← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 61

Sashe 58

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hafiz kana tunanen gaba kuwa kashe mummy kakeson yi da bakin cikin ka kome an maka auren nan na gida don ka natsu ka dawo hankalinka amma ba a huta ba duniyace fa hafiz tsawo da fadi gareta hafiz. Komai shakiyancin mutum ba zai iya ganin iyakarta ba saidai taga nasa hafiz sai yaushe ne zaka natsu kaiwa kanka fada akan irin halaiyan nan mm akane hafiz ? Yanzu ka duba don Allah wani mai mutuncine zai shigo gidan nan haka ya kalleka da daraja ko ita din tayi daraja a idon mutane an samu gidan ku a haka ? Saidai ita matarka da yanzu ya zamo mata dole dole kuma tayi hakkuri dakai tunda kaddaran aure ya hada duk shaye shayen baban boy bai taba yinsa gabana ba asalima bansan yanayi ba sai bayan rabuwan mu nake jin hakan amma waya sani kaga koni matarsa bansan da yanayi ba sai a bakin abokin iskancin nasa yanzu nake ji. Ki bar hadani da wanan kucakar yarinyar da sunan matana a gidan nan wanan fitsarariyar kucakan zaki kira da matana ? Au matar waye a yanzu in ba naka ba kana da sauran ja ke nan ashe har yanzu baka fahinci manufar daddy na hadaka aure da yar uwarka ba to bari in warware maka idan zaka fahinta. Jiya daka dawo a mayenka ka fada min idan wata kake aure ba ita ba idan iyayyenta basu ji wanan haukan dakai mata ba jiyan nan amma ita gata ta shige daki tana hadiyan bakin cikinka. Yadda kake ganin an manna maka ita itama din hakan take gani tsaban biyayya ga iyayyene kawai kaganta a nan din zaune dakai wani kallo ya watsa min daga inda yake zaune din. Tace kwarai kuwa don a rufawa juna asiri daddy ya baka wace yake ganin zata iya hakkuri dakai a cikin dangin ko dangin aiba kowane zai iya yin hakan ba. Enough don Allah kina fadin haka saita dauka ita din wata tsiyace ai nifa ban kaunar yarinyar nan a rayuwata don ku sani. Anji a yanzu baka kaunarta itama bata kaunar ka ai amma yadda tayi hakkuri ta zauna kaima ka danne duk abinda kakeji game da ita a zuciyar ka yanzu ku zauna lafiya kada kuba iyayyen mu kunya. Keda kike ta zncen iyayye su zo su zauna da ita mana kosu ba wani a cikin dangi tunda bani kadai bane namiji ai ko it mum bata da diyan da zata hadata dasu sai ni ? Hafiz ta fada da karfi tare da mikewa tsaye tana fadin ka iya bakinka kada kazo ka fadi abinda zai zamo maka dana sani a gaba. Bani dana sanin komai ko agaban akan wanan mai zubin wawayen zan dawo ina dana sani kome nazone ayita ta kare a daina damuna da zancen wanan yarinyar ana katse min aiyukana dake gabana. Au haka kace ba zaka saduda ba ke nan ta kalloni tace ki tashi kije ki shirya ki wuce school kada ki makara wanan bai san ida ke masa ciwo ba tukun shima ya mike yana fadin idan taje ta tsaya can kada ta dawo gidan nan . Ni dai nashige ina fadin dayafi nono fari a zauciyana a gurguje na shirya na fito na samesu yabini da mugun harara yana jan tsuki ta mike tana fadin mu zamu tafi kaiwa kanka tunane akan hakan. Ban tunanen komai wallahi indai akan wanan yarinyar ne ta gama zama a gidan nan tace muje kyale mahaukaci idanta dawo ka koreta ina shike nan dai ? Motan ta bude muka shiga muka barta ciki har lokacin fada take kwasa dashi tana fadin banda haukan giya a aura maka mace kamar wanan ka tsaya kana bura uba da hauka wai kaiga dan iska ? Baki dai tsaya ya dakeki ba ko ta juyo tana tambayana hakan da kyat na sauke numshi na girgiza kai tare da furta a,a gareta ina hawaye . Kiyi hakkuri don Allah haka yake tun farko da bakin zuciyan nan nasa na banza balle ya fada harkan drugs yanzu shine iskancin nasa ya karu haka. Zancen yakeyi a yanzu baisan babban kuskuren da zai tabka ba a nan idan ya sake aka raba aurensa dake ba baki nayi masa ba wallahi sai yayi kuka da hawayensa ba yana muzantaki a yanzu ba nan gaba zai raina kansane a kan hakan. Ina dai baki fadawa kowa wanan zancen ba zeey don fadan zancen nan zaizo ya shafi kowankune don mutuwan aure baida dadi wallahi ko wani irin aurene kuwa saiya tabawa mutum zuciyansa. Kiyi hakkuri duk wanan haukan shirme yakeyi duk ranan da kuka zama daya dole ya sauko daga duk tsiyar da yakeji avyanzu balle komr hafiz yayi baya sa laifin hakan saboda yana da daurin gindi. Both mummy da daddy suna da hannu cikin lalacewan