Sashe 13
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ehh Dada halimatu wuri ta samu tahaye gado ta kwanta. Ke kam anyi mashiririciyar yarinya duk wahalan ki kin kai na yar uwarkine da suka mayar kamar boyarsu ni inkin debe Kubura sai ince duk ta bar masu ko kawarda kara a gidan nan. A,a Dada aiko aikin ta yaja muna alheri gashi har nima da ban masu komai ba nakai ga kala ukku masu kyau da tsada kaya masu kyau ta samo muna fa da batayi ba ina zama zai samo muna wanan alherin kuma ? Ke arr ja,iri dayi banzane ke kiyi mana ko duniya da kayan cikinta zasu bata ba kumce ba na hana wanan bakin aikin da batazo wazaiyi masu shi ? Dada ki bar halimatu kara zugaki fa takeyi tace aina fahinta basu dai son suga bakin mutum yayi shiru ke dai yar albarka mikon min tuwo naci tun dazun nake son in bude naga me suka kawo min koda yake kuburace a kitchen din banda matsala yau da bakin cimarsu. Mata ki zauna kiyi girkin kwarai ba zata tsaya ba yau ko wuni gidan nan marka batayi ba inama har yanzun bata dawo ba wai suna wajen hada kaya can gidan da za akai yarta. Banda lalacewan zamani ina uwa ina zuwa kallon jerem yarta kuma kisan zamani yaci baya a yanzu kunya ya fita idon mutane ni wanan abin kunya ina zan iyashi don Allah ? Da dane ai tana gida ta saka yarta gaba tana kara mata huduba kan zaman aure amma kaiya haka zata dunkulata ta kaita solai solai kamar rukumi da kaya sai karyan arziki kawai ina aure zaiyi karko a yanzu don Allah. Toke Dada mu ina ruwan mu da wanan zancen ki samesu mana ki fada masu kinzo nan kin tasamu gaba kina zuga fada kamar mu zamu hanata hakan. Ban iya fadan ne kome ta fada a hasale wanda hakan yasa na tsoma masu baki nace a,a Dada don Allah dai kyale halimatu ba komai ne zakiga sunayi kice sai kin maganta ba don Allah ki kyalesu kila haka al,adan garin yake. Tace kuma fa yar nan shiyasa nake sonki dan halin manya iyakata ko idon don kinji dazun mara kunyar yar nan ta fara zancen nazo ina takurawa rayuwansu ai. Ki kyalesu Dada a rabu lafiya tunda haka suke abinsu kinga sai a zauna lafiya inma tayi maganan bari zasuyi halan wahal da kanta kawai zatayi. Waini kike fadawa hakan to kaf dunsu gidan suyi kadan duk iya shegensu kyalesu nakeyi bani hauhuwan da wata tazo daga baya ta nuna min iko a kansa. Mikewa nayi na dauko kayan abincin na dire a gabanta ina budewa kamshin man shanu ya bure dakin lokaci guda jin hakan yasa ta kallo miyan tana kura mai idanu. Tuwon shimkafene miyar kuka da tantakwashi yaji kayan yaji gwanin ban sha,awa sai kamshi ke tashi na kara jawo plate gabanta ina fadin Dada biyo za a bude maki ? Fara bude min gudan ta fada tana shafa wai addua a jikinta bayan ta gama yanka masifa yanzu na ba gaira ba dalili kan abinda bai shafota ba a daidai lokacin kuma wanan hjy ta shigo dakin. Tan fadin hjy kin ganmu sai yanzu yau tun safe dana fita ban samu kaina ba mutanene yanzu basu sa gaskiya ko kadan mun bashi kudin kayan nan da dadewa sai jiya da mukaje kwasa yake son ya kawo muna wani zance kuma. Sannu da zuwa mama na fada tare da gaida ita ta da mika hannu tana fadin yauwa yan matan hjy kuna nan kuna fama da rigiman tsohuwa ko ? Ta kalli abuncin tana fadin yauwa ankawo maki abinci ko dama na damu wallahi na barku tun safe to ai dadin mutum biyu din ke nan a gida in guda bata nan daya na nan sai kiga gida ya rayu yadda akeso. Jin hakan batace komai ba sai cewa da tayi ke Nafisa yau tana ta yabon ki kin mata aiki sosai kun shirya kayata nikan ina naga lokacin wanan yanzu. Muryan babane shima ya shigo dakin nan muka zube muna gaidashi din har halima dake saman gadon ta sauko yake fadin ashe kina nan kina cin abinci yanzu nake maganan ki shigowa na kenan daga kasuwa. An dawo lafiya ko Allah yayi albarka abinda ake nema Allah ya baku ya amsa da amin lokacin hjy ta juya tabar dakin ya kai zaune gefen gado ganin hakan yasa da sauri namike zan fice daga dakin. Muryanshi naji yana dakatar dani ta hanyar fadin dawo ki zauna abinki ina kuma zaki mamana ba a binci zakuci bane ? Dada tace wanan nawane nasu nacan gun uwarsu ai aini kubura ta kyauta min datayi min tuwon nan amma wanan hanjin da matarka ta dinga tura min kwana biyu ai saiya kaini asibiti ba shiri. Kallon juna mukayi da halima muna kumshe dariyan mu ya dade a dakin yanawa mahaifiyarshi bayani kan bukin anan muke jin cewa ai mai mata zata aura ashe . Da sauri Dada din tace aikaji ita kuma gun mai mata ta kare sunki auren hadi da zuria suka gada tun iyayye da kakani a nan