← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 61

Sashe 15

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yar uwa kiyi hakkuri da rubutuna yadda kikeso din ba haka tsarina yake ba idan zaki karanta ki karanta sabodake ba zanje lahira inkasa amsa tambayan da za ai mun kan rubutun nan ba. Akwai masu rubuta rommatic novel saiki nema ki karanta hakan ba laifi bane novel dina yana tafiya bisa ga yadda rayuwan mu kan kasancene a tallakance don babu karyan arziki ko karyan al,ada aciki saidai idan na rubuta bisa kuskure don haka kiyi hakkuri ki barni hakan. Saukin abin masoyana suna fahintar hausana da kuma sakona wanda nasan dole cikin kashi dari kashi biyar suna amfana da rubutu na don haka donke kadai kince wani abu bazai dameni ba haka tsarin rubutuna yake masu hankali ke gane sakona garesu koda yaushe. ZAINAB IDRIS MAKAWA [1/22, 09:09] Aishatu Aliyu Musa : DUBA MIN BAYA FOKON,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Buki kan ya soma don zance tun zuwan mu dai masu gidan basu zauna ba sukan inka debe hjy mum dake dan harkokin ta itama don shirin bukin don muna nan aka canza masu set din part dinsu dag daki har falo komai iri daya kalane kawai bambancin kayan. Koshi saida hakan ya dan kawo rikici a tsakaninsu donko hjy malka tace kalan data zaba ke nan tun shego don me hjy mum zata daukeshi. Ita kuma hjy mum tace ai bata san itace ta sayo masu kayan ba dama sai yanzu data fada in haka ba za a bari matsayin ta na babba ta dauka ba saidai baba ya bar kayansa. Nan rikici sosai ya tashi saida Dada ta fito ta tsawata masu a cikin fushi tace ke marka ban gane me kike nufi ba a nan shin ba shigowa kikayi gidan nan kika samu Kubura ba. Ko har kin mantane wai in tuna maki don ni komai yana cikin kaina kamar yanzu akayishi kada ki mayar da mutane wasu bican don kawai shi ya zama shasha kuna juyashi keda diyan ki yadda kuke so. Tirkashi ranan kan naga fadan manya ba dadi don idan kana kusa kunnene kan girmi kaka duk da muna daki hakan bai hana miji komai dake wakana ba wajen. Shi ya dawo daga kasuwa ya kashe wanan wutan daya hada inda yace don ya bata kudi ai basuyi za,a sayo wa yanda kalansu ya bambanta ba tun shago kudin komai iri daya ya basu don haka ta bari hjy kubura da itace babba ta fara zaba. Dole ta dauki kalan milk din ita kuma hjy mum ta dauki ash color din aka zauna lafiya yan company suka jera masu kayan aka fitar da wanda muka sama akai sauyin su zuwa wasu dakunan. Don haka wuni cur mukayi muna wanan aikin na gyaran part din duk da son jikin halkmatu ranan saida ta amfana ga aikin itama aka rutsa da ita. Don bayan mungama na hjy mum kamar yadda mukaji yan gidan nakiranta muma muka kama nabar gwaggon da nake fadi da farko don ko nace gwaggo sai su kama min dariya kawai. Wanan yasa nabar kiranta da gwaggo din nakama hhy mum yadda kowa ke fadi a gidan a yadda ta rikemu dole na mayar da hankali kanta yanzun ma na rage shigowa wajen Dada idan ba aiki muka rarage a part dinta din. Bata da yawan magana haka mukan zauna zugun sai in akwai wuta ta kuna muna kallo wanda kallon ma dai wa,azine su tafi kamowa sai idan zata shige zata kai muna tashan da ake film mu kalla. Zaune muke mun zubawa tv ido ana wa,azi akan sallah nan kan bamu da laifi gaskiya duk mu muna tsare sallah saudai kara fahintar hakki akan sallah din da yanzu muke sauraro a tashan da malamin keyi. Talla sukaje irin na gidajen talabijin lokacin ta dan nisa tace damu yakamata gobe na kaiku wajen gyaran kai a wanke maku kai kuyi kitso har kumshi don idan sun fara shagalin bukin nan baku da lokacin hakan . Daga inda nake kwance na amsa da to tace kawunan ku yana son kitso koba duk sati kuke kitso bane budan ba halimatu sai cewa tayi sai zainab ba ita da mamanta ta iya kitso duk sati take masu. Kefa hjy ta tambaya cikin kallonta tace nikan gaskiya yana kai sati uku huduma banyi kitso ba ta fada tana dariya tace jam kina diya mace kike barin kanki babu gyara haka ko baku san kun girma bane wai ? Muka kalli juna nida halima din tace kunyi sa,a kunzo lokacin kakanin mu sun mutu aida suna nan da yanzu ko wacen ku tana gidan mijinta tana aure. Indai yadda nasan akidar gidan mune na da komu dai primary aka barmu mukayi zamana ikko ne nasamu har nayi secondary a can din ina batun shiga jami,ane Allah