Sashe 27
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tace kaji wata shegiya nan halimatu din nan bansan me kika tare mata ba a gidan nan. Anyi hakan koda zai dawo sai gashi da waya ya kawo min ina falo ya jefo min ledan saman jikina yace kardai ki biyewa waya ki bar karatu mum tace nina sagartaki da waya ya juya ya fita. Ihun murna na sake jiki na rawa na fada jikin mum ina rawa tace ohh abin naki ya zama shegantaka yanzu na karbe wayan naga tsiya kuma nan na shiga rokonta murna ya hana bakina rufuwa a lokacin caji nakai na saka wayan. Anyi hakan da kwana daya saiga mahaifiyar halimatu wai tazo ganin uwarta Dada har part din naje na tareta amsawan da tayi min ba yadda muka saba da ita bane. Zuwa yamma da mum tashiga saiga mace ta fara yankar kauna tana fadin dama da biyu tazo garin nan ke kubura ki fada min tsakanin Zainab da Halimatu wayafi galihu a gidan nan wajen ku. Ina dai zariya daya muka fito nida mai gidan nan mum tace hakama aida uban zainab ko don banga bambamci a tsakanin ku ba kai har mu tace ato uwa daya dai ta haifomu dashi ko don haka banga dalilin da za a saka min ya gaba da bakin kishi ba. Zainab don ta iya makirci da kisisina tabi ta kammale ku babba da yaro kun mayar min da ya saniyar ware a gidan shine nazo in kafa sheda don ku sani ita ma dai nan gidan kawuntane ehh,hey. Au da kice don ni kikazo ashe tace bake daya ba wallahi dan kowa nazo ke can kin koreta saboda taki yarda ta zamo boyi boyin ki nan kuma data dawo suma sun tasa min ita agaba. Au abinda ta fada maki ke nan dama to inkin dauka haka din ne saidai ki sani ni ban dogara ga aikin yaro ba gasu nan ki tambayesu kiji mamace dai wanan kamar yadda kika fada kuma nima inada iko da abina. Jin hayaniyarsu yasa hankalin mutanen gidan ya dawo gunsu har Dada dake waje tana gugan goro da zata watsa a bakinta tana fadin me nake gani nake kuma ji hakane ke Atika ? Barta hjy tace da biyu tazo gidan nan saboda mu don mun saka mata ya a gaba da wullakanci ehh haka nace ba,ayi hakan bane dama ta fada a gadarance. Atika ki daiyi da mai kalan diya mata amma bani ba don nawa da Allah ya ban sun isheni tinkaho a ko ina a garin nan don ba sai naje ina karamin murya kwaso wasu diyan ba . Sai fadan ya rikice masu tsakaninsu su uku kuma Dada tayi rabo har ta gaji ta fashe da kuka sai anty Nafisa ta daga waya ta kira daddy a kasuwa ta fada mai sai gashi yazo rai bace. Bai tsaya tambaya ba don Nafisa ta fada mai abinda ya kawo rikicin don haka yana zuwa yace Atika ki tattara kayan ki da yarki ku bar min gidana a yau din nan basai gobe ba. Nan kuma Dada tasa mashi kuka tana fadin sai dai suje tare ina zasu da daren nan ga yara dole ya barsu akan washe gari zasu tafi har halimatu di dake ta kuka wai bata zuwa saboda rashin zuciya. Ni dai ina part din mu tunda ba abin kallo bane nan aka zauna bayan sallah isha,i daddy ya tambayi ba,asi mum ta mayar mai da komai tun farko tunda itace babba a cikinsu. Ya juyo kan halimatu yace yau ga ranan magana tunda kikazo gidan nan Kubura ta taba koranki a part din ta ki fadi yau ta girgiza kai yace ba kai nake son ki girgiza min ba ki bude baki kiyi magana. Tace bata taba ba to meyasa kibar part din bayan kinsan nan na ajeku wurinta yar uwarku ta tsaya ke kuma kika canza sheka dama irin wanan rana nake jira yazo ai . Sai ta dukar da kanta kasa yace magana zakiyi ko gobe tunda safe in sakaku motar katsina daga ke har uwarki wallahi jin ya ambaci wallahi yasa ta dago kai ta kalleshi tana dan kokarin budan baki tare da fadin dama dama naga tafi son zeey ne yasa kawai nabar part din. Dole inso mama tunda ke,,,, dakata don Allah banzo gareki ba ya fada sai mum din tayi shiru tanawa yar uwarki wani abune ke batayi maki ba ? Ta girgiza kai to ya kika gane tafi son mamana dake nan ma shiru tayi to tunda baki da amsa kuma ba koranki akayi ba akan me zakije wurin uwarki kiyi hadi ? Nifa yaya bashi ba gidan nan kaf an saka mata Ido sai a gaban idon ka ake nuna anasonta har satan nama da kudi da tufafi saida malka da yaranta suka dafawa yarinyar nan. Gashi kullun hjy malka da yaranta komai zasuci ko susha itake dafa masu amma hakan baisa sun ganewa yarinyar nan