← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 61

Sashe 37

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daya lafe ina kallon ikon Allah saida suka tafine kowa ke fadan albarkacin bakinsa kan yarinyar nasa nikan ina tsoro ban furta komai ba nabarwa cikina mamaki. Aiko labari har kunnen iyayyen mu yakai nan hjy malka aka samu abin fadi don tun mum bata gane ba har ta gano ta tsureni tana tambayana amsa daya na bayar shine kila bayan fitowana sukazo. Wanan kalman ya rabani da kowa lafiya ana gobe suna aka sallamo su Anty suka dawo gida har lokacin uban yaron bai tako yazo yaga dan nasaba. Ko hakan yasa anty Nafisa yin sanyi ba kilama don gaskiya abin yana damunta sosai don tun tana boyewa har ta fitar muna da damuwanta fili nida iya da muke dakin wanda ba komai ya dameta sai rashin radawa jaririn suna da uban bai aiko ba. Nan ta gane lalai furcinshi akansu da gaske yake har dan ya yafe mata ke nan yake nufi wanan nasan yasa hankalinta tashi adaren sunan. Don ba itaba har mummy lokacin jikinta yayi sanyi da zancen don ta rage yawan rigiman da takeyi da farkon haihuwan sun koma shiru shiru yanzu. Ashe bamu sani ba daddy yaci masu mutunci daga uwar har yar nata don yakira shi habib din kan zancen sunan ya so gayawa daddu din zancen banza akan anty nafisa din shine shi kuma ya sauke haushin hakan akansu da yadawo gida. Bayan ya fitane nashigo nan ne take muna korafi nida iyan mai kula dasu shigowan ya Addil gidan yasa muka danji sanyi inda yace suna kan za,ayisa don ba za,abar yaro ba suna ba ai hakan saiya zamo abin kunya ga family tunda yana da ubansa. Ga daddy yayi rantsuwan cewa bai yankawa yaron rago da kudinsa duk nan takewa yaya din complain yace yaro kan yana da gatansa ai don bai fado a gidan banza ba . Shi dai da ya mayar da kansa dan iska yaje duniyace ai zata bashi darasi komai dadewa bayan ya gama lalashinta yake tambayanta sunan da take so ta sanyi dariyan yake kafin tace ga uwarsa nan zeey ka tambayeta sunan da sukeso. Farat nace yaya kasa mashi mohammad don Allah mu dinga kiransa da Amir baiyi magaba ba bayan dan kalloni da yayi sai washegarin suna kowa na zaman darr sai gashi ya shigo yana fadin suna da Mohammed rago biyu manya aka yanka. Sai akwatina set da aka shigo dasu wai inji uban da wanda komai na baby da uwa ansaka aciki daya kai wajen Dada ta kawo ko mum bata san yayi wana hidimar ba don ya hana yar uwarshi kukan zuci mai yawa. Albarka yasha shi wurin kowa wanda bakin mummy ya mutu mutus da ganin kayan idan ba dan gida ba yadda kowa ke fadi idan yashigo yaga kayan zasu tambaya wanan kayan sunane ace masu ehh. Zakiji sunce gaskiya yayi kokari haka akai suna kowa na farin ciki da yamma akai walima anci ansha an raba abubuwa kamar ko wani suna aka watse. Da daren kuma wanan budurwan nasa ta zowa jariri da nata gudun mawan shake da leda don ko Pampers har hudu nagani a cikin kayan. Ranan kuma bata tafi ba saida tabi su mum ta gaidasu taba kowa turmi daya daya har Dada wai na fitan suna wanda kowa yasan aiki ya Addil ne hakan. Sani mum bata so yasa hjy mummy kama zancen kamar da gaske wai danta yayi dace da mace ta gari gaskiya wanda kowa yasan bana Allah takeyi ba hakan da takeyi dayan biyune. Ko dai don rufawa yarta asirine da yayi ko kuma akwai abinda take kokarin kullawa gareshi nan gaba don danin halin mummy din da kowa yayi. Mun dora abubuwan shagalin sunan da akayi wanda har ita maijegon ta dora hakan yasa shi uban dan gani a status dinta har yabi bayan kwana kamar ukku da suna saiga yan gidansu sunzo. Da nasu kayan suna wanda ba wani abin azo agani ciki kuma wai sunan da Sani sunan kakansa Dada ko ta hausu tace su dauki kayansu su tafi yaro ya rigada yaci sunanshi dama mohammadu daga iyayyensa masu kaunarshi. Mum ce tasaka baki har suka danji sanyi aka karbi kayan da sukazo dashi din daga bangarensu suka tafi tsomai tsomai dasu da kunyan da dan uwansu yaja masu. Haihuwan nan na anty Nafisa yasa innan mu zuwa gidan akai akai wanda zuwanta kusan uku duban maijego da danta bayan suna kuma suka dauke kafafun su don gudun magana. Ganin angama shagalin buki lafiya yasa na mayar da hankalina kan karatu na da yanzu saura kiris mu kare gaba daya mu fada wani matakin a yadda nakewa kaina fata nan gaba. Don ganin yadda su Mairo suka maimaita shekara yasa ko ysushe ina addua Allah ya taimakeni