Sashe 41
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ehh nashige na dan dade ban fito ba don na tsaya dan gyara a dakin kodana fito falo na fito don indan samu abinda naci alokacin. Yana zaune tare da mahaifiyar nasa da alama wani zance sukeyi hakan yasa ban tsaya ba na shige kitchen acan tsaye na tsaya naci abinci na kusa karasawane naji muryan mum tana kirana na amsa. Koda nafito ban sameshi ba a falon ashe suna wanan ita kuma Aisha matarsa nata kwala masa kira akan yazo ya dauketa mana baiga dare yayi bane da farko ya fada mata yana wajen mum ne ai. Bata daddaraba ta dameshi da kira karshe ma fada da masifa ta kamayi masa duk mum najinsu tace ta tashi yaje itama bata da lokacinsa dole ya tashi yaje ya sameta a inda take shine mum ta kirani na kwashe kayan dayaci abincin a falo. Sai washegari da yamma mum din ke fadin kinga yaronga ko don kada in masa zance akan matarshi son nace ya tabbatar daya daukota sunzo sun gaida Alh da hjy cewa Dada. Shine shima ya tafi ba tare dayazo yai muna sallama ba yaje ko bace ba gashi gata suje suyi tayi dama abinda kowa ke masa gudu ke nan da auren wa yan nan marasa tarbiyan da boko ya ratsa gidansu ke nan. Yanzu haka itace ta hanasa zuwa ko aikema kin sani tunda bai taba tafiya baizo munyi sallama ba ko yayako yake sauri sai yazo gidan nan watara zuwa zuwa ma saisu shigo garin bamu sani ba harsu gama abinda sukeyi basu zo gidan nan ba ke nan. Kai haba mum bari mashi wanan fatan aishi ba zai yarda haka ya faru ba akansa tunda yasan hakkin iyayye yaushe kuma tunda har nace ga abinda zasuyi taki zuwa kuma ta hanashi shima. Wai dako ta zama sakarai wallahi tunda wata rana itama uwace don haihuwa zatayi ai haka dan zai mata kuwa na fada a hasale raina yana baci da zancen ina maijin haushim yaya din. Ta yaya mai hankalibda hangen nesa kamarshi zai tsaya mace ta juyashi kamar sakarai wanan tunanen nakeyi a raina sunana da mum ta ambata yasa na kallota. Tace jinyan da suwaye a wurin hjy suke zancensu nace matan daddy Enugune tace ai sai kowa yaji wanan zancen da hjy ce zance zata kyale sai ranan da suka hadu zatacisu taran hakan amma wa yan nan sushiga mitan hakan ke nan sai kowa yaji agidan nan. Allah sarki komin fushin uwa da danta bata son yau ace ga laifin danta a waje tausayi hjy mum taban don nasan tana iya kokarinta akan tarbiya. Amma yau sai gashi mace tana son shiga tsakaninta da danta ta hadasu fada a tsakaninsu saboda son kai banta ganin uwar data shaku kwarai da diyanta ba har suka zamo abokan shawaranta irin mum ba. A take naji tsanar wanan macen ya fita raina dako ina son ta dongayunta ina ji da ita har ina son koyi da irin halinta ashe kyau dan macijine da ita. Duk macen dake kokarin raba tsakanin da mahaifiyar shi da sunan aure wanan mace ba karamar shedaniya bace son kanta yana da yawa bata kuma kaunar mijin da take aure din. Kabari a cutama yafi kayi cuta irin wanan mai girma a duniya basu ganewa matan saboda son kai ya rufewa wasu ido har suke jin hakan aiba zunubi suke aikatawa ba. Ranan dai gajeren hira mukayi da mum da safen son ko bayan mun gama karyawa ta shige daki bata sake fitowa ba ni kadai nayi ta zirga zirgana har na hada muna abinci nagama. Mum bata kyale ya Addil din ba donko ta kirasa a waya tayi masa kaca kaca ashe matar na kusa a lokacin nan ta fara yan surutai tana fadin dama aiba sonta akeyi dashi ba. Idan hakane ita gara kowa ya kama gabansa zaifi a tsakaninsu shigo yaji surukulen mata nan ya shiga bata hakkuri yana ban baki kan tabari zai zauna da mum din suyi magana ai bata fahinceta bane. Ni dai a yanzu nikan ga mum ta aikeni wani gida da bamu da nisa a layin mu gidan marayune maigidan ya rasu ance yakai shekara kusan ashirin ga gidan babba amma iyalansa ke ciki zaune. To wanan gidan dama nakan dan kai masu sako saidai na yanzu din yayi yawa don yakai harda abinci dafafe idan zamu dafa mukan kara yawa sai tasa i kwashe daban in dauka inkai masu don irin gidajen su Dad manyan gidaje a layin almajirai basu shiga haka kasafai don suna tsoron yankan kai. Yauma su zan kaiwa sako data ban shake a ledan vaco har da tufafi dasu sabulu omo man shafi da makaroni da taliya niki niki na dauko kayan zan fito daga cikin gida da katon hijabi na don sai ka kula zaka gane ai duka hannuna biyu dauke suke da kaya. Anty Nafisace tsaye da wani namiji shi ya bada baya don haka ban gane fuskan ko waye ba a lokacin kai sister me kika dauko haka kike haki kamar zaki fadi ? Mum