Sashe 16
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
don kuntatawa kawai. A,a,a gaskiya ba,a kyauta ba kan na kallo halima din kafin ta zake nace hjy mum don Allah kiyi hakkuri Allah yasa rashin zuwansu shine alheri su kuma da sukazo Allah ya tsare ya kare ya mayar dasu lafiya tace Amin zainab naji dadin wanan maganan taki sosai wallahi kuma naji zuciyana tayi min sanyi sosai da wanan kalamin naki yanzu. Nace wani lokaci ai mummy zamuga abu muna sonshi amma kuma hakan ba alheri bane tace kwarai tana nisawa zakice wata sa,armuce a lokacin tayi shiru bata kara magana ba har muka shiga gidan nasu tayi packing a inda ta dauki motar da safe. Muka fito zuwa ciki dauke da wasu kaya data miko muna da zamu fito motan nan muka shige ciki wani kamshin dadi part din nata yakeyi kuma yana bude don haka nidake gaba na shigo da sallamata falon. Ciki ciki ya amsa muna yana kwance saman doguwan kujeran falon jikinshi saye da farar jallabiya ta maza mai dogon hannu kafansa farare sun dan baiya ga gashin jikin nan nasa sun kwanta masa lub a kafafun nasa. Ya dan dago yana amsa sallaman tare da fadin mai shiyan bata nan fa saiga hjy mum din ta shigo daga bayan mu tana fadin ki kai min wanan daki halimatu wanan kuma zainab ki aje nan in huta in bude mugani. Mamakine ya kasheni lokaci guda ina kokarin tuno fuskansa in ba karya zanyi ba sune bakin da sukazo katsina wani lokaci har baba yai min bayanin su din nan. Tabbas ma sune shi din ne dai dama dan hjy mum ke nan ake nufi kome ko kuma nan din ma yazone dai kamar yadda yazo muna latsina wani lokaci can lokacin bamu kai hakan ba girma. Halimatu nikan wani suna kika kira dazunne ma ga yayan naku ina sulaiman din ta fada tana kallonshi yace cikin dan dagowa ya fita bansan inda yaje ba sai lokacin nace sannu da zuwa ya dan kalloni. Da sauri nakai kasa ina fadin ina wuni anzo lafiya ya amsa cikin dan kura min ido kafin yace yar gidan baba garba ko ? Itace ashe ka santa ya koma ya kwanta yana fadin wancan zuwan da mukayi katsina na santa kinsan lokacin sun dawo suna katsina tace ehh ai yanzu kam ya dawo gida ke nan . Halima ta fito ta gaidashi itama kafin ta fice da sauri zuwa wajen Dada din dakin mu na shiga nayi sallah ban idar ba nake jin hjy mum din tana kwala min kira ni kuma ina sallah. Saida na idar nazo na sameta ina fadin hjy sallah nakeyi kada lokaci ya shige azahar kawai nasamu nayi a can din dama zance ne ki debowa yayanku abinci ai na debo masa. Na dan rakube ina fadin ayya sallah nakeyi bari naje gun Dada mu gaisa don zuwa yanzu hankalina ya fara komawa gida kan don ban taba tafiya nayi nisa da iyayyena da yan uwana ba sai wanan karon. Da nazo gashi satin mu biyu muka rufe har mun zama yan gida a kano yanzu ko baba na kano ya dawo daga kasuwa baiji duriyan mu ba sai ya tambaya inasu mamana banjisu ba. Wani lokacin idan hjy mun ne kusa dashi zata fada mai abinda muke inko hjy mah ce zata dan basar da tambayan nasa sai yasa murya ya kira wani daga cikin yayansa akiramu. Gashi da halin arziki sai ince sukan haka zariyansu yake da alheri da kuma kula da iyalansu don duk dare baba na kano zai dawo da dan tsarababsa da za,a raba ako wani sashe nagidan. Irinsu yought kilishi limu kaza da gadaden nama mai zafi tare da abin sha kuma sai kowa ya samu a gidan yaci bawai sai wanda yai ra,ayin bawaba kawai zai samu. Tun shigana part din mukaci karo da wanan uwar feleken yar wurin hjy mai nuna kamar tana jin warin mutane idan aka hadu da ita din nan. Nunani tayi da hannu tana fadin wai kece dama ban ganeki ba haka na dauka irin yan classic din nan ne ma a ina kukayi wanan gyaran hakane naga dayan ma yau ta canza sosai. Ban iya bata amsa ba ina kokarin shigewa ga rainin wayau a na magana kina kokarin shige mutum ko ance kada ku fada munane kuma ? Dan murmushin yake nayi mata ina fadin nikan ban dauka dani kike ba ai ku bansan wajen ba wallahi tunda ba garin na sani ba ni andai kaimu an muna hakan na shige dakin da Dada din take. Halima na zaune tana cin abinci nace ke kuma ina can ina jiran kizo muci abinci har na idar da sallah banji ki ashe kina nan kinaci ke ban sani ba Dada tace kyale ja,ira ai na fada mata abincin ku yana can wurin uwarku dama. ZAINAB IDRIS MAKAWA [1/25, 15:44] Aishatu Aliyu Musa : DUBA MIN BAYA FOKON ,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Alhamdullahi yan buki sun fara taruwa a gidan don iyalan baba na bauchi sun iso da na baba na zaria dake aiki a ABU zaria suma sun shigo don haka mun kara yawa a gidan. Yinin yau aiki mukaci sosai a part din hjy mum don hakane ban samu fita inga bakin da suka iso din ba don suyan nama muka wuniyi ko ince na wuniyiwa mum din a kitchen dinta. Wanda lokaci lokaci halimatu kan dan zagayo ta dan tayani kuma ta gudu don bata iya tsayawa ta soyashi kamar yadda nina tsaya nayi mata. Itama mai aikin takan zagayo mu danyi tare kafin kuma ta kama wani tsabga sai wani lokaci ta lekoni don haka a wajen halimatu dake dan zagayowa nake jin komai. Dakyat na samu nagama mun cika wani roba babba mai marfi nayi mata suyan yadda ba zai lalace mata ba wanan yasa na dade ina wahala wajen suyan yaji gishiri da maggi danake dan mirginashi kafin na soya don masuci hakana din. Dakinta nakai roban can kurya na boye wanka nayi na dauro alwala don duk jikina ciwo yake min alaman yayi tsami a lokacin yasa na dan watsa ruwa na dauro alwala don in gabatar da sallolin dake kaina lokacin. Bayan na idar ina wajen zaune lok cin nake jin wata irin iska mai sanyi yana shiga jikina hakan yasa na mike na dauko mai nashafa don kada zazzabi ya kamani a lokacin. Wani dogon rigan da anty Nafisa ta ban na saka a jikina rigan tayi min dagwas a jikina har ina mamakin yadda za,ace wanan kayan suyi mata ita tunda ta darani kiba da cika na yan mata sai kumani ga rigan yayi min daidai a jikina dana saka. Duk da ina son hutu a lokacin amma hakana daure na nufi dayan part din wurin Dada da niyar inje can in kwanta sai kuma na samu dakin nasu da mutane. Sallama nayi na shiga suka zubo min ido gaidasu nayi kafin suna amsawa na raba zuwa wajen Dada na zaune na manne a jikinta ta kalloni tace. Ban sanki da raki ba badai wanan aikin da kikayi bane ya saukar maki da gajiya ko nace a,a Dada amma kamar zazzabi zazzabine ke son kamani yayin dana manna hannuna a gefen wuyana ina tabawa a hankali don naji zafib jikin nawa. Wanan kallon banzan nasa ya watso min daga inda yake kwance saman carpet ya dan kishingide bashi ba dukkansu kallona sukayi lokaci guda. Aiga likita kusa ki fadi abindake damun ki ya baki magani koya rubuta maki a in ma allurane duk yanzu sai a sayo ayi maki karamin ya fada yana kallon mu. A takace nace lafiyata ai kalau kila gajiyace daice a kaina yasa nake jin hakan sai naga duk sunyi murmushi shi din dai ke fadin ashe kina da wayau yau da yarinya kinsha ihu din hannunsa akwai zafi sosai ya dan murmusa yace yaushe rabon da in maka allura kai ? Wai wanan mugun kake zance dama ina zan bari ya makure yar mutane ya halaka masu ya yaje can dai ya samu wa yanda basu san ciwon kansu ba yayi ta zurnuka masu idan sun yarda. Baiyi magana ba sai mikewa da yayi tsaye yana fadin kai Auwal kama min tsohuwar nan in mata allura ko bakin nan nata zai mutu jekaiwa ubanka musa dake kasuwa ko kaje kaiwa Audu ko garba kafin kazo kai mun. Au har da zagi yau zaki fada kuwa don nayi niya babu mai hana in maki allura a gidan in ka isa ai gani gaka. Gadan gadan yako harota saiga allura ya fito dashi daga jikinshi yace yau zamuga karshen cika baki don gaba daya saina dura maki wanan alluran a jikinki. Ganin yadda ya nufota din yasa Dada ta dauka dagaske yakeyi tace yau zanga inda za a binne tsohuwa da ranta kuwa ya cakunata ya rike ta fara sallati tana kai mai duka tako ina tana zagi. Tunda suka fara abin bai dago kai ya kallo inda suke ba sai kallon wayanshi da yakeyi jin hayaniyan yayi yawa ya dago yana fadin kai rabu da ita mana. Wanan ai haukane idan kajin mata ciwofa ya zakayi hakan baisa ya sake ta ba bansan lokacin danace haba don Allah kada ka halaka muna ita mana. Cak ya tsaya yana juyowa ya kalloni zanin Dada dake kokarin kwancewa a gabansu nayi saurin rikewa don nasan a rude take itako Dada sai dura mai ashar da takeyi ta uwa ta uba tana kira masa rashin tarbiya. Ke ina wasa dakene ko rashin kunyan ku na yan kauye zaki kawo min a nan yanzu zan tatakaki wajen nan idan kika kara budan bakin nan naki mai wari a nan. Badai bakina ba na fada ina kawar da