← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 61

Sashe 25

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

part din hjy mommy ne nagaida Dada sai kuma ta tsaya bamu labarin abinda ya faru da anty Nafisa kinsan Dada bata bari na fito ba ta kaimu wai gaida ita. Gaskiyane basa so ai dama nasan hakan zai faru tunda basu tsaya sunyi dogon bincke ba a kansa suka dauki yarinya don kada ranta ya baci suka mika mai. Damani ina ganinsa nasan dan duniya ne don daganinsa irin tashin turai din nan ne ba kwabo komai a sagarce yakeyinsa suko hakan naga bai damesu ba illa murna da sukeyi yarsu ta samu gidan hutu. Dan gidan nan wani irin hutune bai samu ba inba yanzu da Alh ya kori yan aiki muke yan aiyukan mu da kanmu ba da yan aiki nawa ke gidan nan nasa dai akaji amma da za a zauna dashi shima ya fadi nasa nasan tana da laifi itama. Bayan sallah isha,i har lokacin ina lake a wajen mum dana shafawa abonake a jikinta don tace ko ina jikin bata jin dadinsa a lokacin. Ya Addel ya shigo falon da ledoji a hannusa da sauri na mike na karba na aje a gefen mum din fita nayi na wanko hannuna dake warin man na dawo mum ta dago tana fadin na dauka ai plates kije dauko muna. Na amsa da hannu na wanko mum bari na dauko yana zaune shidai haka halinsa yake koda uwarsa bai yawan magana kamar sauran yan uwarsa zai zauna yayi shiru kamar maraya ashe shi. Sai uwar ke magana ina shigowa da plate din tace amma kamar wanan abincin yayi muna yawa fa lokacin ya dago yana cire tagumin da yayi din yace ba abinci bane ai mum don nasan da wuya ki iya cin abinci a yanzu. Ledan nake kiciniyar budewa jin yace ba abinci bane take away na fruit sald nagani guda uku sai dayan leda kaza guda biyu manya irin gyaran shagalinka kudinka din nan. Sai kamshi ke tashi na dora daya a saman plate din nakai gaban mum din na aje komai a gabanta harda madaran hollandia na lwali kananu guda hudu. Ina kokarin dora masa ya sake dagowa yace no ki barshi nawa na cikin mota idan zan shiga zan dauka nakune wanan ya fada kamar a gajiye yake. Mama matso muci kinji ta fada shidai wanan abin da farin jini yake watau don dai nasan ba,a kwana biyu bamuci kazaba amma wanan din na daban ne na motso kamar yadda tace din. Na mika hannu ina dan yaga naman takai hannu ta dauka mukaji sallaman daddu ya shigo hakan yasa ya dan sauko da sauri yana gaida daddy din da wuni daddy din yace. Aliyu dama ka dawone ashe to ya Abuja din da fatan ayi nasaran tafiya dai ya dan sosa kai yana fadin dama yanzu nake son in nagama in shiga ina dakon kagama cin abincine sai inje in maka bayani. Don yanzu shigowana ke nan gidan dazun munyi waya take fada mjn bata jin dadi shine na tsaya nazo mata da magani har na makara . Ai nazo mata da wani Hafiz ya fada min nasoyo mata tasha da zanshigo ai kace nazo a makare ke nan ashe ka rigani tallafawa a nan suka danyi murmushi yakai kallonshi ga abinda nakeyi yace uwata babu ko tayi ? Murmushi nayi ina fadin daddy sannu da dawowa yace naki ai baki ganni ba tunda kina gaban uwarki Allah daddy ina jiran ku gama da yayane ingaida kai na fada ina kumshe kaina cikin kunya. Yau dadi za acine haka ya kara kallon abincin yana fadi mum tace dadi kan ai kullun kana bamu shi gidan nan munaci wanan danka ya sayo muna yace kada kanwarshi tayi girki yamma yayi . Ka kyauta gashiko dama idan mutum ya tashi ciwo yana jin kawa kaga wanan abinda matasan yanzu basu ganewa ke nan sai su dauka kudi kawai iyayye ke bukata akullum ba kula ba. A saka makane mum ta fada da sauri ya Addel din yace no ki barshi bari na dauko masa nawa a mota sai in sayo wani . A,a ka bar abinka wata rana zaka saya min da sauri ya mike yana fadin a,a daddy ya fice daddy ya kai zaune yana fadin yaron nan tausayi yake ban koda yaushe kamar yana cikin damuwa yake ko an tambayeshi yace ba komai. Shi sam baya da sakewane shiyasa nake fita zancenshi mutum ya zauna kullun shi kadai yayi ta tunane ka rasa abinda yake tunane kuma lokacin yayi sallama ya shigo da ledan irin namu yake fadin daddy akaima can ne ciki ? Yace miko min nan kafana kafan kayata fruit din nan yafi min komai dadi a cikin kayan nan don ina sonsa sosai su kuma suna kiuyan hada min shi kullum. Ayya mum ku dinga hada masa don Allah yana da kyau wanda yakai shekarun ku yana shansa kullum don yana kara lafiya