← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 61

Sashe 46

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a lokacin hawayene suka fara fito min kafin nace da ita meye ma bai mun ba anty ya dakeni ya zagi iyayyena yaci masu mutunci ya kirasu da yan maula. Don shi suka asirce daddy don a manna masani suci arzikin Dad din na karasa ina wani irin kuka hannu ta dora akai tana fadin nashiga uku ashe hafiz katon wawane ban sani ba. Baba Garba din zai kullawa wanan sherin mutumin da kowa yasan irin kauna da amincin dake tsakaninsu da daddy zai tsaya kan shirme yana masa wanan sherin haka ? Au kema kinji ko kinji abinda Hafiz ya aikata ke nan duk da kema naga laifinki ai tunda kinsan basu shiri me saisa ki kirasa masa ita don Allah. Wallahi hjy mum na zata alheri ya kawosa wurinta bansan dan iska sheri yazo yayi ba na dauka abin arziki ne wanan babban maganan daga ina yafito masa haka kuma ? Atoh kila abinda yaji ana fada ke nan shima ya fadi in bashi ba yaya Garba sa,ansane da zai jefa masa wanan kalamin kamar ubansu daya fa da Alh. Duk da ran anty Nafisa din ya baci da kalaman mum amma haka ta daure tana bada hakkuri ga mum din wai kada zancen yakai ga daddy don laifinta Dad zai gani. Tace nafisa ke nan wanan abin kema kinsan ba abin a kyale bane tunda har yakai ga dora hannunsa akanta tun yanzu ga kuma cin zarafi ai dole aiwa zancen tufka tun yanzu. Ni har naje na fadawa hjy tun dazun ai don tayiwa Alh magana idan ya dawo don dole dai su sani wanan abin gara abarshi tun rayuka baikai ga baci ba gaskiya. Ayi abu don zumunci ya kara a tsakani azo kuma ana da ansani a tsakani ai kinga gara a bari haka zaifiwa kowa sauki tun yanzu. Kai hjy mum kema kinyi saurin fadawa Dada ai da ki bari in dawo mu samu dan iska muyi masa tas amma duk da hakan bai baci ba ai don zaifi gaskiya a tsawata masa doni dan iska ya tashi jawa magana ai a wajen aiki. Da hukumar makaranta sun sani wallahi wanan abin zai iyasa su bani quiry ko kuma su koreni ma don hakan dokane a garemu mai tsanani. Ta kalloni tana fadin kiyi hakkuri don Allah zeey in Allah yaso za,a tsawata masa ya daina ta daga tana fadin bari naje mum kada suga na dade ban dawo ba azata har yanzu ina can. Daddy kan jin abin yayi kamar al,amara ya dade zaune shiru bai iya magana ba sai bayan tsawon wani lokaci yace me yaron nan yake nufi ne wai ? Ke nan ya nuna ni ban isa dashi ba ke nan da zance dashi ga abinda nake so har ya tsaya yana jayayya akai haka shike nan yaje ga duniyan nan ai fadi gareta tunda yana da wani uban dayafini. Yaro in maka gata in hadaka da yarinya ta kwarai kace min ba haka ba shike nan tunda ban isa dashi ba ai koda yake nafi ganin laifin Nafisa ai a zancen nan. A,a Alh kada kaga laifin nafisa don Allah ita meye nata a cikin zancen nan don Allah na tabbatar Nafisa dai ba zata turashi yaje yayi abin nan da yayi ba maganar gaskiya. In kasan halin mutum ko bayansa ka fadi gaskiya akansa babu ruwanta cikin zancen nan yaje da sunan hirane yayi hakan ita kuma tayi fada sosai ga yadda yayi din . Ai gashi ga duniya tun haka uafi masa din aurene dai ba fashi nayi niya sai anyusa kuma ko zai mutune ranan daddy din ya fada rai bace. ZAINAB IDRIS MAKAWA [2/26, 07:16] Maman K: DUBA MIN BAYA FOKON,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , Rayuwan haka yake tafiyawa bawa da kalubali iri iri wani tun yana karami zai fara fuskantar kalubalin rayuwa wani ko sai ya zama magidancin kansa zai fara karo da hakan. Nikan kusan sai ince tun ina karama din na fara fuskantar hakan na baro kauye cikin kunci da matsi mun dawo katsina wanda zuwa kano ya zamo min babban kaddaran rayuwa a yanzu. Don ko yanzu na fahinci shirin buki haikan hjy mum dina keyi don ko duk wani abu daya kamata ace uwa ta tanada nakai yarta aure da zatayi amfani dashi gidan miji hjy mum tana tanadar min shi daidai gwargwadon halinta zakice itace ta haifeni da cikinta abinda take min. Duk da zaman namu Allah baiyishi da dogon tsayi ba amma haka bai hana taimin komai na sakayya a gareni ba takance nidin yartace ta cikinta don ko dan uwanta ya haifa matani. Nidai ina kallonta don duk gayyan kayan nan basu burgeni kosu ban sha,awa kawai dai ido na saka zuciya tab da tunanen me zaije ya dawo min. Karatuna kawai nasawa gaba wanda hakan ke dan sake min zuciya duk