ce ta aikeni wancan gidan na fada sai lokacin ya juyo nagane ya Hafiz dinsune a wajen ashe nina zatama tayi bazawarine yazo mata hira yadda suke dashi don zaune take cikin motanta shi kuma yana tsaye ya riko kofan motan suna magana. Wai amma kayan nan sun maki yawa ta kara fada na danyi dariyan yake sai naji yace da ita maganinta ke nan ai jakace dama abinda ya dace da ita ke nan daukan kaya. Innalillahi na furta ina runtse ido kamar na dawo in bashi amsa sai kuma na wuce kawai kai tsaye a zuciyana nace na barka ga Allah shi zai aiko mai rama min dan giyan banza kawai . Haka na fita ina fada cikin zuciyana har Allah ya taimakeni nakai gidan ga gidan da shegen girma kafin ka kai cikima aikine a yadda naji wai bayan rasuwan mijinta anso a cinye masu komai daya bar masu. Sai matar bata yarda ba mafarin da batayi aure ba ke nan tana ciki zaune da yayanta su kuma yan uwan mijin sunce basu yarda tayi aure wani miji yashigo gidan dan uwansu ba yaciwa yayansu gado. Rikici dai akace anyi sosai shine ta zabi zama da yaranta a gidan akan taje tayi aure kuma taki yarda da tayinsu na son su aureta da sukayi shine suke cikin wanan bakar wahalan ita da yaran kuma sun hana tasa ko dan haya a gidan ta samu inda abinci zai fito mata mugunta zalla a wajen sukai mata. Tayi murna kwarai tace tana nan zuwa tayiwa mum din godiya da yamma in yara sun dawo daga school kodana dawo ban samu su anty Nafisa din ba motar tama bainan nasan ta fitane lokacin. A part din mu na samu Amir tare da mum zaune kin dawo mama mum ta fada na zaune ina wash amir yazo ya haye min jiki na daukeshi ina masa wasa tare da fadin waya kawoka nan ? Nima gannisa nayi ya fado min yanzu yasan hanya tunda ya samu kafa basai an kawoshi ba ai lokacin nace mum ni bansan abinda nayiwa ya hafiz ba ya tsanani ? Hafiz kuma yazone yana gari ta tambaya a cikin mamaki nace yana nan tare na gansu da Anty Nafisa a kofan gida zan fita son anty Nafisa tace min kayan dana dauko sun min yawa shine yace dani aini jakace dama shine daidai dani. Hummm ki kyaleshi baida hankali inbashi ba ka kira dan uwanka musulmi da jaki kaji dadi akan me don Allah ki barshi karkima kulashi don Allah. Shima mashayi dangiya ai gara da jaki haka Allah ya haliceshi da daukan kaya kar in karaji babu ruwanki inma da gaskiya yana sha tsakaninsa da Allahne wanan babu ruwanki mum ta hanani cigaba da magana alokacin. Shiru tayi tana tunane kafin nace mum matar nan taji dadi sosai wallahi tace ke mai kyautan yan aljanna ce dan kyautanki nazuwa a lokacin da mutum yake cikin matsanacin hali sai mum di n tayi murmushi tana fadin Allah yasa mu dace ga baki dayan mu na amsa da Amin. Bayan kona biyu muna zaune abin mamaki wai saiga ya Hafiz ya shigo part din mu da takardu a hannunshi yake gaida mum kafin ya juyo guna yace ke karbi takardun ki yace in fada maki ranan Monday zakije screening. Yana fadin hakan na mika hannu na karba da sauri ina murna kafin nace nagode na mikawa mum tace takardan kine ai na karatu tun jiya yayaki ya bugo min cewa zai aiko dashi. Sai kibi Nafisa taje dake tai maki komai a can yafada yana karasa mike zai tafi nan mum ke fadin ashe kuma fita zaka sakeyi yace eh wallahi mum can din yafine don su aiki baida wahala acan din. To Allah ya kyauta yasa aje cikin nasara ya amsa da amin yafita hankalina yana kan takardun dake hannuna ina karantawa banko kula da fitansa ba. Na daiji mum na fadin hjy malka bata da tunane yaron nan zata kara turawa kasan waje kuma shi kadai ya zaunacan suna tare da yan uwama bai natsu ba balle yaje shi kadai da sunan aiki. Sam ban tsaya kula mum din ba a lokacin don bayanan dake cikin takardan ya dauke min hankalina Allah ya gani ina son karatu sosai a rayuwata. Na dago ina fadin mum sai nayi wani photo kuma barima in duba ko nawa suka rage min a daki na mike na barta a wajen zaune. Har naje na dauko ban tsaya kallon mum dun ba da gaba daya yanayinta ya sauya lokaci guda ta shiga yanayin tunane mai zurfi dagowan da nayi ina fadin ashe ina da guda biyarma aje. Nan na fahinci sauyin fuskan mum din saidai ban fahinci kona meye ba wanda ba komai take tunane ba a lokacin sai yadda abubuwa zasuzo su kashe tasan dole a samu sabani don rayuka da dama zasu baci a tsakani. Saidai yanzu bata da iko ko power magana koda ko ace itace ta haifeni bata da hurumin ketara zancen mijinta ta tsaya musu dashi duk da ko yanzu din banda bambanci da diyar data haifa. Hakan da za,aimin tauyewane a gareni mai