sosai a jiki. Kai rabu da babankun nan fa mum ta fada a daidai lokacin da wayansa ya dauki kara yana kiciniyar fito dashi daga aljihunsa ya kara akunne. Mu dai munji yace ina zan tsaya kuwa ina nan part din hjy kubura nazo duba jikinta kome tace mun daiji yaja tsoki ya kashe wayan yana fadin mutum bai girma. Wanda keda tashin hankali haka gabansa zai tsaya wani fadan shirme inba hauka ba ni wai ko malka tana da tabin hankaline dai. Wani abu ya farune ya Addel din ke tambaya daddy yace ya faru mana yadda suke so dama in mutum yace iyayye basu isa masa ba shiya iya ai karshensa ke nan wahala. Sai ya soke kai yace Nafusace dai miji ya sako da ciki dazun shine har uwarta taga wurin fadan shirme yanzu nasu na mata marasa hankali. Innalillahi ya ambata da sauri yace garin ya haka ya faru kuma yace ba ita tace taji ta gani ba da auren bare ga diyan dangi tako ina duk yawan mu kamar kwaekwata wai ace saita tsalake ta auri bare toga abinda ya biyo baya yanzu ai. Subbanallahi ya sake ambata ina zaune na soke kai a kasa ina sauraren su na kasa cin komai don daddy dake wajen da ya Addel din. Mikewa daddy yayi yana fadin abin takaici wai kamar Nafisa miji ya sakota taki fita saiya hada da hukuma an mata koran wullakanci sanan ta fito. Kai abar zancen yariga ya faru yanzu kuma ai mata uziri don Allah taji da abinda yake damunta yawan surutun nan sai kuma ya kara jefata cikin wani hali. Ko ance din yana maganine yanzu tunda saki ukune ba gyara subbahanallah wanan wani irin wawane shi da zai saki mace da ciki har saki uku ya Addel ya fada rai bace. Kaddarace kawai amma tun farko mutumin nan yana da matsala ga duk wanda ya kallesa yasan kuma dacewa amma sam Nafisa bata dace dashi ba gaskita abu daine baya faduwa a lokacin aga bakinka ga banza. Har daddy yakai kofa da ledanshi a hannu ya juyo yace ai yanzu dai ta kare tunda ba gyara kuma yasa kai ya fice daga dakin yana dan lalabawa. Ajiyan zuciya na sauke a daidai lokacin da mum ke fadin ai abi ke nan in ce mutum ya bari suce bai waye ba toga wayen nan mungani yanzu Allah dai ya sauwaka Nafisa kan yanzu ta zama abin tausayi ga ciki dole a lalabata. Shiru nayi ina kara nazari kalami kowansu a raina shima bai dadeba ya tashi ya fita yana tajan tsoki nasan abin ya taba mashi zuciya sosai a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA [2/3, 07:47] Aishatu Aliyu Musa : DUBA MIN BAYA FAKON,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Sosai naji dadin fruits din nako bude ciki na dirka naci naman don bambcin da yake dashi da wanda mukeci saboda wanan dai gadashi akayi dan ruwan kazan na ainihi na jikinsa wancam kuma nagida ai soyashi mukeyi wanan ne vamvamci da mutane ke daukin cin nama kasassa wani lokaci saidai da yake ra,ayi ya bambamta wani lokaci kowa da abinda ransa keso. Mun danyi kallo don da alaman Mun ta samu sauki tun shan magani da kuma mai dana shafa mata banji ta kara korafin wanan ciwon kan nata ba kuma don so dayawa yana damunta gaskiya zakiji ta kwanta tace kai na mata ciwo. Saura na dauka nasa a fridge kada ya lalace na rufo ko ina muka kwanta don yanzu a daki daya muke kwana tun bayan barin halimatu wajenta. Da yake washegari ba school hakan ya bani daman samun yin batcin safe sai karfe takwas da rabi na tashi na soma yan aiyukan gida da nasan ni zanyi don nikan gaskiya ba sai an tuna min aikina ba. Kafin goma da rabi har wanka nayi na dauki kayan karin Dada da muke kai mata irin wanam raman nakaiwa Dada din kamar yadda muka saba duk weelend idan muna gida. Sai lokacin na tuna da zancen anty Nafisa din na shiga wajenta zaune take bakin gado ta kurawa kasa ido tana tunane idamuwanta har lokacin sunyi hulu hulu dasu wanda ke nuna alaman bata bar kuka ba. Gaida ita nayi ta dan dago a sanyayye tana amsa min kafin in samu waje a gefenta nakai zaune kasa na dago na kalleta nace. Anty kiyi hakkuri nasan akwai zafi hakan don anzalunceki amma inkinyi hakkuri kin barwa Allah lamarin sai ya saka maki kan zaluncin da akai maki din daga baya don kukan nan illane yanzu a gareki halin nan da kike ciki. Cikin dan tausa murya nake kallonta ina fadin hakan sai naga ta fara sauke wasu hawaye masu zafi a fuskanta nima bansan lokacin da hawayen yazo min ba na fashe da kuka. Ajiyan zuciya naji ta sauke kafin tace
Chapter 25 · 0% Book details