← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 61

Sashe 40

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dashi duk da nakan dan fito tunda safe bayan nayi sallah na danyi aiyukana irin gyaran part din mu gyaran kitchen ko wanki idan mun tara nakayi saidai baki ganina zuwa rana ko a falon mu zaune saidai daki. Yanzun ma zaune nake ni kadai a dakin na kurawa kasan dakin ido ina faman tunane mum tashigo tana fadin ga yayanki nan falo yana tambayanki. Na dauka yaya Nasir ne na dan dago na kalleta nace wai ya Nasir yazone tace bashi ba Addel dai sunzo jiya yanzu suka shigo yake tambayan ki. Ai nasha ai ya Nasir ne nafada ina mikewa tsaye daga inda nake zaune haka na fito tagal tagal ina dan kako murmushin dole a fuskana nace sannuku da zuwa yaya. Kafin kuma na banbanta nace anty Safiya sannu da zuwa ya hanya anzo lafiya tace lafiya kalau ke mai tsoron aure akan aure kikayi wanan rama haka sai kace wani mugun abu can. Zaune nakai da kyat don ta tabo min inda keyi min ciwo watau suma s una da labari ke nan na fada a zuciyana aure ai bashi zai hanaki karatun ki ba zakiyi karatu insha Allahu ina takardun naki suke ya Addil da sai lokacin yai magana ya fada. Zubur nayi nace suna gun mum yaya sai matar tashi ta kwashe da dariya tare da fadin ke wai karatun kikewa zumudi haka kinko san wuyan dake cikin karatu. Ai ita talent ce ba irin ku bace masu tsoron karatu wai ashe hakan daya fada yai mata zafi wai ya nuna ita din ba mai kokari bace agaban mu. Matsalan da yake fama dashi ke nan akanta saurin fushi abu ba abuba yanzune zata murtuke fuska ta dauki gaba dashi na tsawon wani lokaci. Mum ce ta gane hakan don ko bata kara magana ba har suka fita data mike tana fadin muje ko yace ina tace amma kasan ina da abinda nazo yi dama garin nan in baka tashi ba nika sameni a can zan tafi tana kokarin fita. Mun dake fitowa da takardan nawa a hannunta ta kalleshi lokacin wai har ta fita ko tace ya haka kuma wani abin kuma ya faru yace kyaleta mum haka nake fama da ita ashe zancen ya fada kunnenta. Mum ko cewa tayi kayi hakkuri kowa da halinsa ake zama dashi shine kuma laifin mum din a lokacin abin ya taru ya karu ko part dinsu Dada da sauran mutanen gidan bata shiga ba ya fito suka tafi. Takardun ma nawa nan ya barsu hannun mum yace zai dawo nan zaici abincin dare ya karba sai bayan tafiyansu mum takece min akwai aiki ga wanan fitsararar yarinyar da nake gani . Dama abinda muke masa gudu ke nan ga irin yaran nan da gata ya huda duk sune su Nafisa ido ya bude tun a waje basu kunyan kowa balle tsoro. Haka yake son abinsa yar gayene kuma sosai kamar anty Nafisa itama na fada daga inda nake zaune da a bayane banji zancen karatuna ba ko tsinkawa mum din ba zanyi ba lokacin. Don duk haushinsu nake ji don ina ganin da hadin bakinta itama aka hanani karatu don in zauna inta mata aiki tana morana haka zuciyana ta kiyasta min kanta yasa yanzu ko dan girkin ma na daina yi sosai na fake a rashin lafiya yanzu nako san tagane kawaicine irin nata kawai akaina lokaci . Mum tace kinjiki da wani shirme ke bakiga yadda yayan naku ya fada bane wanan kila ko abincin kirki bai samu gayune za,aci akoshi kome ? Mum kinfa san su yan gayune basu son suyi kibane kila taja tsuki donjin haushin magata din tana dorawa da fadin kin daiji yace a nan zaici abincin dare ki tashi ki masa tuwon masara donshine abincinsa. Ba musu ko na fada kitchen din ina kokarin hada girkin ba wani dogon lokaci nagama na wanke kayan aikin na gyara ko ina nashiga wanka nafito na gyara jikina ganin magariba akwai sauran lokaci yasa naje part din Dada. Anan na samu matan daddy Enugu zaune suna hira suna ganina suke fadin yau kan yar mum ta fito a,a lalai hjy kubura sai tasha ruwa tayi barci ga yarta ta fito daidai yau. Dan murmushi nayi ina gaidasu ban kula da Amir ba saida ya fado min ajiki na ganshi kamosa nayi ina fadin Amir dina nayi missing dinka sosai . Wani kin yi abingasane bayan kina son halaka kanki a banza meye a cikin karatun ko aure da kike wanan fargaban in angon nakine bakiso saiki barmin dama mun saba ai . Nace ke Dada waya gaya maki hakane wai in anyi magana kice wai karatu ko aure to anki ayi auren don Allah dama ai nasan kune mazuga masu zuwa lahira da ,,,,, Ni yar nan ni da nake goyon bayanki kuma zakiyi