Sashe 19
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ni dai ban amsata ba don zancen yafi karfina. Irin wanan bani kan tanka mata dan dama dama abinda ya shafi aikin kitchen dana cikin part din ta amma wanda ya shafi rayuwanta gaskiya ya girmewa tunanena nikan duk dako wani lokaci ko damuwane ke saka tayin zancen dani ban sani ba. Shigowan halimatu dakin ya dakatar da ita ga fadin komai ta kallo halimatu din dake fadin ashe kin min wayau kin shigo nan ko nima wallahi wurin kwanci nake nema inna ke fada min ai kina nan. Gashiko dama ke nake jira ki shigo in aikeku nan bayan layi gaki kuma kina fadin kin gaji saita kallo hjy mum din dake shiri tana magana tace ehh aiken ku zanyi yanzun nan kuwa. Nima na kalli mum din dake magana ba alaman wasa a gareta ganin nima na yarda da abinda take fadi yasa mum din cewa wasa nake mata mamana har wani aiki tayu datake fadin wai tagaji haka ina karfin aikin uwatace tayisa ai. Wai da sai ince yanzu ga wayanda aka bari wurin buki dazun suna fadin yadda gari yayi duhu mukan da aka kunna inji ai kinga bamu san wanan ba nan muka dauko hiran bukin tana dai shirinta sai lokaci lokaci take bamu amsa. Zata fitane take fadin idan kun tashi don Allah mamana ki fita ki rufe kofan nan na cikin gida kada ku kwana a sake na amsa da to tayi muna saida safe ta tafi wurin mijinta. Mun dan jima muna hira kafin namike don jin part din yayi shiru nafito don in rufe wajen ganin mutane sun dan rage zirga zirga a lokacin don haka zan rufe gidan kamar yadda ta umurceni dayi din. Kodana fito mutanene har corridor din hjy mum din don dama nasan za,a rina don ba karamin mutane sukazo yiwa baban kano din kara ba sabodashi mutum ne maiyi ga zumunci da kula yan uwa sosai irin mutanen nan da kudinsu bai rufe masu idanunsu ba. Haka na tsatsalakasu don wurin a gyare yake ko yaushe ties ne malale masa har karshe kuma babu wani datti don hakane basuji kyaman kwanciya a wajen ba. A yadda naji suna dan tsegumin cewa da mutum yaje part din hjy malka za,a koroshi ace ga wajen yan katsina can wanan abin yai masu zafi sosai don sunata magana akan hakan nasan ko dama za,a rina dasu din. Don ance wata gwaggon mu saida sukaso fada da hjy malka din take fadin malka ki tuna ba rawa kikayi gaban Allah ya baki wanan matsayin ba ya barmu duk da kika ganmu nan saboda ku mukazo wajen nan balle kita koran mu kauyawa. Itama hjy mum din tace ke kika sani dai haka nace ku koma shiyan hjy kubura don can akai maku masauki matar tace don tana yar kauye yar uwarmu ko to ai zamu koma kuwa inda aka san mutuncin mu din. Jin karan rufe kofa yasa dayan tambayan waye na amsa da nice gwaggo ina rufe kofanne nasa sakata tana gyara kwanciya tace hakan ma yafi sannu kinji nayi masu saida safe nashige ciki. Washegari ban bari an tayar dani ba na tashi kitchen naje na kunna wuta kafin na koma bin daki daki ina kunna heater don a rage wahalan ruwan zafin wanka. Gamu katsina duk yadda kayi da bakatsinem mutum bai yarda yayi wanka da ruwan da baida zafi koda kuwa dan dumi sukayi basuyi zafi sosai ba basu iya wanka dashi. Tun wanan ranan muka samu sauki a part din don hjy mum bayar da aikin tayi ana dafowa ana kawo muna anan saidai muce wahalan rabone muba mutane shine kadai wahalan mu gashi kuma wasu sun karban muna aikin don haka muka samu akai sha,anin bukin damu babu takura. Kamar ko wani gida suma wanan gidan suna da nasu a boye wanda dama sai mutum daya ya kwanta irin hakan har mutane kan zata akwai zaman lafiya a tsakani. Don a zahiri dai hjy mum ce a gidan nan ta kwanta ake takanta iya son rai wanda har mai hankali zai iya gane hakan shigar a farkonshi gidan. Saidai hakan baiyiwa hjy malka ba son ita burinta kawai tabar ganin a gidan ga baki daya shine muradinta a kullum cikin irin hakanne ta samu mijin nasu da wani zance daya bata mashi rai. Har tayi ta kare bai tanka mata ba saidai bata sanda wanan karon takaishi makura ba don ya gama fahintar idan ta dosa dai a yanzu har yan uwashi na kud da kud duk hjy malka bata kaunan kowa dashi to me hakan yake nufi ke nan ? Da yake daurin auren ranane sai ranan dauri aure iyayyenmu maza sukazo daga katsina ciki ko har da babana saidai baizo da kannena ba ya barsu a can gida wajen wata kanwarsu baba musa da keda tsohon ciki ita bata