← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 61

Sashe 53

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wallahi in kira ta in fada mata zuwansu din nan mum ta labarta masu abunda ya faru tsakanin mu. Anty nafisa tace sai tayiwa mummy din magana hakan nan dai sukace ta barta dama sai an samu haka ai tsakanin mu kafin a shirya take fadin don me mummy zataje gidan yarinya suci mata mutunci. Toke Nafisa aiyin maganan naki zai kara rura wutan abin tsakaninsu kawai dai kije kikaga mama din ki bata magana in ma wani abune dole ta kyale akan cewa zatayiwa mummy din magana da tayi niyar yi da farko. Ita ko mummy hafiz din ta kira inda take shiga ba nan take fita ba ta kwashi karya da gaskiya ta fada mashi ya hau yana batsewa yana fadin i can't mummy ba zan iya zama da wanan yarinyar ba gaskiya. Kece wai har yarinyar nan zatayiwa wullakanci tace ba dole tayi min ba tunda tana ganin Alh ya daure mata gindi zama da kai dolene ko bamu so ai dole tai muna haka taga gidan mike kafa a dole. Wani shu,umin murmushi yayi kafin yace a ina fa mummy kawai ta bari inzo in sameta gida zata raina kanta wallahi mutane kamar mayu duk wanan bai isheta ba sai ta gwadawa mutane ita yar dajine ko zanzo zanyi maganin yar iska ai. Hutun mu har ya kare na sati uku don hakane ranan na bugawa daddy waya ina sheda mashi ya danyi shiru kafin yace dani to uwata ba zan tauyeki ba a gida in hanaki zuwa abinda zai fisheki ki shirya kawai ki koma school din ki kici gaba da karatun ki tunda shi haka yaga yafi mai. ZAINAB IDRIS MAKAWA [3/2, 21:07] Aishatu Aliyu Musa : [3/1, 07:51] +234 706 511 1949: DUBA MIN BAYA FOKON,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Zaune take a falon tana katatun littafin da take kai a Islamiyansu yayi sallama ya shigo falon nata ta dago daga karatun tana amsa mashi. Kallo daya tayi mai ta fahinci akwai matsala koda bai fadi ba tasan akwai matsala a wani bangare hakan yasa ta rufe littafin da take duba din ta fuskanceshi. Zaune yakai har tsawon wani dan lokaci kafin ya dago yace zancen hafiz ne dai yake damuna don ban fahinci me yake nufi da yar mutanen dake gidanshi zaune ba da muka tauye. Dazun ina shago ta bugo min tana fada min cewa hutunsu ya kare tana son ta koma karatun ta watau hakan ke nan yana nufin bai waya da ita tun tafiyansa ? Dan murmushi mum ta sake a fuskanta kafin tace ai kaima ka sani Alh ban tsamanin cewa hafiz nada number mama a wayarshi. Kuma hafiz bai yarda ya karbi auren mama ba kamar yadda kake zaton ka shawo kansa daga baya har ya yarda ya amince nina sani saidai sanin baida amfani a gareni . Tunda banda power din da zan dauki mataki alokacin da nasan haka din wayar yarinyar nan samira dake hannun mama din a cikinsa mukaga irin yankar kaunar da yai mata ranan da kuka kaita kuka fita. Mikewa ta tashi tayi ta dauko wayanta data tura ta kunna mashi yayi shiru yana sauraren rashin mutuncin da yake shuka min a lokacin har lokacin da aka fara nocking kofa ya fita da dan hiran mu dasu Anty da suka shigo take fadin har yanzu kukan rabuwa da mum nakeyi ne ? Nisawa daddy yayi kafin ya dago kai ya kallo mum da idanuwansa da sukai ja jajir dasu yace lalai yaron nan yakai dan banza yana ganin banda sauran amfani a garesa yanzu ko ? Tunda nagama masa wahala ya girma yana ganin yanzu kafansa shi sun kama kasa sakaiyan da zai mun ke nan kafin ta kiraka ni ta fara kira ai mum ta katse mashi magana don luran da tayi ya fara fita hankalinshi lokacin. Cikin hikima ta fara canza zancen da fadin tana kirana ta fada min wai tana jin tsoron fadama shine nace dole saika sani ai wanan yasa ta kiraka. Alhamdullahi ai tunda ita yarinyar bata bijire muna ba har yanzu tasan a karkashin iyayye take tana kuma biyayya ka kyaleshi kawai shida kansa zaizo ya gane cewa yayi kuskure abinda yakeyi a yanzu. Yin shirun ka shi zaidaga masu hankali zasu shiga tashin hankali don basu san me shirun ka yake nufi dasu ba amma idan kai magana abinda suke nema ke nan dama rayuka sukai ga baci a yanzu ka kyalesu kawai ka saka masu ido zaifi. Illa iyaka ita mama mu saka ido akan al,amuranta a bata kula yadda ya dace ta yadda damuwan hakan bazai dameta ba ni shawarana ke nan . Ya shafo kai yana fadin neman maganane nina sani kuma da hadin bakin uwarsa yake hakan duk abinda hafiz keyi malka tana da