← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 61

Sashe 31

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ban masan wanan halin da suke min dubaiya a kansa ba din. Amma halimatu da uwarta duk sunbi yan uwa suna shelata nida uwayena wai asiri mukewa daddy da iyalinsa yasa baya kallon kowa a cikin dangi saimu a yanzu. Ga mutane mafi yawa suna yarda da vamfin akan asiri sai kadane suka san gaskiya basu daukan hakan da tasiri a zuciyarsu su dai san hamon jinine bayan hakan kuma daddy din yana fadawa mutane ai uwarsu daya da baba don a hannun maihaifiyar babana ya tasoshi kuma komai da yazama yau itace silar hakan agareshi. Dawowan anty asibitin nan yasa na zamo mai kula da ita bani kadai ba son har hjy mum da Dada suna bata kula na musamman kamar yadda likitoci suka umurci a bata din. Sai kuma hakan ya koma hassada don ko yaran hjy mummy sun matsa da kiranta a waya suna mata gulma wai kada hjy mum ta asiceta su juya mata hankali don ko wani irin abu a yanzu bata sukeyi da sunan samun saukin gwiwa wanda hakan ya dagawa hjy mummy hankali sosai. Nan ta fara bin yan uwa masu fada aji a cikin dangi don sam taki yarda ta koma katsina tun fitanta gidan a nan kano take zama gidan wata aminiyar ta wanda zaman nasu ya fara canza sallo don hjyn ta nuna itafa ta gaji wanan na cikin abinda ya kara dagawa mummy hankali take yawon bin yan uwa abawa daddy hakkuri ta dawo dakin ta. Tare da alkawarin cewa ta fahinceshi ta daina saka mai ido yanzu ga komai nasa har ta labe ga haihuwan anty Nafisa da take fada masu abin kunyane a gareta Nafisa ta haihu bata gidan nan ai . Wanan suka duba sukaci karfi daddy din ya yarda hjy mum din ta dawo sai kice wata yarinya karama don ko bata dawo ba saida ta zauna ta gyara kanta irin da mata keyi harsu kumshi da kitso da da bata da lokacin yinsa duk akan daddy ya rude akanta ta tsaya tayishi a yanzu din don dawowanta gidan daddy din. Saida ta kwana tayini kafin muyi arba da ita koshi anty nafisace ta kirani wai inzo in duba mata abu yasa nashigo part din amma ina jin komai a wajen hjy mum tana fadan yadda mummy din ta dawo gidan tana abu kamar karamar yarinya. Ina shiga falon mukai arba da ita zaune Asiya da mairo suna gefenta da gani wani zance sukeyi a tsakaninsu na shigo zuwa nayi har inda taken na kai kasa ina gaida ita din da fadin mummy ina wuni an dawo lafiya. Ta amsa min ciki ciki ba yabo ba fallasa agareni hakan yasa na mike da sauri na nufi hanyar shiga ciki muryan Asiya naji tana fadin ina kuma zaki shigawa mutane haka zikau dake ? Sallon ki kullawa mutane wani sheri kuma ace ga abinda akayi maki ko don kinga kina da daurin gindi ba dama ayi magana kike zato. Anty Nafisace ta kirani aida baki gani ba nan na juyo ina fada kafin in kara naji mummy din tace jeki don Allah ina ruwanki da shigowanta ko an hana ta shigo part din ne ? Nasa kai nashige zuciyana fal da tunane saiga anty Nafisa din mun hade a kofa da ita ina fadin gani anty sai naga ta wuceni tana fadi jirani a daki inzo sister . Ashe fada tayiwa Asiya din don komai a kunnenta ya faru na gane hakanne don yadda ta shigo tana huci a dakin lokacin tana shigowa tace dani yaran banza kawai suko koyi basayi da halinki su koya basu da auki sai gulma da kisisina da zaman saka ido suna zuga mummy ko yaushe. Dan dariyan yake nayi mata ina kara fadin gani anty ta kara dagowa har lokacin ranta a bace tace gara da baki biyewa yan iska ai gasu nan komai basu iya ba duk jerabawansu baiyi kyau ba to basuyi karatu ba suna aikin gulma da saka ido mana. Kiyi hakkuri anty na sake fada a cikin yar murya saita ja tsuki kafin tace barin fadawa yan iska ita mummy din da take biyewa tseguminsu ai tafi laifi. Wani abu zan makine tace ehh dama wancan jakkar nake son in duba wasu kaya yasa na kiraki don wallahi tun shekara jiya nake son saukesa amma na kasa hakan. Mikewa nayi na nufi wajen ina sake tambayan wanine a ciki ta nuna min shi da kyar na iya jawo jakar na kawo tsakan daki muna cikin budewa kanin nata ya shigo dakin ban masan yana gari ba sai lokacin. Gaidashi nayi ya amsa min da kyat kafin ya murde fuska yace mekuma ya hadaki dasu Asiya kedake fama da kanki tace munafunci don basu kaunan a zauna lafiya a gidan nan. Yarane ai ki barsu zasu bari don yanzu duk fadan da zakiyi masu basu fahintarki sai suce kin matsa masune nayi mamakin jin kalaminsa din ban dauka ya iya kalma mai taushi ba a rayuwansa sai naji tace is Ok ai ya wuce. Gobe