← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 61

Sashe 49

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jaba na dan diba a plate nan na zauna ina tsakura saiga anty Nafisa ta fado dakin. Lah ke kina nan zaune a daki ba zaki je wajen event din naku ba kai na dukar kasa kafin nayi magana mum tace bamu tsara wani event ba don walima kawai. zamuyi a bangaren mu. Haba mum ina tare da yan uwa zatayi komai ko ? No Nafisa kinsan halin yaran nan don Allah barshi a yadda muka tsara zamuyi walima hade dana saukarta shike nan itama idan mijinta nason suyi event idan ya iso saisu tsara abinsu amma barsu can suyi abinsu don Allah mun ta kakabe zancen. Ta danyi shiru kafin ta juya tana fadin Allah kyauta mum don dai kinkine amma ina wajen ai waya isa yai mata wani abin bayan gani wajen a dai bar zancen har mijinta ya iso garin. Mum kina ganin wai hafiz zaizo garin nan ko bakiji irin kwasan rikicin da sukeyi da daddy bane tun shekarajiya kan zance guda. Ban tsamani zai shigo don ko mum yau naji ta kirashi da safe tayi masa kaca kaca ko zaiji yazo ban sani ba dai ni har mamaki yake ban wallahi waima baki san wani abuba mum ? Mum din ta kalleta tayi mata signal da ido ta daina zancen a gabana saita juya tana fadin barin dawo mum yanzu ina sauri sister mum ta hanaki zuwa ko ? Dan murmushi nayi bayan fitan ta mun ta juyo tana fadin nasansu yaran banzane basu da kwabo sai kunje wajen taron nan su nemi su wullakantaki a can gara dai ki zauna gida kawai. Mum nima ba zanje ba don ban ra,ayin wanan event din da zasuyi yau ai yanzu dai na fada mata taje can ta sanar dasu na hanaki duk wani program nasu da zasuyi. Washegari yan katsina suka shigo kusan mota uku na mata bada maza ba wai wasu suna baya tafe ashe yan uwan inna ma sun shigo a ranan su da yan kauyen mahaifin mu baba. Wanan kauyen da muka fara zama a cikinsa suma sunyo gaiya sunzo don sheda aure da za,aimin a lokacin suyi kokari sosai gaskiya yadda suka kashe lokacin su zuwa har kano wurin bukina din. Saidai duk a gidan iyayyena suka sauka basu sauka a gidan daddy din ba don haka ko gidan mu basu huta da jama,a ba don an taru a can din ma. Daddy da kansa ya sauke abinci a can duk dako mahaifina yayi nasa kokarin ya tanadi abinda zasuci har su koma amma duk da hakan saida daddy yayi nasa kokarin. Washegaru mum ta tura akaje akai min jere duk da daddy yai muna komai amma kuma saida tayi nata na fannin uwa a waje an gyara gidan tson kowa ya dawo yana yaba kyawonsa da tsari. Yayin da bangaren mummy sunje su tun saura sati daya buki sunyi nasu gyaran dakin wa diyansu acan garuruwan da za,a kaisu din . Don sun fara tsegumi akan mum wai dama ai sunsan ba zata taba yimin wani abin kwarai a rayuwanta ba tunda bata da alheri bautar dani kawai tayi. Balle ba zata kai min abin kwarai ba ai tunda tasan hafiz zan aura don kawai tana bakin ciki da hassada dashi yana dan mummy haka dai suke ta tseguminsu . Sai gashi sunji cewa mum ta tura an gyara mun daki aka shiga lissafo irin abin arzikin da tayi min mummy sai baki ya mutu kuma ta koma fadin ai dole tayi min hakan. Dama ta rikenine don ganin iyakar mummy din don ta nunawa duniya ita ba kowa bane san nan ai sun san komai duk abinda aka gani daddy ne ya bada kudi a boye akaimin shi son kawai ya farauta muna rai. Niko nace ashe mummy tasan dan nata abin banzane ke nan tunda har take iya zaton daddy ya hada muna dacin hanci don a zauna dashi ko ? Da yamma muna zaune ana hira gida ya cika saiga Dada ita ta saka min lale ta shammaceni banyi aune ba ta zuba min akafa har zuwa sawayena da hannayena tana guda. Wani irin zabura nayi ina hawaye tare da furta ta faru ta kare ke nan na dai tabbata matar hafiz ke nan na fada a zuciyana na mike zuwa babdaki. Kuka nayi sosai kafin nabawa kaina hakkuri na wanke nafito don kada mum ta gane cewa kuka naje nayi saboda nayi alkawarin ban sake yarda inyi kuka kuma kan auren. Nan buki ya fara ga jama,a ko sai zuwa sukeyi daga garuruwa don su sheda kawai su nunawa iyayyena farin cikin ganin wanan lokacin kamar yadda yake a al,adance. Kamar ko wani buki kuma ko wani gida aka hada bukin yayan daki biyu ake samun yan tsegumi da gulmace gulmace wanan ma namun hakan aka samu. Hakan yafi faruwane kuma abangaren mummy din hakane ma a