labari don hakan shawaran ki ya kawo min mafita a cikin zancen nan yanzu ya mike ya fito daga dakin nata . Ranan monday da safe bayan na shirya naji horn direban dake kaimu school ne yazo daukata shiya kaini makaranta a ranan da aka tashi kuma yazo ya daukeni . Anty nafisa bata san da cewa nashigo ba don bamu hadu ba ban kuma nemeta ba don banba office dinta ba har na dawo gida don a yanzu ko waya bamayi da ita tunda aka kawoni gidan dan uwanta halakar mu ya danyi rauni tsakanin mu. Bansan dalilin hakan ba amma tun lokacin buki ta fito da wasu abubuwa gareni mum tace a shareta kawai nikan badon mum ba gaskiya da bansan ya rayuwana zai kasance ba a cikinsu. Hankalina kwance nake karatuna ban sakawa zuciyana komai ba inci mai kyau insha maikyau ba abinda ya dameni saboda kurciya har mantawa nake da nayi aure a lokacin don wauta. Sai wata ranane malam isah ya daukoni zamu dawo gida muka hade da ita a daidai get tabi motan da kallo don sanin motar gidansuce wanan . Sai lokacin ta ganni ciki zaune a baya malam Isah yana jana zai mayar dani gida mamakine ya rufeta a lokacin tabimu da kallo har muka bace mata. Malam isah din ke fadin ga hjy Nafisa can ko mu tsaya ne nace a,a mu wuce kawai illa iyaka ya danyi mata horn ta mayar masa itama muka tafi. Mamaki tayi sosai har takai inda zata kafin ta dauki waya ta kira mummy tana tambaya dama ashe yarinyat nan tana zuwa makarantane mummy yanzu naga malam isah ya daukota zai mayar da ita gida. Wace yarinya ke nan mummy ta sake tambayanta tace Zeey mana ta nan gidan matar hafiz ta fada kai tsaye sai uwar tace kika ganta ina tace school mana mummy na dauka aitamooiu n dainane yanzu don auren nan. Kima daina zancen nan don Allah bari nakira hafiz din inji sai yar ta katseta da fadin to meye mummy idan taje school tunda dama tana karatunta ba sai a barta tayi ta zuwa ba. Wai meyasa ke baki gane abinda ake nufine baby wanan fa anyi hakanne da wani manufa sai yanzu nake gane nufin dan iskan yaron nan me dadin bakin tsiya da har ya bada shawara kan taje karatu zaifi. Watau ita tayi karatu su mairo ko suna gida zaune wai suna aure ba damuwansu bane su kinga abinda nake sha fada maki ke nan baby amma kin kasa fahintana dake ke nan suke son jayayya a gidan nan tunda hjy kubrah bata da diya mace sai wanan yarinyar. Haba mummy ni kuma Zainab fa har yaushe zainab zata iya kaini balle su tsaya kwatantawa dani don Allah sai dai idan suna da wata manufa dai ta daban akan karatun nata dai. Shiko hafiz din data kirashi bai dauki waya a lokacin ba sai data masa da dare ya dauki wayan suka gaisa ta fara fadin kai ka umurci yarinyar nan da tafita zuwa school ? Wace yarinya ke nan mum ya tambaya tace matarka mana zeey dazun baby ke fada min ta ganta malam isah driver ya daukota daga makaranta. Mummy akan zancen yarinyar nan kika kirani don Allah kibar kirana kanta mummy don banson ai min zancen wanan yar iska don nabarwa daddy ita shida ya matsa sai anyi auren nan to anyi din ban bashi kunya ba sai su zauna da ita din mugani. Wai dama har yanzu tana gidan a matsayinane kota koma gida tace kai hafiz ka natsu ka saurareni kaji me zan fada maka akanta. Don na rarasheka ka yarda ka aureta hakan ba yana nufin ka fita zancenta yadda kayi din nan gaba daya bane don akan zancen nan na tabbatar da Alh zai iya saba muna gaba dayan mu daku. Koma yayane akala ka dan kula da ita a matsayin matarka kana dan zuwa baka share haka ba har ana neman kwasan wata baka leko ba me hakan da kayi yake nufi ke nan ? Gaskiya mummy i can't ban taba jin wani feeling akan yarinyar nan ba kwata kwata wallahi mum banko son in ganta a rayuwana wallahi kai kadakata da wanan shirmen ka saurareni kaji me zan fada ma. Nan dai ta koma lurar dashi abinda ya dace yayi har ya fahinceta don a yanzu ta fahinci Daddy ya juya mata baya itama duk da bata san dalilin hakan ba saidai ta fahinci akan zancen dan natane da yake ganin bakinsu daya ya kawo sauyin nan tsakaninsu. Don yanzu iyakan daddy da ita ina kwana ya amsa mata a daure ko kuma inta kawo abinci daga part dinta zai zauna ya danci wani lokacin wani lokacin kuma ko kallon abincin baiyi zai barshi a wajen. Bata saba da irin wanan rayuwan ba sai abin yazamo mata sabon ak,amari don hakane tayi shawaran cewa dole sai tasa dan nata ya natsu
Chapter 53 · 0% Book details