Sashe 26
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dani haba dai sis ke kuma da nake jin dadin kasancewa dake kin dora da kuka ya kike son inyi ni kuma yanzu ? Jin hakan yasa na dan tsagaita ina hadiyan zuciya tace min a sake alaman ta dan fara saukowa lokacin tace kina jina sis nace gyada mata kai don ban iya bude baki a lokacin. Tace can you trust me as i can trust you nan ma da sauri na sake daga mata kai alaman ehh ba tare da nadago kai mun hada ido da ita ba lokacin. Good sis dake kadai na yarda kaf gidan nan kuma kalaman ki gareni da kike tunatar dani komawa ga Allah yasa nake jin dan sauki a zuciyana tun jiya ba wanda ya bani magana mai dadi irinki gidan nan gashi yanzu kuma kinzo kin kara min wani haske. Tabbas Habbib ya cuceni ba karami ba koda yake laifinane don sonsa ya makatar dani a lokacin har na kasa gane illan abinda yake yawan fada min din sai yanzu nake tuno komai. Don gaskiya yasha fadain hakan don yaji dadin rayuwansa dani yasa yake ya aureni yasha fada min hakan amma sai ban daukeshi komai ba idan ya fada min wannan lokacin. Na yarda dake sister dari bisa dari donke din tayuwanki na dabane kin samu tarbiya daya dace ace mun samu tundaga tasowan amma mummy ta kasa gane abinda daddy ke nufi sai son ranmu take bi. Don da ace tayi tsa AQye ta hanani auren habib da wanan abin duk bai faru dani ba yanzu akwai wullakanci kamar wanan cikin yau in haifeshi sister ba tare da ubansa ba duk akwai wullakancin daya kai wanan. Anty kiyi hakkuri hakan na cikin jerabawa daga ubangiji ki daukeshi hakan don Allah ki dinga istigifar da haila sai kiji sanyi a zuciyan ki haka malama mu na islamiya suke fada muna sai tayi murmushi donjin abinda na fada din gareta. Mummy ne ta fado dakin ta bimu da kallo gani ina sharan hawaye tace ita kuma wanan me take nema a nan anty Nafisa tace wurina tazo mana mummy tunda kin ganta tare ta wani daure fuska na mike ina fadin anty zanje in karasa aiki tace ki dawo fa sis nace insha Allah. Ina mikewa naji mummy na fadin ta dawo tayi maki me kuma kidai baku da zuciya wallahi ina ke ina wanan karamar yarinya kuma har kina jaddada mata wai ta dawo fa tayi maki uwar me a nan din. Kilama an aikota leken asirine kike wani cewa taje ta dawo to banson hakana kai mummy do lalacewa mai wanan zata zolayeni dashi kuma ? Ni natsuwan yarinyar nake jin dadinsa kuma haka Allah ya dora min kaunata a zuciyana don Allah ki barmu karkice zaki saka ido ga abinda mukeyi ni banson haka tunda ba yarinya nake ba yanzu dai. Na dai fada maki kiyi hankali da yarinyar nan don sani da kikai mata don yanzu an lalatata da makirci in kin kashi kikaganta zauna a ciki indai wanan yarce. Nikan ko wajen Dada ban tsaya ba part din mu na shiga a falo suke ya Addel yana karyawa a sake na gaidashi da ina kwana yaya duk da nasan ba lalai bane ya amsa min amma sai nayi sa,a ya amsa a lokacin. Ina kika tsaya kuma nace ina wajen anty Nafisace dama jiya tace in dawo ban samu zuwa ba sai yau ba koma sai naga mum tayi min wani kallo kafin muryan yaya ya katseta ga abinda tayi niyar fadi yace OK ta tashine jiya nashiga ance tana barci. Caraf nace barci kuwa andai fada ma hakane amma ita kan tana nan tana aikin kuka zancen mukeyi da ita saiga hjy ta shigo nafito ke mama ni dai kibi a hankali don Allah. Ban sanki da jaye jayen magana ba dai kinsan halin uwarsu dai yanzu ba sai na fada maki ba dai don haka ki kula don Allah. Yanzu mum harda yara za,a hana mu,amula da junansu kema kinsan halin Nafisa ai in bata yarda da ita ba aiko kusa gareta bataga wajen zuwa ba ai ki barsu kawai suyi abinsu ita wanan bata taba yarda da mutum dama idan ba jininta ba. Kaida bari in tsawata mata ko banza nasu baizo daya da mama ba nasan ko tunda tana wajena ta dauki tsana ta saka mata don ni itama ta iya badon iya ba ko ganinta batayi part dinta yanzu kuma ga Nafisa. Kai ya dago ya kalloni yana fadin kisan yadda zakibi dasu a zauna lafiya na amsa da to da sauri ina mamaki ashe yana magana mai tsayi irin haka. Saida ya gama ya mike zuwa wajenta sun dade suna magana a tsakanin su yana bata shawara a karshe take fadin wallahi daga kai sai zainab kuka ban shawara mai dadi a gidan nan. Yace wace zainab fa tace zainab din mum mana yarinyar nan dake zama da mum ina jin dadin kalamin