inketare nawa ba tare da tabgardan komai ba ZAINAB IDRIS MAKAWA [2/17, 08:02] Maman K: DUBA MIN BAYA FOKON,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Alhamdullahi zance a yanzu don duk wani challenges din rayuwa da nake samu a gidan daddy hakan bai hana in tsaya inyi karatu ba don ko naga abubuwa kuma naji da kunnuwa amma haka na daure na fuskanci karatuna. Sai gashi Allah ya taimakeni na fito da sakamako maikyau da har daddy din ke alfahari dani akan hakan wanda wanan abin a wani bangare yayi min dadi wani bangaren kuma baimun dadi ba. Don ko yaja min bakin jini a cikin gidan sai bangaren mune kuma suke nuna min farin ciki sosai a kan hakan suna yabawa. Mun gama da sati biyu lokacin akai bukin auren ya Addel wanda asha kwama cala a lokacin bukin don hjy malka ta dauka cewa daddy ne ke masa hidima wanda hakan har ya kaisu da zama da manya akan bata yarda da abinda Alh yakeyi ba tunda shima yana diyan daya haifa da cikinsa. Hjy malka bata da kunya ta ido Daddy baiyi magana ba saida yace a kira hjy mum don abune daya shafi family tazo dashi don haka suka bukaci da mum tazo falon a zauna da ita. Bayan mum da Dada sun shigo daddy ya kalleta yace hjy kubura ina son ki fadi tsakanin ki da Allah ya mukayi da Aliyu kan zancen aurensa daya nace sai wanan yarinyar . Kallonshi tayi cikin mamaki tunda abin sirine daya shafi ahalinta a lokacin yace maimaita don Allah mum din ta dan gyara zama tace ehh to kace ba ruwanka da zancen auren iya sadaki zaka biya masa tund yaki bin akidarku na gida sanan bayan hakan yasani zaka kara mai mata muddin ana raye yar gida kamar yadda yake ga al,adan nan gida lokacin zakai masa naka auren kamar kowa . Hannu ya daga yace ya isa haka kunji ko bayan wanan me suke shiryawa me suka hada wallahi ban sani ba kayama da kike zance nasan akansane ga hjy kubura ta gaya min nazo nagani sungama hadawa nace sukai Allah bada sa,a koba haka akayi ba ke kubura ? Allah da Annabinsa sunyi gaskiya da sukace zato zunubi koda ya zamo gaskiya a wajen bawa kin daiji hjy malka ba hannun Alh a wanan zancen ashe . Daddy ya dauka da fadin jiyan nan yazo yana fada min cewa yasai gida a Nasarawa nima da mamakin hakan na kwana a raina. Saidai banyi mamaki ba duba ga inda yake aiki yanzu a matatan mai na kasa koda yayi hakan zai iya yin fiye da hakan ma idan yaso. Wani gwauron ajiyan zuciya mummy ta sauke dayan babansu yace ai a haifi da arziki yafi a mutu abarmai gado wanan gaskiyane kowa nan ya sani. To amma waya dorashi a hanyan hakan ai kaine dai Alh kana da daman yadda ka samu nashi aiki a nan wurin samu suma sauran ka sama masu ai kamar yadda shima kai masa hanyar. To ban samoba din don bansan inda ake samuwa ba ko kina nufin sai kin jefawa diyana kiyayyana dana dan uwansu a kanmune kwadan ki zai fada. Bansan ya yayi ya samu abinsa ba illa takarda daya zo muna dashi gidan nan na aikinsa danki dana samuwa aiki ai rainaw kukayi ashe hangen nesa kuke masa wayasan na samuwa hafiz aiki a gidan nan bayan ke ? Ko ita kuburan bata da dan dana haifa da itane da yake son aiki baga Nasir nan zaune a gida ba shima ya gama nasa karatun ? Yanzun dai abar zancen tunda angano gaskiyan yadda lamarin take kowa yasan yadda zuciya take bata da kashi ke hjy malka kinyi kuskure ai kafin ki taramu nan yakamata ki tambayi mijin ki yai maki bayanin komai. Kona tambayesa aiba fada min gaskiya zaiyi ba don haka na kiraku a nan hjy mummy ta fada cikin jin nauyi da kunya da batayi tsamanin zai koma a kanta ba lokacin. Ba zan fada ba tunda ita yar uwar zaman naki bata taba tsareni kan harkuku tasani a gaba ba duk da tasan ina tauye ta wani lokacin ta barmu ga Allah dani dake. Baba kun gama dani in tafine mum ta fada tana mikewa don takaicin daya rufe mata idanu lokacin Dada tayi magana tace ina zaki ai ki tsaya kisha labarin irin cin zalinki da sukeyi a gefe daya tunda yau ranan tonon sili a garesu. Murmushi Mum din tayi tana fadin niga Allah na dogara don shine gatan mu nida yaran nawa duka tana fadin hakan ta juya ta fita nan yan uwa dasu Dada suka hau kan mummy din da fada akan bata kyauta ba tana hassada da dan yar uwarta kan duniya. Akarshe dai dole taba daddy din hakkuri su babanane suka samu mum a part dinta suka bata hakkuri akan abubuwan da ake mata gidan ana danne mata hakkinta din. Inda daddy Enugu yake cewa
Chapter 37 · 0% Book details