo mutuwa a rayuwansa yace wai a,a bari nabar kaza a kwai mutuwa ko wani lokaci zata iya riskana saidai shagala da duniya ana dukar daji da kafafu. Ban daki wurin wanka da bahaya daya ko biyu ansan tashin wace ansan sunyi sunna da mijinta mai kishiya akwai yan tayata gani suna saka mata ido a kishiyanta su zasu fada mata sunga tayi wankan tsarki ko sunga mijin yayi wankan asuba. Duk damu da baba ya dan kebewa inna wuri bata tsira da hakan ba don sai kiga mace ta fado mata wai a san mata waje ta kewaya don gulma har yara suke turawa yin wanan laccan ga junansu. Saidai ni dana dan tasa a cikinsu Allah ya kareni ga hakan don iyayyena basu yarda insha cikinsu ballema a koya min wanan akidan na babban gida babban bala,i. Don da zaran aka fahinci mijinki yayi wankan tsarki baiyi a dakin kishiyarki ba aiki ya samu a gidan yanzu zancen boka da malam zai tashi aje kuma a zageki tsakar gida sai kin tsargi kanki da kanki kan hakan. Idan kuma ke kadaine gun mijinki tofa nan ma ba,a barki ba za a sakaki gaba dasherin cewa kullun kina mane a kafadan namiji kin hanasa ya karo maki kishiya kin mallakesa kin hana wata tashigo itama taci arziki. Wanan jahar su inna ke nan su akewa irin shaguben nan don duk ranan da aka ganta da sabon kaya zakiji an fara dama hakan take so taci ita kadai daga ita sai yayanta bata son wata tazo aci tare. Saida baba ya tsaya tsakar gida ranan yai fada kan kewayawan da suke zuwa yi sashen mu sanan muka samu sauki saidai baiwai sun bar zuwan bane sukan faki idonshi s shigo su kewaya din don gulma. Kai gaskiya zaman babban gida a kauye ba karamin fitina bana yasa ko baki da baki idan kin shigo dole bakin zai bude sai kiga yar karamar yarinya tana ciwa tsohuwa mutunci a tsakar gida gaban yayanta da kowa. Nikan nayi barka naji dadi da Allah ya kadarta iyayyena suka taso dani don da karshensa a gidan aure zai kamani ace anyi auren hadi tsakanina da wani can a dangi. ZAINB IDRIS MAKAWA [1/16, 12:13] Aishatu Aliyu Musa : DUBA MIN BAYA FOKON BIRI ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Yau weekend ne muna gida bamu fita school misalin shadayan rana ina kwance daki naji shigowan baki gidan hakan baisa na fito ba don naji muryan mazane ba mata ba. Can naji muryan baba yana kwala min kira cikin daga murya na fito da sauri ina fadin baba gani yana zaune sun zagayeshi saman tabarman da suke zaune akai. Yace kinci gidan ku bakiga yayyunki bane baki bakizo kin gashesu ba na dago kai na kallesu sau daya saboda kwarjinsu ina fadin sannun ku da zuwa ina wunin ku suka dago suna fadin lafiya lokaci guda. Jeki ki kawo masu ruwa ya fada cikin bani umurni na mike ina tafiya cikin yanayina na yanga da tun ina fociciyata hakan nake tafiya wanda yanayin jikina yasa hakan sai wanda bai sani ba y a dauka yanga nakeyi. A fakaice wasun su suka bini da kallo ruwan leda na dauko na dire a gaban su kafin na mike da zumar barin wajen muryan babane ke fadin dakata kinji kinga wanan. Ina jin hakan na juyo na mayar da hankalina gun baba din dake magana dani naga ya nuna min na farko dake gefenshi yana fadin wanan dan babankine dake Kano zaune yanzune na wancan gidan na kusa da Dada din nan. Wanan kuma dan kanwar muce Jummai matar babanku Ahmed dake Abuja wanan kanninsa ne data haifa a gidan babanki Ahmed din. Baba na fadin hakan sai naga na farkon ya danyi kasa da kai ya lumshe ido a hankali kamar zancen bai masa dadi ba yadda baba ya fadi zancensa a gabana amma shima din mahaifinsa dan uwan mune saidai Allah ya karbi ransane tunda cikinshi. Saida yayi min bayanin su kaf dinsu kafin ya barni in tafi suna ta hiransu