din zaka tafine yace wai haka naso gara nabi file din nan naje ayi komai a gabana zaifi yafi min wanan zaman da nakeyi a nan yanzu tace is better karfe nawa zaka tafi din ? Yace zuwa dai sha biyu nake son in kama hanya OK ta kara fada tare da furta zan ganka kafin katafi din yanzu muna wani dan aikine da sister nan sai ya dan kalloni inda nake duken idan mun gama zan kiraka a waya kazo mu san yadda za,ayi din. Ya juya ya fita ba tare da yayi magana ba nidai ina duke da kaina saida ta juyo tana fadin sorry sister na barki da kaya a hannu aiki yake son samu a abuja su kuma sun aje shi a zamfara shine yake so canzawa. Allah ya taimaka na fada cikin yar siririyar muryana ta amsa min da to Amin abinne akwai wahala mutum ya gama karatu sai kuma aiki yazo yayi tsaye mukaci gaba da gyaran kayan sai kusan magariba na samu kaina kodana fito gun Dada na biya don bamu hadu wunin ranan ba da ita nasan ko sai tayu min korafin hakan. Gashi kuma kwana biyu bata nan taje gun iyayyena ta zauna dasune tayi kwana takwas da tace sati biyu zatayi amma jin dawowan mummy yasa Dada ta kasa zama ta dawo gida don sa ido. Aiko ina shiga ta shiga min korafin ba,aganina yanzu ai take zancena da yake halimatu dakilace saita kyaleta bata tanka mata ba sai kuma gani nashigo wurinsu din. Ina kika shiga hakane ta tare dashi tun jiya dana dawo kowa yazo gaidani banganki ba sai yau din nan har na fara zance ko baki da lafiyane wai ? Nace lafiyat kalau Dada jiyan dai bana gida ina islamiya kinsan na kusa sauka yau kuma tun safe ina wanki yanzu nagama sai kuma anty Nafisa ta aika inzo tun dazun ina wurinta ina gyara mata kayan ta yanzu nafito. Ta dan duba kofin tace dada kinga uwarku mara kunya dai ta dawo taga bin boka da malam da kuka a wajen manya saida ta dawo gidan nan don naci Allah ya gani banson zuri,an mahauta gidan nan don ba mutanen arziki bane cikin mu dama tsoho ya fadi tunda isuhu ya shiga dabi,an nan yace zai gurbata masa zuria gashi kuwa hakan yana faruwa yanzu. Toke Dada ina ruwanki inta dawo tunda ba saman kanki zata zauna ba niko keda ruwa mara kunya tacewa halima data katse zuban da takeyi din tace. Da ban haifi dan ba zata ganshi ta aureshi har ta nace tana zuba iko da mulki iya son ranta haka au ke kika haifeshi ashe na zata Abu mai gyadace ta haifeshi ai cewa takwarana. Don naga da ita daddy yake kwantace ai ungo nan ta fada Abu maigyada tayi komai wallahi don yayi alfahari da ita ai baiyi ga banza ba don ya rike amana har bayan ranta. Niko nasan halima din ta fadi hakane da biyu banko kai karshen tunane na ba sai naji tace wani amana ita kadai ta rike da ai kuma kun rika meyasa ba,a hakan yanzu ? Kina da wata manufa ke nan ga zancenki diyar nan ke kenan baki son a zauna lafiya kulun kina takalan magana to Abu mai gyada da zurianta dai sunfi karfinki don ki sani don ko suna da abinda baki dashi shine tauhidi. Nan ko tasa Dada din agaba tana ci mutunci don me Dada zatace mun fita komai a duniya ke nan ita bata arziki a duniya Dada ke nufi kome ? Nikan nafice na barsu suna rigima a tsakaninsu su biyu a part din na kuma samu mum ta hau fushi dani akan dadewan da nayi saida nace ina gun Dada ne suna rigima da halima na tsaya sai kuma ta koma tambayana akan me kuma suke rigima ? Na labarta mata abindake faruwa tace wanan yar da tada zaune take yanzu kuma ta bugawa uwarta waya tace ga shirin da akai mata akanki baida wuya a wajenta itako data fita hauka ta hau zancen ta zauna tunda ba kunya garesu ba. Nasamu hjy mum tagama duk aikin da zanyi a lokacin don haka na nufi dakuna na gyara a gagauce don magariba ban fito ba saida nayi sallah har isha,i na fito don cin abinci faten tsakin masara yaji kayan hadi mum tayi muna shi kuma mukaci matsayin abincin dare a ranan har ina zancen in kwanta ya Nasir ya shigo shine dan farko da mum ta fara haifa a gidan nima sai daga baya nagane hakan. Don ba zakice bashi ya haifi ya Addel ba gaskiya dubaga irin shakuwan dake tsakaninsu don daddy yafi sonsa da anty Nafisa yana yawan shawara dasu koda kuwa basu kasan zaice ajira Aliyu ya dawo wanda hakan ke batawa hjy mummy rai. Tayi fadan hakan har tagaji dole ta saka iido a karshe tabar zancen a fili amma tana yawan korafin hakan lokaci lokaci zatace abin yana damunta ga diyasa ya dauko bare ya saka ajikinsa duk da tasan shi din ba bare bane a wajensu mutuwace ta kawo hakan. Ba wani abu mai wuya bane indomie ne da kwai zan dafa
Chapter 31 · 0% Book details