Sashe 42
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
yawa take hangowa don kamar fin karfi da son kai za,a nuna min da iyayyena take gani duk da tasa suma a bangarensu sunfi tsanar hadin fiye dasu. Ita mace ce bata da karfi ko power da zata tsaya min tace kada ayi hadin nan haka kuma iyayyena suma basu data cewa don Alh shine babba ga mahaifina. Mum lafiya kalman dana jefo mata ke nan na katse mata tunanen ta a lokacin ta nisa da karfi tana sauke ajiyan zuciya tace bari kd dai mama duniya nake tunane wallahi. Jikinane ya danyi sanyi a zatona kan zancen tafiyan ya hafiz din ne data dauko min na shareta abin yake damunta sai mm aji tace akwai Allah ya Allah ka shige muna gaban lamarin nan yazowa kowa da sauki. Na amsa da Amin take fadin sai ki shirya don Nafisa zakibi takaiki ranan Monday din abin ai yazo da sauki tunda ana saka wayewan kai aciki ba irin namu bane da kowa jahilci lokacin bamu ba ba iyayyen namu ba. Part dinsu ya nufa kai tsaye don ya karya yana shiga Dada na zaune suna hira da Anty nafisa ya samu gefe daya ya zauna yana bata rai. Dada sai zolayanshi takeyi yace dama ina son ganin ki muyi magana sai gaki Allah ya hadamu a nan yanzu rage fara,an fuskanta tayi don ganin yadda shima yake cikin damuwa tana kallonshi tace ai gani kamar Allah ya turoni meka samo min fadi muji. Dan furzo da iska yayi daga bakinsa kafin yace Dada akan wanan auren hadin da daddy ke son yai min ne gaakiya Dada kwata kwata banson auren nan kuma yarinyar batayi min ba don ba kalan zabina bace ita. Ita mace har tana da wani bambamcine a wajen namiji ina dai mace macece ya tsuke fuska cikin damuwa don ya kula zaisha wuya koda zai samo kan tsohuwar. Dada nasan ke kadaice zaki fahinci me nake nufi ni sam bani kaunar wanan yariyar koda yan uwantaka balle da sunan aure kinga yin aure tsakanin mu hakan kuntatawane ga gaba dayan mu sai hakan ya kara haifar da matsala har yashafi wanda ba,a zata ba.. Tunda ya fara maganan Dada ta bude baki take masa wani kallon na mamaki wanda shi bai iya tantance ko nameye alokacin. Haka mummy ma data fito daki da manzafi data daukowa Dada daga daki dama shi Dada din tazo nema a wajensu ta zauna itama kallon mamaki tabi dan nata dashi lokacin don sun riga dasun aje magana dashi don mafita akan zancen. Kai ashe rashin hankalin naka yakai haka ban sani ba yar uwar haihuwan naka kake fadi a gabana baka kauna koda zumunci balle da aure ? To ka fara zuwa wurin ubanka daya hada zancen a tsakanin ku kafin kazo wurina watau ni gani tsohuwar banza mai yukan yanke zumunci bari kazo wajena ka laba ayi yankar kauna ko ? Ke Dada wai bakya ganewane shifa so wani abune kada ku tauye min rayuwata mana don Allah zaku hada baki ku cinna min wanan mahaukaciyar yarinyar in kaita ina don Allah ? Inda ubanka yakai uwarka nace inda ubanka yakai uwarka Dada tafada a hasale cikin mikewa tana haki kamar zata dokeshi daga inda hjy malka take tsaye ta kwala masa kira tace hafiz bakaji ko zan saba maka idan baka fita part din nan ba yanzu. Kallon mummy din yayi kafin ya juya a kasalance wurin Dada din yace na dauka zaki taimaka min ki rabani da wanan auren alkakan da daddy keson yi min she duk bakin ku daya ban sani anywhere kuyi karku fasa din ai . M ummy ce ta karaso acikin masifa agareshi tana rantsuwa idan bai fice daga part din ba zata saba mashi rai fiye da tsanmaninsa. Lokacin Anty Nafisa ta dago kai ta kalleshi tace Hafiz wai bada kai mummy ke magana ba ka bari a lalaba zancen nan mana tunda ku duka bakwason junan ku. Wani kallo yayiwa yar uwartasa tace yes kamar yadda baka son hadin nan ko ita sister na tabbatar da bata so don ko bashiri a tsakanin ku . Shine daidai idan anyi auren sai suje can su shirya a tsakanin su tunda sunfi kusa Dada ta fada cikin daga murya har ya juya ya fara tafiya jin hakan yasashi ya dan dakata yana mai juyowa ya nuna Dada din da hannunsa. To indai har hakane babu wanda ya isa kaf ya fasa wanan auren acikin uban nan ku muddin ina da raina ya nunata yace aisai ki zauna da ita ki jika kisha tunda kince hakan. Shege ka fasa tunda kace haka in maka na mahaukata wallahi hafizu idan kaga an fasa wanan auren tsakaninka da Abu tabbatar bana raye a doron kasa ta karasa zancen a cikin bacin rai. Anty Nafisa ta mike tana fadin saika fita tunda ka bata komai dama haka kakeso ai Dada ce zaka sama ko daddy dayayi ma wanan hadin meye na Dada a cikin zancen nan. Kai ya girgiza a cikin yakaici yana fita daga falon yakai iya kololowan tashin hankali don yanzu ya tabbatar da wanan auren da daddy ke ikirarin ya zaba mashu mata yar mutunci yar albarka ba fashi sai anyisa. Idan gaskiyane meyasa ba aiwa ya Addil auren dole bashi saishi da aka raina za a kakaba masa wanan kucakar yarinya da sunan aure wai fa zeey a matsayin matarsa. ZAINAB IDRIS MAKAWA [2/21, 14:52] Maman K: DUBA MIN BAYA FOKON,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.