dashi wanda yawan hiran tambayane yafi yawa da baba ke masu. A lokacin na sulale daga gidan na faki idon su nafice zuwa gidan Dada don ganinsu a gidan mu yasa banda sukuni a lokacin duk na tsawala da ganin mutane a gidan namu kuma bakin fuska maza haka. Na samu Dada ita kadaice agidan hakan yasa na dan saki jiki na debe hijjab fura ta miko min a wani kwanon shan silver mai marfi na girgiza kai ina fadin a koshe nake Dada nagode. Tace ja,ira dama nasan ba zakici ba ai wanan mara yarda a bakuwa kike shigowa mutane ke a kullun kinki sakin jiki har yanzu da kowa kaf a dangi na dan turo baki ina fadin haba dai Dada akwai wanda nake sakin jiki dashi bayan ke kafin ta ban amsa na mike shara nayi mata na gyara dankin har tsakar gida kafin na dawo na zauna a kusa da ita muna hiran harira jikanta dake zama da ita datayi tafiya zuwa kaduna. Anan mukaji sallaman su sunshigo gidan Dada din gaba dayansu yadda na barsu zaune a gidan mu din haka suka jero su hudu suka shigo gidan. Farinciki naga a fuskan Dada din kafin ta fara tafawa tana fadin lale marhabin da bakin turai kune a tafe haka da rana tsaka ashe da rabon zamu gana daku kuma. Koda yamma muka iso badai kin ganmu ba ina ruwanki da time din shigowan mu sai naga ta kwashe da dariya bakinta da goro ya bata mata hakora ya baiyana a fili. Cikin dariyan take fadin ja,iri har yanzu dai kana nan a yadda kake ashe kai kam turai din baisa ka canza halin naka ba dama ance kada ka kara a yadda kasan halin mutum a baya. Zama yayi a gabanta ya dora hannayesa bisa cinyarta yana dan murza gwiwanta din daya dora hannunsa a akai ta tureshi tana fadin ja,iri kaga kada ka karasa tsohuwar mutane don Allah. Ka zama wani jibgege da kai kamar wani zaki nikan ma wanan karatun yayo a can ko zamancin abinci tana fada tana kallon yan uwansa da alaman tambaya a garesu. Dariya ya kwashe dashi yana fadin nifa Dada nazaci kin mutu tuni don ko dan tsaraban goro ban riko da sunanki bani don na dauka ko kin bi mijin naki ashe kina nan gyagyau din ki baki tsufa ba. Wani harara ta galla masa tana fadin da yake ni ba uwarka bace ai dole ka fadi hakan dadin abin dai akwai wanda suke son su ganni a cikinku koba haka ba ta kalli na gefenshi din sai ya murmusa yana dukar da kai. Dariya ya fashe dashi yana fadin tsiyata da tsohuwar nan bata son mutuwa ko kusa yanzu da jin zancen mutuwa duk kinbi kin rude kina batun sakawa mutane kuka. Allah sarki kaine dai baka sonta nikan ai yanzu a kullum zaman jiran nakeyi da fatan cikawa da imani a zuciyata . A,afa Dada kada ki ganta a yanzu ki dinga kwala muna ihu kina fadin azo a taimakeki nan sauran suka kwashe da dariya Dada dai ta mike tana fadin ja,iri halin dai yana nan ashe bari na kawo maku farau farau ku jika makoshi kafin mu gaisa . A,a Dada kibar wanan farau faraun naki kada kisa cikin mu tsatsa ni dai kan bazan sha wanan abin naki ba don haka dawo ki zauna muyi fira kawai na yaushe rabo. Tsayawa iyan tayi tana kama baki kafin tace Ja,iri bakai kadai bane ai idan bakasha ba wani zaisha ai a cikinku ya kallo yan uwan nasa yana fadin to ku kunji da mai son shan tsatsan kwanonta a yanzu cikin ku? Wanan kan kam anyi ja,irin yaro a nan ga yayyunka basuyi magana ba sai kaine da bakin iyawarka kake zuba haka ya dan dago ya kamo hannunta yana fadin Dada nifa naga kin koma min wata yar caras hakan nan ko kin fara zance da zawarawa suka kawo maki namane kika koma hakan wai. Haba ta kama tana sallati kafin tace kaji min dan kawai ko to ubanka Amadi daya dawo garin nan ina kun sani dan albarka shine kullun ake dafo min nama a gidansa ana
Chapter 4 · 0% Book details