Sashe 51
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shiga lissafo irin abin arzikin da tayi min mummy sai baki ya mutu kuma ta koma fadin ai dole tayi min hakan. Dama ta rikenine don ganin iyakar mummy din don ta nunawa duniya ita ba kowa bane san nan ai sun san komai duk abinda aka gani daddy ne ya bada kudi a boye akaimin shi son kawai ya farauta muna rai. Niko nace ashe mummy tasan dan nata abin banzane ke nan tunda har take iya zaton daddy ya hada muna dacin hanci don a zauna dashi ko ? Da yamma muna zaune ana hira gida ya cika saiga Dada ita ta saka min lale ta shammaceni banyi aune ba ta zuba min akafa har zuwa sawayena da hannayena tana guda. Wani irin zabura nayi ina hawaye tare da furta ta faru ta kare ke nan na dai tabbata matar hafiz ke nan na fada a zuciyana na mike zuwa babdaki. Kuka nayi sosai kafin nabawa kaina hakkuri na wanke nafito don kada mum ta gane cewa kuka naje nayi saboda nayi alkawarin ban sake yarda inyi kuka kuma kan auren. Nan buki ya fara ga jama,a ko sai zuwa sukeyi daga garuruwa don su sheda kawai su nunawa iyayyena farin cikin ganin wanan lokacin kamar yadda yake a al,adance. Kamar ko wani buki kuma ko wani gida aka hada bukin yayan daki biyu ake samun yan tsegumi da gulmace gulmace wanan ma namun hakan aka samu. Hakan yafi faruwane kuma abangaren mummy din hakane ma a asirce mum taba da girki da za a dinga yo mata daga wani gida ana kawo mata nan gidan kawai saidai aga ana shigowa da manyan kuloli na abinci apart dinta. Sai hakan kuma ya tsonewa mummy ido sai gasu har gaban Alh wai bata yarda da tsarin da mum ta dauko din ba nan daddy yake fadin baki yarda ba sai kije kiyi yadda tayi din mana kema. Ni dai nasan Kubura bata tambayeni kudi wai zatayi girki ba haka kuma nima ban dauki kudi na taimaka mata tayi girkin nan ba ina duk abinda tayi tayine da sunan taimaka muna dai a cikin sha,anin nan . Tunda dani dake keda bukin nan ba dole bane sai kubura tayi wani abin bajinta da har zai tsone maki ido idan kina da tunane mu tayi wa wanan karan ai a nan. Duk da haka mummy bata fahinta ba don bata yarda ba kishi ya rufe mata idanu a lokacin sai cewa tayi dama ai bakinsu hadene gashi ita din dake cewa mum tana da rowa . Itace irin halittan nan ne da komai sai sunci riba dashi kudin ba bata samu bane wajen miji bata dai iya fitarwa ne akashewa jama,a ta zata daddy zaicewa mum a hada a dinga kawowa ko wani part ga nata wautan. Sai daren da za a daura aure hafiz din dasu yaya Addil daya shawo kansa suka iso garin cikin dare sosai bayan mum tayi ta korafin rashin zuwan nasu akan lokaci. Tana cewa rashin zuwan matarsa da wuri yaci mata rai ace tana bukin kanwarsa amma ace wai ba matar Addil a wajen don tana yar rainin wayau. Wanan yasa washegari da sukazo mum din taki tsayawa ta basu lokacinta tana nuna masu fushinta ga hakan da sukayi na basu kyauta mata ba son gaba su gyara. Amma sai gashi itama Aishan wai tayi fushi don mum bata nuna tana da muhinmanci ba a wajen ta ga idon jama,a din haka ta sulale ta fice daga gidan ba tare da kowa ya sani ba. Saida mum tace akirata tana kitchen shine ake fadin ai bata nan a zaton mun ta shiga wani part na gidan ne sai gashi ana fadin anga fita ai tabar gidan. Ita kuma mum nata matsala ke nan daya fara bullo mata shine matar danta bata da mutunci balle kirki don sam bata da tarbiyan bin nagabanta uwar miji da take tankat uwarka ga me tunane amma ita ko gaban dan sai ta nemi ciwa nasa mutunci. Don hakanema gaba daya gidan ba wani mai dogon shiri da ita baya ga gaisuwa da za a tsaya a danyi sama sama don gani take ta girmi wayewan kowa a gidan don haka babu sa,anta take daukankai Sai dai ita a wajenta kuma gani takeyi kawai dai ba,a sontane don hakane bata nemi hanyan gyarawa ba sai iskanci da takeyiwa mutane tana kara bata kanta a zuciyan yan gidan mijin nata. Don ko hakan datayi ba wanda baiji wanan labarin ba kowa na tir da halinta a cikin taron nace kinga bone kowa ya zageki Allah yasa mu gane gaskiya mu gyara ba sai ana son mu zamu kyautatawa uwar miji da yan uwan miji ba halinmu zai muna alkalanci a gid ajen auren mu mata. ZAINAB IDRIS MAKAWA [2/29, 06:30] Maman K: DUBA MIN BAYA FOKON,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Rana bata karya saidai uwar diya