Sashe 32
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mashi na shigo falon tambayan mum ko kwai nawa zan dafawa ya Nasir din. A falon na samesu da ya Addel shima yana fadan ba zai iya cin wanan faten da mum tayi ba da daren nan sai gani mum tace ga mama nan saita dafa maku abinda take dafawa Nasir tare dakai ai. Me take dafa mai ya tambaya yana kallon mum din tace ina zan sani ai gata wai me kike dafawa Nasir ne ta kalloni tana tambayana nace indomei da kwai mum tace shi yafi wanan faten nawa kama ciki ke nan ? Kwai nawa zan saka mashi mum na tambaya daga bayana naji an bani amsa da hudu muryan ya Nasir ke fadan hakan gareni na dan juya ina kallonsa yayinda mum ke fadin tunda kai kadaine sai a dafama hudun ai. Draman su bai karewa da Nasir din hakan yasa na juya da niyar komawa kitchen din naji mum na fadin shi baki tambayesa ko kwai nawa zaki saka mai ba nace nasani biyune. Hakan yasa ya lumshe idanunsa lokacin da mum ke fadin watau har kinsan ko nawa yakecishi nace nasani mana mum naahige na barsu ban fito ba saida naga hada masu komai na kawo masu abincin a gabansu na dire nan na barsu ya Nasir yana zuba masu santi yanaci. Ban fito ba saida safe nayi duk yan aiyukan da zanyi na koma na kwanta don akwai gajiya a jiki barci na samu sosai nayi lokacin kafin in tashi inyi wanka nafito da zumar in karya don kunun gyada mukayi kuma ina sonsa sosai don haka mum take munashi don itama tana so. Haka kawai ganinsu yasa girjina bugawa duk da baiko kulani amma masifan tsoronsa nake ji tunda na fahinci baida mutunci ko kadan a fuskanshi. Masangalin kujera kawai na dafa nace ina kwanan ku wanda jin hakan yasa suka juyo kamar kullun wanan kallom wullakancin nasa ya jefo min sabanin yan uwansa da suka amsa min a cikin mutunci kamar yadda muka saba. Ai gara da kika fito ki taimaka ki dafa muna wani abu mu hada da kunun gyadan nan zamubi hanya dan anjima kadan don muje da nauyi ya Nasir ya fada. Saidai kai nikan ba zan tsaya cin jagwalgwale ba in bi hanya cikina ya rude ina tsayawa kai wanan yarinyar ta iya girki harda na indiyawa sarkin barkwanci ya Nasir ya fada yana dan dariya. Zakace shi ba ciki daya suka fito da ya Addel ba saboda yawan barkwancinsa ga mutum don hakanema nafi sakewa dashi kaf inkin debe anty Nafisava cikin yaran gidan duk ko da dadewan da na danyi a gidan yanzu dasu. Kitchen din na nufa don in duba abu mai sauki naji wanan ya Hafiz na fasin me zata dafama ta wuce baka fada mata bafa kada tayo muna jagwalgwale don Allah. Aiba don ka zanyi ba don dan uwana zan dafa amsan yazo min a takaice kuma na fada kowa naji ni kaina amsam yazo min ne a hasale don rainawa mutane wayau da yakeyi. Kanshi kawai ya girgiza cikon wayencewa ya kuta nashige yake fasin mum wata rana saina karyawa yar nan taki kafa tana wasa dani wallahi ya Nasir yace wayaga ball ke nan. Abinci lafiyayye nadafo masu kuma suka zauna sukaci harshi miskilin da suke faman cika wasu takardu a part din mum din wanda nasam shiya kawoshi part din dama. Daki na samu mum kwance na zauna a kusa da ita muna hira take ja min kunne kan na kiyayyeshi don ba hankali ko kunya ke garesu ba insun tashi tsiyarsu. Haka dai zaman ke tafiya a gidan muka koma hutu don ya kare munsha dogon hutu a lokacin daga komawa aji shidda zan shiga nida Halimatu sai kuma aka samu akasi sunan halimatu ya fito cikin yan repeating dole saita maimaita shekara kuma. Aikuwa nasha zunde a gidan mu don sheri suka laka min cewa wai ina hurda da malamai a asirce yasa suke passing dina ko wani jerabawa son sunga ina da kyau. Ita mummy ce wanan karon ta kashe wanan zancen kafin ya fito fili amma duk da hakan saida zancen ya dawo kunnen mu ranan kuwa hjy mum tayi fada saida anty Nafisa tace ai mummy tayi masu fada sosai kan hakan. Don agaskiya mum tayi niyar kai zancen wurin daddy amma jin hakan yasa ta kyale zancen gashi kowa ya gani zai yaba sai cewa ake nayi kokari na Wanda hakan yake karaba halimatun haushi sosai don har kyauta daddy yayi min don cin na farko da nayi ya sayo min lace mai kyau da takalma har da hand bag na yan gayu sai murna nakeyi. Nasan yayi hakan ne don yan uwana suji haushi suyi kokari don tare zamu zauna dasu yanzu su kara zana jerabawan nasu a school din mu din. ZAINAB IDRIS MAKAWA [2/14, 11:14] Aishatu