ya karbi ran mijina lokacin. Zakice sa,arta muke wani lokaci idan mun zauna muna hira da ita amma saboda cika idonta a fuskan mu bamu iya sakewa da ita muna zance haka dan dama ma halimatu don ko lokacin itace tayi magana. Tace haka Dada ta fada muna Allah ya jikansa ta amsa da amin nima na kara fada tare da dorawa da Allah yasa ya huta aljanna makoma a garesa tace amin . Ban taba tunanem zan kara aure ba a lokacin amma abu ga mai magabata ban jimaba suka kara hadamu aure kuma da babanku nan ashe rabon yayan nan ne dama sai bata karasa ba yadda bahaushe kan fada din suce ya kashe shi. Hjy mum ina suke ne wai bangansu ba mana Dada tace muna kuma kina da yara ai tace suna waje suna karatune dukkansu naso ko karamin abar min nan Alh yaki ya turaahi madina karatu . Tunda ya tafishi har yau ko hutu baizo bama shiyasa yanzu aida nasameku nake jin kamar kada ku tafi wallahi don kuna debe min kewan kadaici sosai wanan zuwan naku. Sai lokacin nayi magana nace wai mukan ai mun kusa komawa school ma hutun mu ya kusa karewa kai mai sunan hjy har ina cewa zanwa babanki magana ya bar min ke nan mu zauna tare. Da sauri nace wai innata bata yarda ai shima baba nasan bai taba yarda da hakan wallahi bai yarda halimatu ta fada a karshe tace ranan fa da Dada tace ya bari ki dawo nan da kwana wajenta cewa yayi ai Dada tayi hakkuri. Duban baya fakon biri sai meshi don Allah Dada tayi hakkuri ta barki a gaban innanku zaifi tunda kina shigowa ai ko wani lokaci. Ninayi mamakima daya yarda kikazo din nan wallahi koda Dada ke fadin ai dake za,azo wallahi ban yarda ba saida kika fada min da bakinki cewa tare dake zamuzo. Dariyan hjy mum din yasa muka kallota don bamu fahinci me takewa dariya a cikin zancen ba tagane me muke nufi tace shi yaya garba din yace DUba min baya fakon biri ? Hakafa yacewa Dada lokacin nakasa fassara wanan maganan nidai na rike kalman kawai a bakina lokacin amma bansan ma,anarsa ba. Aiba wani abu hakan ke nufi ba duba ga zamanin nan da yara basuji suma mutane baka yarda dasu abu a hannunka shine yake abinka ba,a hannun wani ba. Irin hakan da mukan dan zauna tana sake muna fuska yasa muke jin dadi yanzu a gidan bamu ko zancen Dada da sai wani lokaci ma ta kekomu ta samemu zaune ko muna aiki. Washegari din kuwa kamar yadda tace acan muka wuni wurin gyaran kai da kumshi dama ba dabi,ata bace karin gashi don Allah ya hore min suma har gadon bayata da acema ina saka mashi mai da ya sauko min sosai a baya amma kaina yana da santsi don haka shagon mai ya huta dani. Da gashin kaina aka tsantsara min kitson bare bari mai kyau ga wani kamshi dadi na gargajiya mai dadi na tashi a kawunan namu da halimatu dai suka kwasa don tace ita sai ankara mata oulu a kai. Su kuma masu wajen sukace hjy batace ai muna kari ba hakan yasa tayi fushi amma da aka gama kuma sai ta koma murna don sun iya kitso da kumshi kamar tsiya a wajen nasu na bare bari. Hjy mum din tazo ta kwashw mu cikin motarta ni sai kallonta nakeyi ina mamaki don ban taba zaton ko tsamanin ta iya mota ba har tanada shima ashe saida naga ta fito da key munje mun sallami Dada mun fito ta danna key motar tayi kara tun kan mukai waje motar. Yanzu ma din da yamma kuma itace tazo ta kwashemu komawa gida muna faman raba ido ba gida muka nufa gun tella mukaje ya dubamu bai auna muba ya dai ganmu kawai ya tambayi sunan mu ya danyi rubutu a wani littafi muka fito zuwa gida. Mun kamo hanya gidane sai lokacin tayi magana don tunda ta dauko mu kamar ranta yana a bace don yanayinta daya nuna hakan har kana iya ganewa tace. Zaku koma ku samu munyi baki fa don su Addal sun dawo dazun da safe bayan fitar ku duk da nima bansan da zuwansu ba sai ganinsu kawai nayi daga sama kamar anjefosu. Sai ranan na yarda da damuwa nasa babba ya maida yaron dake yawan zama kusa dashi kamar sa,ansa ko amininsa don yadda hjy mum din ke fada muna magana lokacin. Da farko halimatuce tace hjy mum wai Addle kuma tace ba Addale yake ba Addal don yana da sunan baba malam ne mahaifinsu babanku muke kiransa da Addal. Sunan nake maimaitawa a zuciyana na rike sosai can tace akwai dai Allah yanzu don Allah ace an min adalci ke nan duk yaran mamanku malka ankosusu don bukin nan amma ni don son kai dan karamin akawo min shi na ganshi babanku yaki hakan
Chapter 15 · 0% Book details