Sashe 2
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
waje daya ga iskan sanyi da yake huro muna don yanayin da muke dosa din na daban da namu yanayin da muka baro a baya mai dan surkin zafi zafi zafi da kura. Fada gari fada kauye har Allah ya kawomu lafiya gidane mai kyau irin ginan da din nan mai nuna halin gameshi don yaji simiti da yar dakalin zama a wajen gidan . Ga wasu ginan na zamani wasu kuma shige daya da namu nan baba yace dani Humaira yau gaki a gidan ku na gado nan da kike gani kaf unguwar nan kusan duk abu daya muke sai yan tsirarune surke a cikin mu nan. Ido na ware ina kallon ikon Allah wai yau mu dake cikin bunu mune a wanan gidan haka mai kyau duk dasu yan wajen sunawa gidan kallon ginan kauyaci don samfarin dane ginan bana zamani ba . Da kyar na sauko saman akori kuran na diro kasa ina faman raba ido cikin unguwar ina bin ko ina da kallon kwam saida naji muryan baba yana fadin bissimillan ku mushiga gidan mana yasa naja kafana da sukai min nauyi na hango wata mota a guje ta shawo kwanan da gudu na manne da gina don kada tazo ta kadeni a wajen nawa ya sameni kafin nabi motan da kallo don gaskiya mukan mota a can akori kurane muka sani sai yan futu futun da can ba,a rasa ba da sukan shigo lokaci lokaci garin muyi ta ihum ehh mota mota mota. Baba yaja hannuna zuwa cikin gidan ina jin yayi sallama nima nayi azatona zamu samu wasu mutanene a cikin gidan amma sai naga sabanin hakan babu kowa saidai akwai alamun wasu sun zauna ciki sun tashi don gidan ba sabo bane gaskiya. Tambarman dake hannun baba dashine ya fara shigowa dashi a hannu ya ahimfida don inna yana fadin suzo su zauna ke kuma humaira muje waje mu duba abinda zaki iya daukowa ki shigo dashi koda muka fita yaran unguwama suka taya baba shigo da kayan sunawa inna sannu da zuwa a cikin ladabi sai hakan ya bani sha,awa . Can kuma saiga matansu sun shigo su suka share gidan suka wanko dakunan kafin aka saka kayan mu ranan mun kwana cikin wutan NEPA ga fankan sama yana kadawa sai da muka dunkule saboda rashin sabo da hakan. Washegari tunda safe muryan Dada tsohuwar gidan ya tayar damu din daga barci ta shigo yi muna sannu da zuwa suna magana da baba da inna da can jefi kake jin muryanta haka na fito na dauki buta na zaga bandakin dake can kuryan gidan na fito na duka ina alwala suna zance hankalinta yana kaina yadda nake alwalan naji tace. Zaman kauye bai hana kaba yayan ka tarbiyan data dace ba Abdullahi hakan nada kyau yaro ya bude ido da ibada ko ina yaro ya shiga za,a sameshi da natsuwa. Ban dai tsaya ba daki na shiga na tayar da sallah na fito bayan na fito nazo don in gaidasu da kwana a nan na samesu ita na fara gayarwa kana na dawo kan iyayyena. Naji ta kara fadin ehh lalai wanan takwaran namu gaskiya anayi da ita idan haka ya daure mata kada ki biyewa yaran nan da basu san darajan babba ba sai shagantaka a gaban mutane da shakiyanci. Bata bar gidan mu ba saida tajawa inna kunne kan zama da mutanen shiya har mu bata barmu ba ta danyi muna nasiha kafin su fice gidan tare da baba daya dafa mata baya. Lokacin inna ta kalleni nima take fadin yar manya kin daiji kin daiji irin nasihan da nake maki kullun ko a can kusan shine tsohuwar nan ta maimaita maki a yanzu. Don Allah kece babba a cikin ku ki kama kanki ki rike yan uwan ki a wanan bakon wajen duk da gidankune amma mu bakine a cikinsu don bamu san akidunsu ba nan. Ki girmama kowa ki kama darajanki duk da kina yarinya akwai bata garin da basu san yaro ba basu yaro ba basu san babba kedai ki tsaya matsayinki a inda muka ajeki banda wuce gona da iri kije hangen nesa . To inna nace duk da ban gama fahintar inda zancensu ya dosa ba sai ga baba ya shigo da ledoji a hannunshi yana fadin humaira dauko kwano ki juye kosan nan ga kayan shayi kuma ki hada koki kawo gaban innan ku ta hada a raraba a karya kafin anjima in fita in hado muna abin girki a gidan. Yadda baba yace din hakan nayi na hada ruwan zafi a tsohon murhun inna da mukazo dashi wuta ya kama don inna ta koya min aiki tun ina da shekara bakwai na fara aikin gida tare da inna din. Har zuwa yanzu din da nikanyi ni daya saboda nauyin da inna tayi na cikin jikinta da yake yawan bata matsala ko wani lokaci cikin rashin lafiya inna take. Mun karya