← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 61

Sashe 7

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ZAINAB IDRIS MAKAWA [1/17, 21:35] Aishatu Aliyu Musa : DUBA MIN BAYA FAKON,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE AGAREK SHI HAKKI, BA ABIN WASA BANE , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. A zatona sun bar garin don washe garin lahadi ko kofa ban taka ba har islamiya banje ba don mun tsaya wanki da kitso da sai ranan lahadi mukeyi don inna ta camfa kamar yadda yake ga addini. Bata wanki ko kitso ko tsifan kai ko yankar kumba ko sharama dole dai akeyinsa don jin da tayi malamai na fadin cewa ba a son mutum yayi komai daya shafi rayuwa a wanan ranan idan baya zama dole ba. Wanda rashin sani da kuma akidan nasara yasa a yanzu mun take hakan muna aiwatar da abubuwan mu kai tsaye tunma daurin aure a yanzu harda wanda ba aikin gwaunati yakeyin ba sun mayar dashi wanan ranan ta asabar sabanin jumma da kakannin mu suka fiyi a da ayanzu a sabar din akeyinsa. Sai yan tsirarune da suke da fatawan hakan akai suke zaban kyawawan rana da Annabin ya koyar damu suke abunuwa a yadda addini ya koyar damu yinsa din Allah yasa mu dace Amin. Safiyan Monday mun fito zamu school daidai gaban gidan nasu na hangoshi a tsaye gaban wata jar mota kirar jeep da a lokacin bansan sunnanta ba ya jingina jiki da bayan motar yana tsaye. Jikinshi yana saye da koriyar riga ta maza da akaiwa rubutu da manyan haruffa an rubuta VERSECE sai yar wandon maza fari mai aljihauya da yawa manya da ake kira cryzy ya dan wuce gwiwa har hakan ya baina santala santalan fararen kafafunshi waje da gashi ya dan rufe ga hannayensa saye da wasu zubba da biyu da suka karawa hannun nasa amarshi. Ganin hakan da yake wanda kallo daya nayiwa yanayinsa na dukar da kaina kasa da sauri don kada na kwashi zunubi garin kallon kwam dinsa don nasan hakan ne zamana da yan matan gidan namu da nakanji kallo daya sun haddace abinda ke jikin mutum sin fada gashi nima a yanzu na iya hakan. Magana suke da wani baban mu karami dashima muke kiransa da baba karami amma yanayinsa kamar yana sakar muna murmushine don mu din ya kurawa idanunsa muna tafe. Sai naga ya juye min kamar mutanen kasan su inna da yan cikin tv da nake gani yanzu masu rawa da waka a wasanninsu din nan. Ina kwananku nayi masu cikin dan rusinnawa da muka saba dashi tun a kauye idan zamu gaida mutum iya abinda na iya furtawa ke nan garesu sai naji muryan baba karami yana fadin yan buko har zaku tafi ke nan da safen nan ? Ai gara suyi sammako zaifi masu abinda naji ya fada ke nan da hausa badon haka ba sai ince ko baijin hausane din zama a kasan turawan da ake fadin sunayi yanzu. Kuzo ku karba kalman daya fito bakinsa ke nan sai naji kunya ya lulubeni gashi muna da tarbiyan cewa a,a ga mutum farat daya idan ya nufemu da alherin abinda yake ci idan mun riskeshi. Toga wanan babu komai a hannusa ya kumace muzo mu karba yaya ke nan zanyi jin hakan yasa naja na tsaya ina kada kai alaman a,a sai baba karamine yace dani kuzo mana ana magana daku. Tuni naji kunya ya lulubeni lokaci guda a wajen yayin dana dan sada kaina kasa cikin kunya na tako zuwa garesu din ina rike da hannun kanne na dake rike dani har zuwa wajensu din. A daidai lokacin ya tura hannu cikin aljihun wandonshi ya fito da kudivyan dari biyar biyar guda uku ya miko min da sauri na sake girgiza kai ina fadin mungode suyi yawa baba ya bamu hamsin hamsin musai abinci muci. Kai amma yar nan da wani zance kike ana batun dari biyar meya kawo zancen wani hamsin can kuma karbi don Allah kin tsaya kinawa mutane shirmen banza. Shiko murmushi yayi yana fadin kinga kanwata karba ku kara ai harda na gobe na baku kinga baba ya huta baku gobe ke nan idan ran mu yakai koba haka ba ? Jin hakan yasa na dan rusunna na mika hannu a cikin ladabi na karbi kudin a hannunsa tare da furta mungode na juya muka tafi har kafana yana hardewa waje daya. Kwata kwata raina baiso karban wanan kudin ba gaskiya don inba Allah ya gyara ba nasan sai munsha fada a gida tundai ni har mukaje muka dawo suna cikin littafin dana sakasu a ciki. Sam na manta da zancen su saida yamma da baba ya dawo gida sune zaune da inna suna hira naji yana zancen kudi abin ya fado min a rai daga inda nake tsaye nace lah . Jin hakan