da banda kawa da zan nuna ince ga aminiyata yau acikin kano. Bawai kuma ban samu bane a,a bandai ba hakan muhinmanci bane a rayuwata don akwai mutum uku da mukai karatu tare a secondary da yanzu course din mu daya don suma pepper su yayi kyau sosai an kaisu uni. Dan dama su wani lokaci zaki ganmu tare muna hira ko muna dan tatauna abinda ya shafi karatun mu na yanzun don sanin da sukai min mai fasaha tun a secondary a sanadinsu sunana ya fara dan dagawa a class din. Gashi har Saturday nakan shiga school around twelve mu dawo four na yamma don hakane na zama busy sosai a wanyanzun din ban kuma fadawa kowa zancen aurena ba. Wani lokacin nikanyi mamakin rashin fara karatun su Mairo amma nakan bar zancen da cewa watakila dai don result din su baiyi kyau bane daddy din yaki kaisu ko kuma ni na samu daurin gindine a wajen dan uwana daya tsaya min har yaga na samu na fara karatun a yanzu kar a tauye min rayuwa gaba daya. Ranan na dawo school din rana na samu part din mu cike da matan gidan ina shigowa da sallamana Anty Nafisa dake duke ta baza zannuwa tana kallo ta dago tana kwala guda tare da fadin kunga amare fa. Yan gatan daddy aini wallahi daddy ya nuna min banbanci irin wanan lefe haka gaskiya yaran nan kun taki sa,an daddy ba kadan ba gabana yayi wani irin mumunan faduwa lokaci guda na dan daga kai na kalli kayan sau daya na shige daki. Zaune nakai don gaba daya wani irin duhu nake gani lokaci guda saida mm a dade zaune a wajen kafin na rage jin muryoyinsu a falon da alaman sun fita kenan part din. Hakan yasa na daure na mike lokaci guda na fara rage kayan jikina motsin mutum ya shigone yasa na dan juyo inga maishi Antu ce dai still ta shigo dakin nawa. Haba sis kayan lefe ba abin wasa bane balle ku da daddy ya kashewa wa yan nan makudan kudin wajen hada wanan lefen komai iri daya daddy ya saka maku saidai ya banbanta kala don kowa da kalan nasa haka kuma,,,,, Sai naji tayi shiru don fahintar da tayi ba ita nake sauraroba a lokacin tace gaskiya banso ki da haka ba zeey zaki biyewa Hafiz ne ku sabawa daddy ga baki daya ku ? Bayan duk kokarin nan da daddy keyi akanki kada ki bari shedan ya rudeki har a gane hakan akanki bayan kowa na yabon yadda kikayi biyayya ga iyayyen mu din yanzu kuma ki bata rawanki da tsale. Gaskiya kada ki yarda wanan labarin ya kai ga daddy din yadda yake fama yaba hankalinki a wajen kowa ko mairo fa Auwal yazo daga bauchi sun shirya yanzu duk ta rage wanan iskancin data dauko yi kinsan guy din hadadene ga kuma ilimi. Asiya daice da take bin zancen mummy wai ba zata katsina ta zauna ba har yanzu nake dan ganin kanta yana hayaki itama dai din ta rage ba kamar farko ba don na zauna dasu nayi masu nasiha sosai. Kuma na lurar dasu gatane fa daddy yayi maku zeey ke mace ce zeey duk wani iskancin Hafiz na dan lokacin nan ne kina shiga gidan na tabbatar da zaku shiya dashi. Abu dayane zuwa biyu shine nasan Hafiz dan karyane na gasken gaske don haka sai kin zage sosai kin koyi kwaliya girki don kamar Addil yake shima su biyu keda rayuwan tsada da jin kyama a gidan nan bako ina suke shiga ba ba kuma ko wani abinci suke ci ba haka kasafai. Kinga nan ma sai kin kula haka kuma nasan hafiz da son jiki da son jan girma kuma kamar yadda kika sani kowa kuma yasani kinga ke nan a nan sai kin hada da hakkuri. Hakkuri kuma bana wasa ba don nasan kinsan komai basai na fada maki hafiz yana shaye shaye ba duk da mummy tana ganin ba wanda ya sani a gidan nan nasan kin sani a ranan da mummy ta aikeki kai masa abinci part dinsu kuma munyi zancen dashi. Don haka kinga nan ma akwai matsala na zauna nayi tunane da hikima daddy yayi wanan hadin naku keda shi zeey don ke din ta gidace zaki iya rufawa dan uwanki asiri ba kamar wata bare ba ta waje da zata iya tona mashi asiri ga abinda yakeyi din. Zuwa lokacin na kasa boye hawayen da nake faman riko a idona kuka sosai nakeyi a dakin naji ta dafani tana fadin wallahi zeey da hikima sosai cikin wanan auren Daddy bai hadaku ba saida yayi nazarin hakan ya hada kowa da daidai da ita. Kada kiyiwa daddy mumunan zato a wanan hadin naku kice ya manna masa dansa dangiya alhalin su yayansa ya zaba masu masu kirki . Ba haka abin yake ba zeey wallahi na fahinci daddy a yanzu duk wanan hadin da daddy yayi yayisane akan hikima
Chapter 46 · 0% Book details