a cikin sallama da daukin yau bamu ci sauran tuwo da muka saba kari dashi saiga shayi mun fara karyawa dashi har muna fadan burodi baba ya karawa sadiya nasa don ya kashe maganan tunda tace karami muka bata. Ruwa yai zafi na tashi na dora sukayi wanka na shafa masu mai nakaiwa baba ruwa yayi wanka naga ya dauko tufafi masu kyau ya saka sabanin can da yakanyi shigan yan kauye riga daban wando daban haka kuma zaiyi kwanaki dasu a jikinsa sai gashi nan naga ya saka kaya wankaku iri daya kuma yayi wankan safe. Kinsan yaran kauye akwaimu da wayau da saurin fahinta indai nazarine ga iya maida fadi a bakin yan kauye saidai kaf din mu halin innan mu ne damu don bamu da yawan surutu gaskiya don haka inna take shiru shiru da ita muma ita din muka dauko da rashin magana sosai. Ganin inna bata zauna ba yasa nima na mike tare mukayi gyaran gida da inna mun kafa ransdunan mu na kasa mun gyara kitchen din kwanon na kwashe tokan da wa yanda suka tashi a gidan suka barshi da sauran kayayakinsu da basu so muma mun dan tsunta a ciki sauran nakai wajen shara na tara don bansan yadda zanyi dashi ba sai baba ya dawo ya fada . Saiga gidan ya koma tas har yafi wanda makwabta sukai muna kyau na kafa labule ako wani dakin na gyara dan gada gadan inna na dora masu dan tsohon katifansu sama na shifida zanin gado mai dawisu da inna bata faye amfani dashi ba sai lokaci lokaci shina shifida mata saiga baba ya dawo da cefanai su mai magi gishi nama dan tumatur da tattasai inna tana gyara na fito na amsa na tayar da uwata nayi jajagen kayan miyan yadda muka sabayi a kauye . Ban tsaya bakunta ba don a cikin gidan mune nan mu kadai saidai abin kurciya dole daga inda inna take zaune tanayi ta gyara min har na dafa muna shinkafa da miya muka zauna mukaci muna jin dadi har kasan rayuwan mu don bamu ganin tumatur sai ranan da baba ya shigo birni don hakane a kauye ko yaushe cikin cin tuwo muke ko shinkafa da mai idan anyi abin dadi a gidan mucishi man shanu dai ne baka raba baba dashi a gidan mu don hurda da fulani da baba ke yawanyi a daji wajen aikinsa idan yaje yake dawowa da nama da man shanu mai yawa ayi amfani dashi. Amma baikai ko ina duk matan babban gida zasu kwasheshi wajen roko har sai sunga karshen kwano sanan zasu huta zuwa tambaya yanzu ko da bamu nan nasan saidai idan mutum ya saya din zaiciwa bakinsa ZAINAB IDRIS MAKAWA [1/7, 21:41] Aishatu Aliyu Musa : DUBA MIN BAYA FOKON BIRI ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Zauren gidan namu sabo shine daga farko sai idan kashigo daga ciki kuma zaka fara cin karo da rijiya sai dakin farko wanda babane a cikinsa. Sai tsakiya dake zaman inna na karshe kuma mune da kannena a cikinsa da shimfidan mu na tsohuwar katifan inna da take yar muna dashi kasa muke kwamciya tun a kauye. Tsakar gidan da simiti tako ina sai kitchen daga gefen dakin namu sai kuma wani dan daki baikai sauran dakunan girma ba shi kuma sauran tarkacen mune a cikinsa da yan akuyoyina da aka saka a cikinsa. Ban gajiya da kallon Gidan don abin yana burgeni ko yaushe ina waje ina bin ko ina da kallo sai ina ganin kamar munzo bakuntane zamu koma. Inama ace su mama tambai zasuzo suga gidan nan namu da bakin ciki saiya kashesu don nasan zasu koma kauye da labarin bakina fadi tsuliya na fada na abinda suka gani a katsina din. Saida muka kwana biyu ranan muka shirya da safe muka shiga gaida Dada daga nan ta turamu da wata jikanta taikai iyalan Audullahi gidan yan uwa su san mu mu sansu. Matashiyar itace take fada muna alakan mu da inda muke shiga din wanda maganan babane duk yan uwane saboda yanayin inna muka dawo gida badon mun gama zaga dangin Ruma ba a lokacin. Gashi yadda baban mu keda kalangu a gefen fuskanshi duka biyu haka suma nake ganin hakan a fuskansu har dayara a wani gidan muka dawo gida ina wanan tunanen ni kadai a raina. Wanan abin kamar a mafalki saiga baba yana muna zancen makaranta nayi murna nayi murna sosai islamiya aka fara kai mu a nan kasan unguwa har uniform aka dinka muna. Muka saje da sauran yan uwa wanda duk yawanci diyan dangine a wajen a gaskiya duk wanda iyayyensa ke da ilimi ko uwa ko uba ya godewa Allah don za a bashi tarbiyan da ba zai wahala ba a duniya sai idan shiya jefa kansa cikin wahalan. Don hakane