min wanan fatan da sauri nace nabari to Dadana tace yar nema ai baban naku shine maganin ku. Waini dazun ba Addil bane suka shigo gidan nan matar daddy Enugu take tambayan cikin kallona nace sune zasu dawo wani waje zasu na gajarce zancen a takaice. Nikan ai nace nan dada ke fadin amma ko suna sauri aita lekomu tace yan banzan nan kuna lafiya dama na kula bata da marmari tun ranan da muka kai mata wuni tasa ya dawo damu gida din nan. Kai kedai Dada baki mantuwa wallahi abinda akayi tun tana amarya yanzu kike tunawa kuma kedai bari ina zan iya manta abin nan ai yarinyar nan ta iya yankar kauna dama abinda ubanku yai masa gudu ke nan ga auren. Biyu ke nan na fada a raina mum ta fada yanzu kuma Dada ta fadi wai kodai akwai matsalane ga zaman su nake tambayan kaina a lokacin. Wai yaron nan shi a dole yayi kewana yake nufi na fada don kawai a kawar da zancen ya Addil din data dauko har Dada ta fara kumdumawa matarshi zagi a lokacin. Ina gudun in jawa kaina wani matsala yazo yaji yace ya fasa goya min baya naje karatun da nake son zuwa din in kara samun matsala kuma nawa ya sameni. Nakoyi sa,a sunbar zancen don sai aka kama na yaron ana fadin baijin dadin part din kakansa don basu da lokacin kulashi saboda mummy ba mai zama bace ita. Irin matan nan ne da suke amfani da daman mazan su idan sun fita nema suma su laga su fita suje nasuyi don har ta saba da hakan daddy yayi fada ya gaji ya barta da Allah. Haka suma yan gidan sunyi gulma hakan sungaji sun saka mata ido gashi yanzu har diyanta su dauki hannu suna Allah Allah daddy ya fita ko uwar suma suje yin nasu harkan a waje . Ya Allah ka hada zurian mu da iyayye na gari mun kuma godewa Allah da iyayyen daya bamu Allah ya kara masu daraja yaji kansu badon hakin mu ba Allahuma Amin. Don koda ake zancen nan sunce tun safe mummy din ta fita sukuma yaran bayan azahar sai bayan karfe hudu kowanin zai dawo anyi daidai da kafin biyar daddy yake dawowa daga kasuwa. Ganin magariba ya gabatone yasa na mike zuwa part din mu na samu mum a falo tana waya gefenta na zauna saida ta gama ta juyo tana fadin ke kuma daga ina hakane ? Gun Dada naje mu gaisa na zauna kuma muna hira dasu mum ashe dazun dasu yaya sukazo sun gansu shine Dada ke fada wai basuje sun gaisa dasu ba. Dama nasan haka zai faru wanan yar tana son jamin magana acikin gidan nan haka wancan karon abinda tayiwasu hjy ya kasa fita min a raina. Aiko yanzu ta fada na amsa mata shiru tayi kamar tana nazarin wani abu a zuciyar ta kafin ta dawo fadin ai bari zaizo ya sameni dole ya taka mata burki akan hakan ZAINAB IDRIS MAKAWA [2/19, 21:12] Maman K: DUBA MIN BAYA FOKON,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Ina daki ina sallah naji shigowanshi har kofan mu ya tsaya daidai kofan mahaifiyarshi yana sallama hakan yasa nagane ya dawo gidan kamar yadda yace. Baifi minti biyu ba daidai ina idar da sallah naji muryan mum tana kirana daga dakinta shafawa nayi na mike ina amsawa zuwa dakin nata gani mum nace daga inda take zaune take fadin. Jeki falo kiba yayanku abinci don Allah na amsa dato ai naji muryanshi ina sallahne dama na juya zuwa falon kitchen na fara zuwa na dauko abincin nafito mai dashi dama a shirye yake a kitchen din. Zaune yake saman kujera yayi shiru ya kurawa kasa ido kamar mai tunane jikinshi yana saye da tufafi baki na dinki irin na maza sai yar hulan maza irin na pakistan mai gashi daya kafa a kai abinka da farin mutum sai kalan kayan ya amshi jikinshi sosai. Sallamana falon yasashi dago kai yana amsawa cikin yar siririyar murya nagaidashi tare da fadin akawo nan ne ko in aje a dinning ? No kawo min nan ya fada dama nasani yaranta basu damu da zama saman dinning suci abinci ba dan table na jawo na dora masa a gaban sa zan juya yace . Don Allah dauko min ruwa mara sanyi na amsa da to na kawo mai goran faro da cup har da ruwan wanke hannu na aje thanks ya furta tareda cire hannun daya tokare fuskanshi dashi ya motsawa zuwa gaban abincin. Hannu ya daure kafin ya bude abincin ina jin sautin bissimilanshi a daidai lokacin da zaikai loman farko a bakinshi don ina falon ban fita ba saboda na tsaya tattara kayan da mum ta bari nata watse a falon da muka shiga sallah. Ina shiga mum din tana fitowa tace dani harkin bashi na amsa da
Chapter 40 · 0% Book details