ba. Kutuma wace yarinya ke muna wanan aikin wazaici girkinta ko jagwalgwale amma kin rainawa mutane wayau watau kinzo fada daine akan yarki. Meya rabata da part din hjy kubura idan ba son jiki da munafunci da kika koya mata bandashi bata iya komai ba a rayuwanta. Idan kince hakan gaskiya kika fada nazo nan da biyu kai kuyi min shiru gobe ki shirya keda yarki ku koma gida ta huta yiwa mutane bauta a nan shike nan daddy ya fada masu. ZAINAB IDRIS MAKAWA [2/9, 09:51] Aishatu Aliyu Musa : DUBA MIN BAYA FOKON,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. An samu an sulhuta da kyat bayan yan kokekoken daya biyo baya tsakaninsu kan cewa zata zauna tare da Dada a part dinsu tunda dama a wajen Dada take zaune din. Don Dadan ta nuna cewa tashin tashinta idan ya kori Halima din da a yanzu nida Dada muka saura kiranta da halima ita Dada sai tace halimatu din nan niko ina fada ta dinga fada dani ke nan wai ina bata mata suna. Don yanzu ta koma amsa Sadiya a school su kuma yan gidan daddy din yan gayu suna kiranta da Sady cool sunan da takeso ke nan fiye da wanda ake kiranta dashi da baya. Ga karyan tsiya tana nuna ita din diyar cikin daddy ce ta dinga shara karyan arziki saidai azo a tambayeni ince ehh hakane din amma kowa yasan ni iyayyena suna katsina don ko a hausa na suna gane cewa lalai daga katsinan na fito. Saboda hausan namu ya dan bambanta da nasu kanawa kamar yadda hausan kowani dan state ake saurin gane jaharshi don harshe da dabi,u yakan bambanta. A cikin wanan dan takin mahaifana suka dawo kano da zama a cikin gidan da daddy din ya gina masu wanda wasu yan uwa manya sukayo masu rakiya har zuwa kano din. Naji dadin wanan abin duk da dai ba,a wajensu zan zauna ba amma munje nida hjy Mum mun dan dade a gidan tare dasu naga kannena sun kara min girma sosai yayin da baba bai boye jin dadin ganin yadda na koma ba yanzu a hannun Hjy Mum dake rikona. Don nazama wata babba dani komai ina yinsa cikin hankali da wayewa wanan yasa iyayyen nawa jin dadin ganina din da sukayi a lokacin. Ana sallah azahar nice ma na matsawa Mum da mutafi saboda ranan mum ce zata bawa daddy abincin dare don haka muna da aiki da zamuyi idan mun koma din. A bakin Hjy Mum da suke zance da diyata naji irin rikicin da akayi da hjy Mommy da daddy akan dukiyan da daddy din ya warewa mahaifinmu da sunan ya bashi su halal malak har gaban Allah. Wanda hakan ya tunzurata ta shiga ballawa daddy din miyagun magana marasa daddy har abin ya kaisu ga saki a tsakaninsu sakin ma kuma na tijara da har yasa ta bar masa gida wanda sai a lokacin nasan ashe mommy din wai bata gidan na daddy. Allah shedata banji dadin jin wanan maganan ba duk da ba,a kan baba kawai ya faru ba amma kusan hakan shine sanadin faruwan komai a tsakaninsu din. Nan na barsu suna hira na dauki abincin Dada don in kai mata don ina son in dawo in wanke uniform dina da ban wanke ba a ranan kafin dare yayi sosai duk da ina da wanda zan saka a jikina din. Tunda na doso part din nake jin muryan Dada yana dan tashi da alaman fada takeyi da wani a lokacin har na karasa na kai abincin can ta baya dakunan da su Dada din suke zaune wanda aka gyara mata shi don an saka komai irin su kujeru tv capet da sauran abubuwa wanda a takaice dai daddy ya dauko gyatumanshi ya dawo da zamanta yanzu a kusa dashi ke nan ba zancem komawa katsina kuma a wajen Dada din . Duk wanan yana cikin tashin hankalinda mommy din tayi da daddy har yaja mata saki a cewan bakunan su wai mommy tace don daddy yaga baida lafiya shine yake rabar da dukiyanshi ga yan uwa don yai masu keta su iyalanshi yana kwasan dukiyanshi yana bawa yan uwanshi da sunan taimako. Idan ba aikin asiri ba wani mai hankali zaiyi wanan abinda daddy din keyi don haka ita wallahi bata yarda da wanan tsarin daya dauko yi ba. Saidai in hakane ita ma yayanta ya ware masu nasu kason ya basu tun yanzu kowa ya rike a hannunsa mamaki kwarai daddy din yayi da kalamanta din gareshi. Har ya dago yana fadin waiko malka kina cikin hankalinki kuwa ko so kikeyi ki konani da gaske ki hana min lahirana a sanadin ki ranta ya baci tace ina ruwanta da lahiranshi ita su dai ya basu dukiyansu kafin asiri ya kara