tayi kunya to Allah ya gyara kamar kullum wanan uwar diyar batai kunya ba kamar yadda kow keyin abinsa cikin rufin asiri haka Allah ya rufa wanan asirin don an daura aure kamar yadda kowani aure aka saba daurashi lafiya an kuma samu jama,an da suka sheda hakan bila,adadin wajen taron. Karfe hudu bayan daurin aure masu waliman da hjy mum ta kira sukazo suka cika unguwa da lasifika suka hau sharfi akan aure da biyayya ga iyayye suna kuma kwatance da irin kokarin daddy wajen tada zumunci da zamanin nan yake neman gagara a tsakanin yan uwa ko makwabta. Anyi an watse lafiya an raba gifts wani mai hoton amare mu uku wani kuma hotona da ya hafiz ne a manne duk wanan kokarin mum ne datayi na aurar da yarta. Sai washegari za,a tafi da mairo da Asiya garuruwan mazansu saini dake gari da za,a aje gaba da unguwarmuce za,a akai ranan. Duk dako angon ya fada masu cewa komawa zaiyi washegari don matsa mashi da daddy yayine ya dauko pass yazo halartan bukin ba don wani abu ba can. Duk da jin kalaminsa hakan baisa daddy ya girgiza ba ga abinda yayi niyar yi haka mahaifina ni dai sai ince tu ranan da yazo wajen mum sukayi magana ban kara ganinsa ba duk ko da kaini gidansu da mum tasa akayi ana gobe za a daura muna aure a can na wuni cikin yan uwana tare dasu. Sai yamma akaje aka daukoni amma banga baba ba ko a idona haka mahaifiyata akwai damuwa sosai a fuskanta amma saboda kawaici irin nasu batace dani uffan ba har lokacin dana barsu din. Ana gama walima muna zaune saiga Dada ta shigo part din mum tana fadin ina amaryan hafiz din ina jin hakan na bata rai take na hade fuskana . Take fadin ki taso iyayyenki na jiranki waje iya abinda ta fada min ke nan dole na tashi nabi bayan ta bayan na nemo mum na fada mata. Mukaje da Samira don tare muke sai dawowa samira tayi ita kadai tana fada masu cewa su daddy sun wuce dani ai sun tafi su kaini gidan mijina. Nan take gida ya rude da mamaki mum kasa hakkuri tayi daidai motar su ya tsaya saiga kiranta tana tambaya hankali tashe da Alh wai kunje kai mama dakinta yace gamu har mun iso gidan ai ya kashe waya. Su daddy Enugu suna gaba su biyu daddy kano yana rike dani har zuwa cikin gidan yana saman bakinshi da nema muna kariya daga sheda da sauran abin ki ga musulmi. Gabana yayi wani irin faduwa a daidai lokacin da muryan hafiz ya daki kunnena ashe yana gidan yana sana,arshi kiran da daddy yayi mai yasashi tashi ya feshe gidan da air fresher gidan ya dauki kamshi lokaci guda. Nasiha sukai muna sosai saidai na daddyn mu nasihan shi kamar wanka da jurwaye yayi muna don nasihace ta gugar zana garemu daga shi har ni kan zaman takewa. Har kofa ya rakasu bai dawo ba saida yaga motarsu ya daga daga wajen ya juyo zuwa ciki ina nan rakube a inda daddy ya barni zaune sai tsukinshi naji hakan ya sanar dani shigowanshi daga rakiyan da yai masu din. Banza ukuba yanzu kika shigesa duk wanan barnan miyau bakin da daddy keyi akanki zai kare bani ba don ki sani daga yau kin shiga tashin hankalin rayuwa ke nan a rayuwanki zakice nace. Tunda har kukai sanadin mai dani bazawari bazanyi ni kadai ba koda ace maza suna zawarci saidai muyishi tare dake saina bar maki mugun tabon da gobe ko ance maku ga kwadayi dake da iyayyen ki makwadaita zakuce yana wari. Ke dasu sai kunce,,,,,, Knocking din kofan gidan da akeyi ya hanashi karasa abinda zai fada yaja wani ubab tsuki yana fadin kawai kawai mutum yana zaman zamansa a dauko masa masifa a sarkafa mashi a habasa shakat da rayuwansa wanan wani irin masifane wai a hana mutum hutawahasale. Yana bude kofan a hasale anty Nafisace ke fadin dama nasan kana ciki tunda naga ba,a bude da wuri ba ko har ka fara shan angoncinne kai ni basu Dada waje su shigo don Allah ka wani rdakin kofa kamar baka son mu shigo yan kawo amaryane sukazo. Ido ya waro waje yana fadin wace amaryan ke nan kuma ya tambaya cikin mamaki. Dada tace naka mana ko an kawo maka itace dama tana zolayanshi ido ya waro waje yana kallon kofan dakin daya barni a zaune cikin razana . Gudan da yajine ya kara firgitashi yana fadin wai da gaske Nafisa ita wacan na zaune a dakin fa ita din wacece Dada ta amsa data karfece wanan kuma amaryan danko muka kawo maka yana bin samira dake rufe da kallon mamaki. Kaje dakinka don Allah kada mata su sameka wajen