kuma yanzu ta fada. Aina fada mata tun farko daga ita harshi babangida din tunda sunki hadin da mukai masu yanzu banda korafi daga baya sai Dada din tace Allah dai ya gyara kundai bi ra,ayin diyanku kada ransu ya baci a nan . Amma banzaci hakan ba gareku don ban taba tunanen wanan zamanin zaizo ya sameni da raina ba Allah ya gyara yace ya dan dukar dakai. Muma dakin shiru mukayi kamar ruwa yaci kafin Dada tace dashi jeka huta da iyalin ka Allah ya bamu alheri ya mike da kyar da alaman wanan maganan ya dan tabashi lokacin. Yana fita nace ci abincin Dada kar yayi sanyi tace to yar nan ke dai ta jawo abincin ta faraci halimace son jan magana ta sauko daga saman gadon zuwa kwabon abincin Dada ta tsami nama daya ta mike da sauri tana dariya. Dada din tace ja,ira baki jin bakina tunda mai kaunata ta hanani yawan magana nace haka shine daidai ai Dada dinga sawa kowa ido wata rana zasu tunaki. Ashe gaskiyane wasu yaran zuciyan manya ake dora masu ashekarun nan naki kike wanan maganan tankar yar shekara hamsin gareni Abbulle gaskiya ba karamin tarbiya da hangen nesa iyayyanki suka baku ba . Da duk uwan zamaninan zasu diga lurar da diyansu alkibilan alheri da har yanzu duniya tana kwance tana barci yadda aka santa a baya amma kayya a yanzu mun aro wani akida mun yafawa kan mu na bata da sunan boko. Naman ta dauko ta miko min na girgiza kai ina fadin a,a muma ansaka muna munci Dada wanan rabonkine ai wanda naci ma gashi ya lake min a hakori yana damuna yanzu. Yarinya mai dabara karna matsa maki ki karba kikace hakan sai na dukar da kai ina dariya adaidai lokacin wanan karamar tasu data dan girme muna tashigo dakin babu ko sallama da waya makale a kunnenta tana fadin gani dakin ai nashigo. Duk muka bita da kallo cikin mamaki wanan shigowan nata haka babu ko sallama itako sai cewa da tayi ehh gata zaune ai OK sai kawai ta miko min wayan dake hannuta din. Ban karba ba sai dago kai da nayi na kalleta a cikin mamaki kafin na mika hannu na karbi wayan daga hannunta bayan tace a cikin tsawa ki karba mana sisterce ke son magana dake. Na karba na kara a kunne na naji tana fadin sister ki shiga dakina cikin wanan jakkar da muka saka less din nan wanda nace zankai dinki ki dauko min gani kofan gida ki kawo min amma ki sak a leda fa. Nace to anty ina mikewa namikawa mai waya abinta naji Dada na fadin wane kuma nace amaryance ke magana tace na dauko mata wasu kaya a dakintane. Shine wanan ta shigo muna daki haka kimkau kamar me shaga coci bako sallama kina faman wani guntaci kamar gaban baya. Wai dani kike Dada ta juyo tana fadan hakan baisa ta tsaya ba ta fice daga dakin kai tsaye nabi bayanta nima zuwa dakin Nafisa din inda ta aikeni . Zakice ba dakin da muka gyara dazun bane yana kamshi kan dakin amma ga kayan da tayi amfani dasu a wanan yinin ta cire watse a dakin ko ina nayi mamakin hakan taya mutum zai debe tufafin amfanin shi ya watsar kuma ? Nidai na dauko abinda tace din nafito bayan na dauki wani leda danagani saman kujera na saka aciki har na dan gwauta dakin sai kuma wani zuciya ya ban shawaran nasawa dakin key don kare mutuncina a gidan. Hakan nayi nasameta a wajen saidai ban ganta wajen ba nan na tsaya dan dube dube ina neman inda take din naga an sako min wutan mota anyi horn saina doshi wajen don ina ganin yadda yan mata ke hira a mota unguwar mu don haka yanzu nasan wanan don tun ina mamakin hakan har na dmotar. Dan nisa dasu na tsaya kadan sai naga an sauke glass din motan muryanta naji tana fadin ya kika tsaya can kuma miko min mana ta fada daga cikin motar. Hakan yasa nataka zuwa bakin motar ina mika mata cikin ladabi kallo daya nayi masu na kawar da idona don yadda suke zaune din a motar ban taba ganin wasu mahaluki a hakan ba. Yauwa yar kanwata shi kika dauko ko nace ehh anty ki duba ki gani ko shi din ne tana kokarin bude ledan yayin da kamshin su duk ya cika min hancina a wajen. Muryan mutumin naji yana fadin wanance bakuwar bakatsiniyar tamu ashema yarinyace karama haka take da kwazon manya amaryata ta fada min kin mata aiki sosai yau dole in maki wani abu nima. Yana kokarin tura hannunshi daya cire cikin jikinta cikin aljihunshi ya ciro kudi dabai tsaya kirgawa ba yan dari biyar biyar ya miko minsu yana fadin ai tunda kikeson matana nima ina sonki dole na yabawa kwazom ki. Kallon kudin da yake miko min nayi na girgiza kai alaman a,a yace dakyau bakatsiniya kunya gareku badai tsoro ba ki karba aike kanwar muce ko nayi maki kama da dan yankan kaine