← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 61

Sashe 21

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dake rike dani tayi kokarin ajeni ta mike don hjy Mummy ko gezau batayi ba lokacin balle taje dauko maganin. Cikin tsawa daddu yace kije mana malka sai ta mike ta tafi ta dauko gami da goran ruwa a hannunta ta bare ta miko min duk da halin da nake ciki dana karba zan hadiya saidana furta nagode a gareta. Da kyat na hadiye nakoma na lafe a jikin Mum din ina sauke numfashi wai dama bata da lafiyane Mum tace ina zato don kwance na sameta kuma ai dole hakan ya faru da ita tun safe take abu guda baya tafiyan yan gida. Batune dai bai faduwa amma a maida yarinyar nan gun iyayyenta shiyafi don me za a mayar da ita ko tana can ciwo yazo bayi zatayi ba halan banson irin wanan kalamin daga yanzu naji zancen a mayar da ita zan sabawa maishi a gidan nan kowaye. Nikan ina jin kan nawa ya fara lafawa na yunkura na tashi zaune nabar jikin hjy mum din dake rike dani lokacin tana dan min tofi a jikina duka. Ina zaki na juyo ina kallo daddy din a raunane nace daki zanje in kwanta yace kubura kaita dakin ta kwanta ta amsa da toh Alh muje mama ta fada ta rikeni na mike duk da ina dan iyawa a lokacin. A cikin bargo na kudundume don sanyin da nake ji a jikina gami da runtse idanuna ina jin wani zazzabi mai karfi yana son kamani ina dan rawan dari aciki. Muryan mum naji tana fadin haba mama dama baki da lafiya baki fada min ba aisai a dauka tun yanzu ban iya kula dakene yanzu bari na kawo maki ruwan shayi kisha ko zazzabin zai sauka tunda baki son asibiti kamar daddynku kike. Duk sai naji tausayin hjy Mum din ya kamani lokaci guda don ita din dai me kaunatace gaskiya don tunzuwa gidan ta nuna min so da kauna irin ta jini duk da naji Dada tace min dukkansu zaman gwaggonina suke don jininsu daya da ubana dukansu. Barci barawo ina wanan tunanen yayi awon gaba dani da har bansan dawowanta ba dakin ban falka ba sai tsakan dare kuma naji garau ina yankan zufa a jikina. Kokarin yaye bargon nayi lokacin naji muryan hjy mum dake gefena zaune ta kafa glass din idanu tana karatu tace Ya mama wani abu kike sone ya jikin naki ko yunwa kikejine ta jefo min wanan tambayoyin lokaci guda don haka na rasa wani zan amsa mata sai cewa nayi kewayawa zanyi inyi sallah. Kaita girgiza tana kokarin mikewa tace zaki iya tashine nace naji sauki mum zan iya na samu na mike zaune ina jin jikina wani iri alaman jikin dai ya tabu a ranan. Hanyan fita daga dakin na nufa don fahintar danayi a dakinta nake naji muryata tana fadin ina zaki yanzufa karfi biyu da rabi na dare ki kewaya a nan mana . Alwala na dauro na gabatar da sallalolin dake kaina tun daga la,asar duk da hijjab din Mum din kana na mika kukana ga ubangiji Allah wanda yafi kowa sanin daidai ga bawansa zamana a gidan nan yasa alherine a gareni kamar yadda yan uwa suka tafi suna fada min har hakan yasani kuka a lokacin. Wanda a yanzu ya haifar min da wanan zazzabin da nake ciki komawa nayi na kwanta har lokacin mum na zaune saman gadonta tana karatun Al,kur ani mai girma cikin dan murya. Banyi barci ba nima har zuwa lokacin data gama ta kwanta duk ina jinta sai zuwa asuba barci ya dan saceni saida ta tayar dani nayi sallahn asubahin ranan. A gaskiya zance a dan kwana biyun nan naga canji sosai ga kowa na gidan har hjy malka da yaranta don wuni suke suna shigowa part din hjy mum din suna min ya jiki. Don haka a dan wanan karnin tayi iya kokarinta kamar yadda mijinta ya umurci kowa da baison yaji ko ya gani a garesu kaina don hakane ashe suke kokarin nuna min kulawansu akaina lokacin. Yayin da hjy mum ce da Dada suka zamo sanyin idanuwana a gidan saboda natsuwan da nake samu a wajen mum din tare da kulawa irin wanda mahaifiya zata ba yarta. Don mum ko fita zatayi tare danine saidai idan ni naki fita amma kafanta kafana duk inda zata shiga islamiyan da take zuwa nan nima ta sakamu nida halima bata yarda ta kaimu wanda yaran gidan kezuwa jefi jefi ba sai sunga dama. Cikin hakan zance Alhamdullahi don yanzu gaba daya na manta da zancen gida don nasan ba komawa a gareni na kuma ba kaina shawara gara na hakkura da ida Allah ya ajeni din inyi biyayya kamar yadda suke so a zauna lafiya. Sati biyu da yin hakan daddy ya kaimu wata makarantar kudi don ba karamin fiti akayi da hjy malka ba data nuna bata