yasa suka kallo inda nake duke ina wankin uniform din mu na school nace na manta in fada maki inna dazun da safe da zamu tafi school wanan yayan din da sukazo ya bamu kudi wai mu kashe a school shine na aje sai yanzu na tuna dasu na tsame hannu na wanke na nufi daki na dauko littafin dana adana kudin a cikinsa banko tsaya kidayawa ba don a zatona kwara ukune ya bamu kowa guda guda ashe ba haka bane. Don ina bude littafin kudin suka watso kasa shar sabbi dasu mikaku sukai fale fale a kasa hakan yasa na fara sanin sunfi kwara uku ashe yadda nake zato. Muryan innace ke fadin waya baku kudi haka masu yawa kika karbo ina jin hakan na dago da sauri na kallo inda inna din take zaune kafin naji baba yace dakata muji ai wanda ya bata. Tunda har bata kashe ko kwabo a ciki ba aiba zamu fara mata fada ba sai munji ba,asi akai na hada kudin daya watse na dago ina fadin dazun ne da safe da zamu school mukaga wanan da kace su yayan mune faein nan dogo tsaye da baba karami suna magana. Shine da muka gaidasu yace muzo mu karba muyi breakfast dashi nace ya barshi ka bamu hamsin hamsin sai baba karami ya kama min fada wai ai shima yayan mune don haka mu karba shine na aje na manta da muka dawo in nuna makine inna . Amma aina hanaki karban abin mutane ko haba Rukkaiyatu kibi zancen nan a sannu itama ta sani ai na hanata hakan amma ai kinji tace babansu karami yasa ta karba don haka ai mata uzuri . Da alaman inna bata gamsu da hakan da baba yace ba son yadda naga ranta ya baci har fuskanta ya nuna hakan a fili sai naji baba yace dani aje kudin kije abinki nagane ko waye mai sunan malam ne Aliyu ko tunda kince fari dogo shine ma dai fari sosai a cikinsu ai. Bayan nabada baya baba ya rage sautin muryanshi yana cewa ina din ki dinga bin yarinyar nan a sannu tasan abinda takeyi ai tunda kikaga duk da abin kwalam a school din baisa ta kashe ko kwandala a cikin kudin nan ba gashi kuma a karshe ta kawo muna duk dai bamu sani ba ai tana amfani da zancen mu ke nan a kanta. Malam tsoron zamanin nan nake ji a kauyema an yaudari yaro da kudi balle nan da yake birni abin ne sai ana tsawatawa haka ai nasani amma ki sani Rukkaiya insha Allahu Allah zai kare min zuriata dana musulmai daga masheranta. Ban taba aikata zina a rayuwanta ba ko makamancin haka in Allah ya yarda Allah zai kare min zuriata da yardan sa insha Allahu amma fadan yana da kyau garesu sai dai a hada da nasiha. Ai kinji hankali bai tashi ba don nasan yaron natsetsene baiyi hakan garesu da wani manufa ba sai da niyar alheri irin na yan uwantaka a tsakanin su dan uwatane donshi na kyale aida nine zan fara fadan karban da tayi din. A haka rayuwa ke tafiya damu a sannu a hankali ayanzu nasan duk wani dan uwa na kusa dana nesa har matan babanin mu maza dake zaune wani gari izuwa yanzu dai nasansu gwargwado sai wanda baizo ba na gansane ban sani ba. Gashi shakuwan mu da Dada yasa suma din sun sani sosai don yanzu mun shaku da ita fiye da dacan da mukazo rashin sabo yana sa ina mata make make narashin sabo a tsakanin mu. Saidai cikin hikima da nuna so da kauna irin na tsofi har Dada ta saye min zuciyana dagani har iyayyena a yanzu banda wani zance sai nata a bakina itama kusan hakan. Don duk cikin jikoki tafi yarda dani da kuma kamar sakani a rai bisa ga kowa wanda nasan shakuwan dake tsakanin mune ya kawo hakan. Hakan yasa da tafiya kano ya kama Dada ta bukaci baba ya barni mu taka mata baya nida halimatu jikinta dake wajenta baba baiki ba don dama yana da burin hakan nakai ziyara ga dan uwansa dake masa korafin yana masu rowan mu bai bari muna shiga dangi a san mu. Shiri sosai Dada takeyi na tafiyan mu din don a bakinta nake jin cewa buki za,ayi nan da sati biyu a gidan baban nanu dake can zaune kano din kusan duk dangi zasuzo wanan bukin don shine karo na farko da zai aurar da yarsa mace don maza basuyi aure ba saboda karatu. Itama yar nasa da ake kira da anty baby naji Dada tace ta tsaya karatune yasa ba ai mata aure da wuri ba sai yanzu data kammala zatayi aure. Mukan a bangaren mu ba wani shiri illa zaban yan tufafin mu mu goge sai kuma kitso da kumshi wanda inna da kanta ta zauna ta dandasa muna kitso har siifa a kafafun mu nida halimatu din. Mota sukutum baba na kano ya aiko da za a dauki Dada din dashi don haka
Chapter 7 · 0% Book details