Aliyu Musa : DUBA MIN BAYA FOKON,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Hjy mummy da mamaki ta dawo gidan tana barazana wai bata yarda yarta ya haihu ba watakila an mata hakan ne donvta dawo daga unguwar. Wanan yasa tun a mota da daddy ya kirata take yankan sababi dashi ya za,ace ta haihu kuma wai agida abu kamar almara don haka ita bata yarda ba har saida ta shigo gidan . Ta fara ganin alaman gaskiya don jin hayaniya yan gidan da ake a ciki murna kamar yadda ake taya mai haihuwa da wanda ya shafa fari ciki a kasan hausa. Nan ta shigo tana fadin wai dagaskene baby ta haihu din abinda ta shigo tana fadawa mutane ke nan a dakin cikin fada tana shigowa falon dake cike da yan gida suna murna da haihuwan don yanzu gidan ya koma gidan jama,a cike yake da mutane don daddy Enugu daya dawo da nasa iyalin. Kallon mamaki kowa ke mata don basu tsamaci hakan gareta ba farin ciki da jin dadi suka zata a wajenta don Allah ya sauke yarta lafiya a gida kuma. Mamakinsu bai kare ba saida ta furta wanan ai gangancine dole a dauketa akaisu asibiti daga ita har abinda ta haifa din a duba lafiyansu a can. Lalai Marka baki da imani kuwa ina wanan zance mara dadi haka ya fito a bakinki kuma ga yar ki ana farun ciki zakizo da zancen banza yanzu kuma ? Wani asibiti kuma kike zance yanzu Allah ya rabata da talan munta gaban mutane ta haihu daki daga ita sai kanwarta data dafa mata baya lafiya yanzu kizo muna da zancen banza. Don kudi yaiwa mutane yawa haka kuma kice aje asibiti yanzu don hauka ai wanan ya zama kuwa bayan halri ke nan kuma ai saida aka haihu za ayi zancen asibiti. Wani kallo mai alaman shock tayiwa rasarkuwar nasu Dada tana fadin wace kanwarta wai badai mama ba don yanzu dole itama da mama take kirana agidan ko uwar masu gida tun ranan da Dada taci mata mutunci a gaban mu kanta kirani da Abuwa. Wa kuwa inba Abuwa ba itace dai me wanan karfin halin ita ta karbi haihuwar yar uwan,nata sai kiran mu kawai sukayi daga baya bayan sun gama zugansu a dakin su kadai. Wai baby tana da hankali kuwa Maamah ce zata kira ta kama mata haihu mama dabata ko san inda ke mata ciwo ba tunkun ya Malka ai farin ciki dai zakiyi tunda ta sauka lafiya Allah ya tsare gaba kuma matan daddy enugu uwargidan ta fada daga inda suke tsaye cirko cirko suna kallonta cikin mamaki don basu zaci hakaba gareta. Fitowan hjy mum da jariri a hannu tana fadin ku shiga mungama tana ciki yasa mummy din juyawa tana kallonta mairoce ta mika hannu da sauri tana fadin hjy mum kawo babyn mu gani me aka samu. Tace gashi kun samu baby boy mai kama da ubansa sak har dan dingon nan na habib yaron nan saida ya dauko don kara ta fada tana dan dariya fuuuu mummy ta wuceta ba tare data shiga ba sai sauran suka bita a baya. Nikan wajen su mairon muka tsaya munawa baby din kallon kwam da shawa,awa tare da jin dadin haihuwar yar uwar tamu din a lokacin don abin farin ciki ya samemu. Kunya nakeji naji ance wai ai zainab ce ta tsayawa anty Nafisa ta haihu don ko kowa haka yake fadi a gida ta haihu ita da maamah ai maamahce ta karbi haihuwan. Muna part din har yamma na tsaya kara gyara dakin da fiddo mata da kayan da zasuyi amfani dashi ita da jaririnta su daddy suka shigo su ukkunsu dashi da mahaifina da daddy Enugu. A falo muka tsaya suna fadin ina abokin namu ance mun samu abokin kokuwa mai karfi jin muryansu yasamu fitowa ko maijegon fitowa tayi tare damu don ta gaidasu din. Muryan mommy data rigamu fitowa tana fadin gashifa mai karfi dashi haka tayi kasadan haihuwa a gida su kuma suka biye mata bayan kowa yasan yanzu yadda haihuwa yake tattare da hatsari gashi kuma na fari. Sai naji daddy din na fadin Allah ya kawo muna sauki an haihu a gida shine saukin aida ake fata daddy enugu ya fada yan kuda na kwana inji manya yana karban yaron daga hannun Asiya. Mr Enugu gasadane hakan ai daga ita sai maamah suka haihu don maamahce doctor tayi karban haihuwan don wauta ta fada rai bace. Daddy dasai murmushi yakeyi yace interesting ashe zan samu likita mace a gidana ke nan gaba kinyi kokari sosai mamana haka ake son karfin hali ga mutum ya koya ya iya Allah ya raya ya fada yana karban yaron a karshe shima. Hjy mommy bataso jin hakan ba ta juya ta shige tana jininin abin babane ya kallo inda nake yace ku bani dabino da