son akaimu inda yaranta suke tunda tagane gasa hjy mum keson yi da ita wai yasa ta matsa mu dawo garin da zama . Wanan yasa mum taba daddy shawara ya kaimu wani school shima na kudi don nasu baifi namu din ba duk bamu san anyi ba sai murnan hakan mukeyi mukan tunda ba abinda ya damemu sai kewan gida wanda yanzu mun rageshi koshi tunda ga Dada a tare damu. Da mun dawo daga boko zancen islamiya ne don haka ko aikin gida yanzu bako yaushe muke yinsa ba sai weekend da muke gida zamu dan kamawa hjy mum din aikin gida din muyi. Ga kuma kulawa ta musan man daga daddy da muke samu don zai kiramu har yayansa biyu da dai sun dan girmemuna ga shekaru yaji korafin mu zai zabi na zaba dake da muhinmanci yayi muna nikan kullun aka tambayeni zance hjy mum ta saya min ban karban kudin daddy din amma daya gane hakan halinane saiya ban kudin yace saiki kaiwa mum din naki ta kara tayi maki yar gidan mum. ZAINAB IDRIS MAKAWA [1/31, 08:06] Aishatu Aliyu Musa : DUBA MIN BAYA FOKON,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Shi baiwa ko daukaka wani abune dake zuwa daga Allah halittan bawane da aka haifeshi dashi hakan saidai mu yan adam bamu gane hakan. Na fadi hakan ne duba ga yadda na koma cikin dan lokaci kadan dubaga yadda na saki komai na rugumi kaddara sai gashi cikin dan lokaci kadan rayuwata ta canza ga baki daya. Zakice ni din ma haihuwa binnine ban taba zama kauye da muka baro nida iyayyena ba da farko to ba komai araina sai zalla kwakwan karatu both bokon dana mahamadiya dana sa a raina. Bazance ban tunanen iyayyena ba wanan yana min makale a zuciyata dare da rana ina cikin kewansu koda yaushe suna a zuciyana saidai ban nuna damuwa akan hakan. Wanda hakan yasa aka fita zancen nakoma ina bawa kowa mamaki daga karshema aka daina damuwa akan hakan dani tunda anga na sake a gidan. Saboda hjy Malka yasa bana shiga part dinta don bata iya boye bakin cikinta akaina don ma tafi matsa min saboda ban bada kafa irin na Halimatu ba da har zasu dan bugi cikina suji halin da hjy mum ke ciki kan wani abinta. Nima daga baya nagane cewa halimatu din nawa hjy mum din mu zagon kasa tana fadin zancen ta yana fita daga bakinta don da farko hannuka mai sanda mum kanyi muna takance amma kuke wurina bani kaunan abinda zai taba rayuwan ku. Na dauka irin rikon da nake maku kuma zaku rikeni har zuciyar ku ba tare da munafuntata ba idan tayi wanan maganan nakan tsargu da ita nakanyi mamaki don me take yawan fada muna hakane. Da hankali ya danzo min ya karu saina fahinci ida matsalan yake watau dai halimatuce ashe shakuwansu dasu mairo diyan hjy malka da biyu sukeyinsa don wani lokaci zaka sanesu a part din zaune ana yan dararaku a tsakaninsu. Bankan tsaya kulasu zan shige wajen Dada mu dan jima muna hira wanda bai wuce hiran takuran da take ciki ba a nan din dkgidan rashin fita yadda takeyi a gida yanzun kuma bata samu sai abin yake damun ta sosai yanzu. Yau ya kasance asabar don haka nakan dan zauna na wanke kayana tunda safe na hada hardana hjy Mum din idan sun bushe saina goge nakai mata daki yanzun ma haka nayi. Nashiga da salamana tana zaune a bakin gado tayi tagumi da hannayenta biyu yadda ta amsa tun nan nagane a cikin damuwa take lokacin. Kafin matace na bude durowa na saka na nufi wajen kai tsaye na bude na jera kayan har nagama zan fita batace dani komai ba hakan yasa na dan koma satan kallonta don na kara tabbatar da zargin da zuciyana ke mata. Sam bani take kallo ba asalima a yanzu hawayene ke sauka a idanunta hakan yasa naja na tsaya cikin dan rudewa da nuna damuwa agareta. Nake fadin Mum lafiya kuwa naganki hakan lokacin ta dago kai tana fadin ba komai mama jeki abinki kawai ganin hawaye a fuskan nata lokacin da take maganan yasa na tsaya a hankali na taka zuwa gareta ina fadin. Mum ko mun maki laifine bamu sani ba na duka gabanta ina fadin hakan sai naji ta dan sauke ajiyan zuciya tace inma an min laifin bani tunanen dake ciki mama. Nafi kyautata zaton halimace don a yanzu nasan halinku kaf nasan abinda kowan ku zai iya da wanda mutum ba zai iya yi ba a kullun burinki a zaman mu shine kiga farin cikina mama a gidan nan ni shedan hakanne akanki amma halimatu tana yarda ana hada kaida ita wajen cuta min ma,ana dai tana munafuntana a yanzu. Don kusan ince banda siri a sashen nan da zanyi Halima bataje ta
Chapter 21 · 0% Book details