asirce mum taba da girki da za a dinga yo mata daga wani gida ana kawo mata nan gidan kawai saidai aga ana shigowa da manyan kuloli na abinci apart dinta. Sai hakan kuma ya tsonewa mummy ido sai gasu har gaban Alh wai bata yarda da tsarin da mum ta dauko din ba nan daddy yake fadin baki yarda ba sai kije kiyi yadda tayi din mana kema. Ni dai nasan Kubura bata tambayeni kudi wai zatayi girki ba haka kuma nima ban dauki kudi na taimaka mata tayi girkin nan ba ina duk abinda tayi tayine da sunan taimaka muna dai a cikin sha,anin nan . Tunda dani dake keda bukin nan ba dole bane sai kubura tayi wani abin bajinta da har zai tsone maki ido idan kina da tunane mu tayi wa wanan karan ai a nan. Duk da haka mummy bata fahinta ba don bata yarda ba kishi ya rufe mata idanu a lokacin sai cewa tayi dama ai bakinsu hadene gashi ita din dake cewa mum tana da rowa . Itace irin halittan nan ne da komai sai sunci riba dashi kudin ba bata samu bane wajen miji bata dai iya fitarwa ne akashewa jama,a ta zata daddy zaicewa mum a hada a dinga kawowa ko wani part ga nata wautan. Sai daren da za a daura aure hafiz din dasu yaya Addil daya shawo kansa suka iso garin cikin dare sosai bayan mum tayi ta korafin rashin zuwan nasu akan lokaci. Tana cewa rashin zuwan matarsa da wuri yaci mata rai ace tana bukin kanwarsa amma ace wai ba matar Addil a wajen don tana yar rainin wayau. Wanan yasa washegari da sukazo mum din taki tsayawa ta basu lokacinta tana nuna masu fushinta ga hakan da sukayi na basu kyauta mata ba son gaba su gyara. Amma sai gashi itama Aishan wai tayi fushi don mum bata nuna tana da muhinmanci ba a wajen ta ga idon jama,a din haka ta sulale ta fice daga gidan ba tare da kowa ya sani ba. Saida mum tace akirata tana kitchen shine ake fadin ai bata nan a zaton mun ta shiga wani part na gidan ne sai gashi ana fadin anga fita ai tabar gidan. Ita kuma mum nata matsala ke nan daya fara bullo mata shine matar danta bata da mutunci balle kirki don sam bata da tarbiyan bin nagabanta uwar miji da take tankat uwarka ga me tunane amma ita ko gaban dan sai ta nemi ciwa nasa mutunci. Don hakanema gaba daya gidan ba wani mai dogon shiri da ita baya ga gaisuwa da za a tsaya a danyi sama sama don gani take ta girmi wayewan kowa a gidan don haka babu sa,anta take daukankai Sai dai ita a wajenta kuma gani takeyi kawai dai ba,a sontane don hakane bata nemi hanyan gyarawa ba sai iskanci da takeyiwa mutane tana kara bata kanta a zuciyan yan gidan mijin nata. Don ko hakan datayi ba wanda baiji wanan labarin ba kowa na tir da halinta a cikin taron nace kinga bone kowa ya zageki Allah yasa mu gane gaskiya mu gyara ba sai ana son mu zamu kyautatawa uwar miji da yan uwan miji ba halinmu zai muna alkalanci a gidajen auren mu mata. ZAINAB IDRIS MAKAWA [2/28, 06:27] Maman K: DUBA MIN BAYA FOKON,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Duk wanan badakalan da akeyi iyayyena basuce uffan ba duk ko da zagi da cin mutuncin da mummy keyi kamar a gabansu take fadinsa don komai sunaji amma sun taushe zuciyarsu saboda zumunci. Akwai sauran imanin zumuci a lokacin dan uwa na iya bugun gaba da dan uwashi ako wani lokaci ya yanke hukunci akansa ba tare daka daga kai kace don me akayi hakan ba. Duk dadai har duniya ta nade akwai masu imanin gaskiya da biyayya bisa ga tsarin musulunci don sai ince duk yawancin al,adun malam bahaushe kadan ne yake tsarin al,ada duk koyine da addini bahaushe yake abinsa. In banda yanzu da boko ya sauya wasu suke ganin tsarin na farko ba tsari bane akwai tauyewa acikinsa yasa karfin zumunci da bahaushe yake girmamawa ya rage a zukatan mutanen yanzu sosai bisa ga mutanen baya da suka kwanta dama. Allah ubangiji ya jikansu da rahama ya gafarta masu albarkan kalman shahadan da suka rike a bakunansu Allahuma amin. A kwana a tashi hasaran rayuwa inji malam bahaushe buki dai ya karato kowani bangare sai shiri akeyi inda hjy mum gwaggona uwar dakina itama ba,a barta a baya ba wajen shirya yarta da zata kai aure watau ni ke nan. Don ko wani tsimi wani gunba wani hayakin jiki dana tsuguno da siracin irin na shuwa duk nashashi a wajen hjy mum don sai dare yayi kafa ya dauke zata tasani agaba da wa yanan abubuwan tun ina sha ina amai har ya
Chapter 49 · 0% Book details