← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 61

Sashe 23

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

ba lokacin sai wanan amsan dana bata nima bansan zai fito min ba sai naji tace ke nikike son mayawa da magana ki kama kanki kafin bakin nan naki yaja maki matsala a gidan nan wallahi. Mota nayi kokarin shiga ina gunguni ciki ciki ina fadin ni ina ruwana da zabcen ku nidai nasan ba munafuka nake ba wallahi. A,a mommy na fada maki kibar yarinyar nan don yanzu inkinyi haka wallahi zai koma tsakaninki da daddynmune kuma ku kyaleta don Allah gadai shegiya nan wanan munafukan halima Asiya yarta ta fada. Yan iska duk sai kun bar gidan nan koda tsiya da bala,i babu shegiyar yarcin arzikin da zatazo ta mamaye muna gida ta hana mutane walawa saboda kwadayi . Mairo data shigo motan bayani taji me nace don cewa nayi cin arziki aiba akan mu aka faraba don kowa yaci saidai idan ya manta yanzu. Lokacin ta juyo gareni tana fadin kewa kike fadawa hakan mommy kowa jin hakan ban tankata ba nace gaba da yan suraitana ciki ciki ina jan tsuki. Koda muka isa ban tsaya binta kan halimatu ba nashige aji ranan na hasala sosai na yanke cewa idan mun koma gida zan roki daddy ya mayar dani gidan mu. Bayan an taso breakne halimatu tazo ajin mu take fadin kingani ko kinga wanan muguwar yau dai da idanunki kin gani ke nan halinda nake ciki. Wallahi sun yaudareni zainab sunci amanat,,,, tareta nayi da fadin ni banga komai ba don Allah bar zancen wanan matar banso tunda ba a karkashinta nake zaune ba. Ke zaki iya tuda kina da sauran kimarki a gidan ni kuma sun rabani da hjy mum yanzu kuma sun koma hattarata ga bakin aiki kamar boyar su haka na koma a part din nan. Abinci na bude muka faraci tanata zuba surutu dayasa har naji abincin ya fice min a rai na kudurta zan samu daddy da zancen komawa hannun iyayyena da zama.
Chapter 23 · 0% Book details