hafiz Don sun gwada masa gata fiye da tsamani yanzune daddy yake son nuna masa matsayinsa na uba agaresa an riga da an makara ga hakan ko . Nidai ban ma jin wasu zancen nata saboda hawayen dake zuba min duk da na dan makara ranan bata yarda na wuce class ba saida taga dan natsuwa yazo min ta rakoni har bakin ajin don ta daukar min excuse ga malamin dake ciki lokacin kada ya hanani shiga. Ranan haka na wuni a cikon bacin rai sai faman sake sake nakeyu a zuciyana kan yadda zamu kwashe dashi idan na koma din tunda ya furta kada in dawo masa gida a lokacin. Kamar yadda mukazo tare itace tazo ta daukeni don komawa gidan sai naji dan sanyin hakan datayi min sai dai koda muka isa gidan arufe muka samu gidan da katin kwado ya saka ta baya. A gabana ta kira mum tana fada mata abindake faruwa mummy din tace wai hafiz yana da hankali kuwa ko sai na bata mai rai akan zancen nan ne wai ? Kafin tace yanzu ina mama din tace gamu tare da ita gaban gidan tsaye sai mummy din tace ku dan jira yanzun zan kirasa ya bude maku. Amma anty dakin bari na koma gida kawai zaifi don karki tafi yazo yai min wani wullakancin daya wananbdin kuma tunda yace ba bar mai gidansa. Ki koma ina zeey baki yarda da zancena ba ke nan komawan ki gida ai shine babban illa kuma kikoma kice masu me tunda ba sakinki yayi ba balle kije da tushe. Gun baba zan tafi ba gidan daddy zan koma ba na bat a amsa da hakan sai naga ta dago ta kalleni kafin ta girgiza kai tace shi baba garba din shine baisan tashin hankali ba ko ? Ai kina zuwa gida zance ya baci harma in ba ai hankali ba sai zumuncin su ya baci da daddy kan hakan don wanan ba karamin zance ba. Jan bakina nayi ban kara magana ba saboda tunane sa bakin ciki dake cina lokaci guda nine yau namiji kewa koran kare haka kuma ina lake saboda iyayye. Baifi rabin awa daya ba sai gashi da mota fuuu ya shigo saida maigadi ya kauce mai da sauri kadaya take shi muna kallonsa ya fito yana busan iska cikin tafiyan kasaita. Yazo dakey din baiyi maganan komai ba ya bude gidan zai juya ya tafine naji tace dashi abinda kayi ka kyauta ke nan hafiz kai me kake son ka zamane wai ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [3/7, 10:17] Aishatu Aliyu Musa : DUBA MIN BAYA FOKON,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Tare muka shiga ciki da ita bata zauna ba sai bin ko ina da kallo dayi nagidan ga falon sai warin taba sigari da wani tsami da nake zaton na giyane . Daki na juya zan shiga don ban iya jure jimirin wanan takaicin a idona da hancina naji muryanta tana fadin hakkuri zakiyi zeey ki fito ki gyara wajen nan don dan iskan baisan inda kansa ke masa ciwo ba har yanzu shi. Dole ke zaki zage ki gyara gidanki kada wani bakon kunya yakai ga shigo maki gida na hankan ga kinga akwai nauyi da kunya sosai don wanda bai sani bama sai ya sani yanzu ga halin da mijinki yake ciki ai. Cikin kuka na juyo ina fadin anty bazan iya wanan abin ba gaskiya kuyi masa magana idan zaisha ya tsaya waje don Allah yasha abarsa warin abin nan yana sa kaina juyawa sosai wallahi. Nasani zeey ko baki fada ba nasan hakan tare da ita muka tsaya muka gyaro ko ina tana fada min muddin yana gari kada in sake inyi wasa da saka kamshi ako ina a gidan. Bata bar gidan ba saida nayi muna girki mukaci tare ga mahaifiyarsu nata kiranta a lokacin don kira yakai ukku tana fadin tana gidan har yanzu muna gab da kammala cin abincin ya shigo. Ban dago kai nako kalleshi ba yana fadin wai ke har yanzu dama kina gidan nan tace to ina zani hafiz kana son kajawa mutane wani tashin hankali kuma inya kama in kwana a nan yau har kwana zanyi gidan nan ai. Dariya ya kwashe dashi yana fadin zakiko hadu da daddy yau ajiku don yanzu nasan ya dawo gida by this hours bai kai dare a wajeshi ashe kasan da hakan kai ina kafito yanzu ? Cikin gari mana ya fada yana zama kusa da ita yace naga mum da boy ai gidan hjy Binta na fito wurin salis acan nagasu zasu shiga islamiya,Ooh abokin tabaran ka ko ta fada tana hararansa. Kajiki da shirme salis din ne abokin tabarana kawai sako naje in karbo a wajensa wai meyasa kuke zargin salis ne haka sosai lokacin na mike ina fadin. Anty zanshiga ciki idan zaki tafi kiyi min magana na fada ina tattara kayan da mukaci abinci da ita a
Chapter 58 · 0% Book details