yarinyar zakace wata babbace idan tana bawa mutum magana. Kai haba wanan meta sani banda shirme Allah yarinyar nada hankali sosai ta fada kafin mummy ta fado dakin kamar yadda tayi min haka shima tayi masa amma bai kulata ba don bai tashi ba cigaba sukayi da hiransu kan aiki ta gaji da zama ta mike ta fita wai tana amsa waya. Halin rayuwa irin na mummy sai a barta irin mutanen nan ne da basu da yarda ko kansu basu yarda dashi ba balle wani ga korafi da cin zarafi ga dan abu kadan idan ya hadaka da ita idon ta zai rufe ta yankewa mutum kauna nan take. Yanzu kan ko banje gun anty Nafisa ba ita zatazo har part din mu ta sameni ta zauna nan abu ga mai ciki tace wanan take so wancan takeso a kawo mata. Mum bata faye zama damu ba a irin wanan zaman don ta kula duk tazo sai an turo yan leken asiri azo aga me takeyi a part din zakiga kwana biyu ta dauke kafanta kwana biyu kuma ta dawo muna. Idan ta dauke kafanta nima nakan da jaye mata a lokacin sai kuma ta aiko a kirani ranan a gaban yan uwa take fadin kai zainab nifa wanan zaman naki ba waya ya fara isata haka . Ko mutum yana son kiyi masa abu sai ya aiko ko yazo gashini yanzu nayi nauyi tashima yana zama min wuya wani lokaci don haka ina da karamar waya zan baki ki rika yafi mun sauki hakan. Wani waya anty badai iPhone din nan naki nada ba Asiya ta tambaya cikin kashe yar nasu da idanu tace meye in shine ba nawa bane kuma zan bata. Ta mike da kyat ta dauko min wayan a dakinta tabani nan na kama murna da jin dadi taban kuma dubu biyu tace nasayi sim nasa da kati nayi ta mata godiya sosai. Washegarine muna zaune da Mum falo saiga hjy mummy kamar an jefo muna ita falon ina kusa da Mum na mane mata don dadin da uwata bata ban ba na tajani a jiki yanzu ina samu a wuri mum gaskiya. Lafiya mum ta tambaya a yadda ta ganta ta fado yace gun yarki nazo ina wayan da Nafisa ta baki jiya nace yana daki dauko ki kawo min ta fada a hasale tana gimtse fuska nace to a daidai lokacin da mum ke fadin jeki ki dauko mata. Kafin in dawo na samu suna cacan baki a tsakanin su mum na fadin kaiyya dadin abidai badai sata tayi ba bata akayi ke kuna jakkadiyan shedan kin hana yar ki alheri. Zance kike so ni dai waya nake son a bani ba wani abu ba kiji dadin zuwa kulla min sherin da kika saba to van fada ba waya nace ta miko min kawai ba wani abu ba. Ina mika mata ta fisge a hannuna kamar mai shirim kwata tafice tana fadin haka kawai ni ba a kawo min iskanci ai ke kuma kinci bashi don nasan nayi kike nema yanzu tana fadawa mum din tace tafican mara ta ido kawai. Ta dawo gareni tana fadin ke kuma kingani ai saida na fada maki kibi sannu da mutanen banzan nan kina ganin kamar ina son in rabaki da yan uwankine togashi kin gani da idanun ki. Har kuka sai da nayi don waya akwai shiga rai sosai dan kwana dayan da nayi da ita har na fara sabawa da wayan tun lokacin kuma zancen ya fice min a raina. Ban kuma nunawa anty Nafisa komai ba kan wayan zata sakani aiki in mata ta kuma shigo wajen mu nan wajen mum tayi yadda takeso ta tafi abinta. Bayan kamar sati biyu sai gata tunda safe su ya suna zaune suna karyawa ta shigo bayan sun gaisa take fadin ina zeey tana ciki mum ta fada ta nufi ciki sai gani muka juyo zuwa falon da ita. Nan take fadin wai ashe mommy tazo ta karbi waya a hannun ki ban sani ba kuma baki fada min ba akan me kika bata tunda ba ita ta baki waya ba watace fa don me zata karba taba Asiya Asiya ta fiki garenine ko me ? To nan tazo muna da tashin hankali a bata waya ni kuma nace ta dauko mata ta bata ta fita tana zage zage ba wanda ya kula tana kallon mum din kafin ta juya wajen yan uwarta tace . Wai me yasa mummy take hakane for god sake bana son irin wanan abin ta sani daddy ma baya so to ba zan ba Asiya wayar ba tunda ba wani ya saya min ba. No ki bar mata ita ta bari zan sayo mata waya idan na fita shike nan don Allah abar zancen ya tafi a haka please tayar da zancen yana iya kawo matsala kuma a gidan nan yanzu. Kinji dan uwanki yace abar zancen nima ban faye son ta rike wayan nan ba yanzu tunda karatu takeyi gaskiya no bari dai a saya mata tunda duk yan uwanta suna da waya itama a saya mata din ya fada. Sai ta juya ta fita ya juyo gareni yace wani irin wayane mummy ta karba nace ko iPhone nawa karama daice naji su halima na fadi mum