samu zuwa bukin ba. Yayi murna sosai yadda yaga na koma a dan zuwan nan namu kano din sai washe baki yake ya kasa boye farin cikinsa a lokacin gareni na tambayeshi kannena yace suna gida tare da gwaggon mu a can ya barsu da zaizo ninayi ta dawainiyar kawo masu abinci da abinsha da aka tanada donsu dama. Sai bayan daurin aure da sukaso tafiyane baba na kano ya hanasu tafiya ranan sam basuso hakan ba don tafiyan nasu bana kwana sukai niyar yi ba a ranan suzo daurin aure idan angama su juyane sukazo sai gashi yace yana da magana dasu kada su tafi. Dole suka dagata da tafiyan sai washegari da safe aka hade a wajen nan akaita dawainiyar kai masu abin karya kummalo bayan sunci sunshane Alh ya dauko masu zancen ya fara da sallama tare da godiya kafin ya danja lokaci irin ta manya yace. Dalilin dayasa na tsayar daku a nan shine kan matsalana da iyalina shine ma musassabin tsayar daku din da nayi din ina son in kafa sheda daku don ku sani na kusa rabuwa da malka a matsayin matata na sunna don ba zan yarda ta konani ba saboda son zuciya irin nata. Nan suka dauki fadin subbahanallahi meyayi zafi haka Alh yace hakane donshi na tsayar daku don kafa sheda don kada kuji zancen kuce ban kyautawa iyayye ba ko wani abu a gaskiya nagaji yanzu. Don nasan bayan wanan bukin akwai gagarumin fitina da zamuyi da ita wanda zai biyo baya tsakanina da ita don haka ku sani wanan karon zan dauki mataki akanta. Baikai can ba Alh ka bari abi komai a sannu zamu zauna da ita din akira muna ita yanzu basai mun tafi ba nan ya fayece masu irin zaman da sukeyi dashi yace kowan ku nan yasan yadda na auri malka. Takuma shigo gidana ta samu kullu da kubura har tayi sanadin fitan kullu data biye mata a lokacin sukai ta tashin hankali har yakai saki ya shiga tsakanin mu. To hakan takeson yanzu a maimaita kan Kubura kuma ya kasance an barta gidan ita kadai daga ita sai yayanta a gidan nan tana yadda take so wanda ko hakan ba zai taba yuyuwa a gareni ba. Don ba zan yarda inje lahira in tashi da barin jiki shanyayye a na nunani ana fadin ga wanda mace ta halaka a duniya to ba zan yarda takaini can ba donta hakan ya faru dani. Hakan ma ba zai faru ba insha Allahu Alh kowa yasan kai mutumin kirkine a cikin yan uwa bamu fatan hakan ya faru dakai insha Allahu wani dan uwan hjy malka din daga cikin iyayyemu ya fada. Nan sai aka kirasu har Dada da hjy Mum sukazo a zatonsu sallama zasuyi da bakin gida din zasu koma sai bayan sunzone sukaji sabanin hakan ga bakin baba sani. Indaya zaiyano abubuwan garesu cikin hikima amma kafin yakai hjy malka tareshi da fadin shi Alh din ya fada maku hakan ko wani dan game game ya tsayar daku ya fadi hakan a kaina don makirci. Tunda wanan zancen nasan gun yar bakin cikin nan zai fito tunda ba kauna takeyi ba ta kallo inda hjy Mum din take zaune a falon gefen Dada. Au wai dama dani kikeyi hjy malka niki sani baku cikin zancena don nina dogara da turban da iyayyena suka dorani tun farko nasha tmTabara nasha Yasin sai gani sai hange a wajen ki duk wani sherikin a yanzu ni baya girgizani tunda ba kallan sherin ki daban sani kuma ba hjy Malka. Haka dai kikace fadi a baki Annabi a baki zuciya fir,auna waye bai san abinda kema kikeyi in kina takama kinsan na wani. Saidai zargi irin haka din don ba zan biyewa sherinki mu lalace a tare ba saboda duniyan nan me karewa ga bawa. Kina ganin akwai wani abinda zakiyi koki fada yanzu da zai firgitani kuma nasan irin ku shedanun mutane masu kai mutum ga halaka to bani cikinsu kin sani. Ku dakata don Allah ba mun taraku a nan bane kuyi muna irin wanan haukan yanzu mun tarakune don mu sulhuntaku mu gyara tsakanin ku kun tsaya kuna muna hauka. Mune ma mahaukata yau Garba don samun waje wai tsaya kina nufin Garba din ma baida daraja a idonki ke nan kome ta kallo baba na kano dayai maganan yace kun gani da ku barni da ita in nuna mata iyakarta. Nan dai akai ta magana aka taru wajen aka bata rashin gaskiya tare da ja masu kunne kan zaman nasu kamar kananun yara dasu. ZAINAB IDRIS MAKAWA [1/28, 09:55] Aishatu Aliyu Musa : DUBA MIN BAYA FOKON,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Da ace nashiryane aida mun sauka gida a yau din nan muma Dada ta fada daga inda take tana mikewa tsaye don tagaji da jin irin jayayyan da akeyi da hjy