Sashe 44
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
rana haka naga dare barci sai wajajen asuba nasamu don ko mum bansa tayi barci da dadi rainmba a rana kowa zuciyashi ba dadi a gidan. Washegari monday haka na tashi ina shirin bin anty Nafisa school har na shirya mum tasa na dan kurba ruwan shayi mai zafi don cikina ya walwale don tasan banci komai ba da dare tun abincin safene dana karya acikina na jiyan. Bata zo sai waya data bugowa mum ajan cewa inna shirya in fito gata waje tana jirana koda zan fita saida mum ta kara ja min kumne kan kar in yarda inyi wani zancen dabai dace ba da wani. Zaune na sameta cikin motan tana jirana ina zuwa ta bude min gaba gefen drive nashiga na zauna muka tafi mun dan bar kwanan gidan take fadin waike zancen daddy ne har yanzu a zuciyan ki ? Zancenshi yakeyi kawai don yasan wanan abin da yake sonyi ba abu bane da zaiyuyu haka don wanan zamanin ya shige na auren hadi abin ma babu ko dadin ji ai gara dake. Asiya da za,a dauka zuwa katsina fa ansan aure yana iya kai mace ko ina amma ace wai kamar Asiya za a hada da wanan don Allah. Me Asiya tasani fisabilillah gaskiya idan daddy yai haka bai maku adalci ba a raina niko fadi nake wani dama da auren mashayi ai gara zuwa kauyen koda kuwa kauyen kauyayyene. Itama din danata bacin rai don cewa tayi sister kiji min Dad fa wai zai min auren dole ina karamata haba dai sai kace ku di n nan ba aimin auren hadi a daba balle yanzun nan dako mijin nan yaga iskanci. A gurina mai saukine idan daddy yace na bar mai gidansa kawai saina tattara inbar gidan in kama haya ko in nemi gida aban nan quarters din staff din mu in zauna. Amma wanan auren hadin gaskiya ba mai min shi a yanzu dai kan koda banyi ba balle yanzu wai kinsan mun taba soyayya na yara da Addil tun lokacin mummy ta sakani gaba saida ta rabamu tun wanan auresu na gida ya fita raina. Duk da na tabbatar dashi nake aure a yanzu da duk wanan bai sameni ba da ina gidan mijina a zaune don Addil mijin aurene halinsa yana da matukar kyau sosai wallahi amma mummy ta rabamu. Halin da nake ciki bai barni nayi mamakin zancenta ba don jin abinda ta fada kan dan uwan namu watau wanan yasa dukkansu sukaki auren hadi sukayi na son ransu ke nan. Muko anki bamu dama mu gwada sa,anmu a wajen mugani koda sa,a sai wani hadin ganbiza da daddy yai muna inani ina ya hafiz mai zuciya kuma dan giya koda yan uwanshi da suke uwa daya ina ganin yadda suke kwasa dasu kullum shi basuyi daidai ba a idonsa. Balle ni yanzu da zan zauna da sunan aure dashi ya rayuwan zata kaya a tsakanin mu nida yakewa kallon bagidajiya yar kauye kuma fa ? Nasan akwai fitina kwance a kasa ga aurenki da hafiz tunda hafiz ba zai hakkura ba don yace ke ba kalan macen da yake so bace bayan hakan kin masa karama ga aure nasan da hakan. Amma naso yayi hakkuri kubi umurnin daddy din yaki ya fahinceni shida mummy yanzu kuma ga zancen auren su mairo ya taso gaskiya daddy baiyiwa mummy adalci ba a nan. Shi yana duban nawa auren yadda ya kayane shin daddy baisan da kaddara bane dama Allah baiyi zamuyi dogon zama da habbib ba ko kuma dayan mu na iya mutuwa zaman ya yanke ai. Ban tsamanin shi yake kallo anty amsan dana san na bata ke nan kada tayi ta zuba ita kadai ba tare dana dan tanka mata ba sao naga ta dan girgiza kai tana dukan sitiyarin motan tace. Baki san waye daddy ba ke nan yadda mukai mai banga da auren habbib shine yanzu yake son ya rama akan yan uwana ya rike zancen a ransa tun farko kuma nasan hakan zai iya faruwa tunda abin nan ya faru tsakanina da habbib din nake fargaban hakan amma ban dauka yan uwana zai shafa ba. Mun shiga haraban makarantan ta samu waje tayi parking din motan sai lokacin ta kalloni tace nasan kina cikin wani yanayi a yanzu ki daure ki tsaya ki dage da karatun nan shi zai kwato maki rayuwa a nan gaba insha Allahu kin dai gani yanzu a gareni. Kusan tare mukai komai don bata barni nayi wani wahala ni kadai ba sai wajajen biyu nagama don samun taimakonta da nayi na zama daliba ke nan a yanzu nima . Don gata yai min komai bansha wani wahala da sauran dalibai suke samu ba yayin cike ciken form dinsu saboda ita don tana aiki a tare dasu wajen. Karfe hudu duk ina gida part din mu na nufo kai tsaye sai dai ban samu mum ba don haka na nufi daki in rage tufafin jikina har kuma nafito falo mum bata shigo ba hakan ya ban mamaki fitanta tabar part din abude . Cikin gida na dosa in tambaya ko ta fitane a tsaye na samu matan daddy enugu suna magana suna ganina kuma sukayi shiru gaidasu nayi nake tambayan mum din. Amaryan ke fadin tana ciki dasu Alh tun safe yau bai fita ba yana gidan nan suna rigima da hjy Malka akan zancen auren yayanta Allah dai ya sauwaka tashin hankali baida dadi wallahi shi kuma Alh ya kafe sai yayi abinda yayi niyar yi. Hafiz ma yazo dazun nan duk suna ciki suna magana tare da wasu yan uwa da sukazo daga katsina a raina nace Allah yasa a wargaza zancen nan. Saidai a fili juyawa nayi na koma ciki na kwanta a saman dogon kujera ina faman tunanen abinda zaije ya dawo akan zancen. Don nasan mahaifina ba zai taba budan baki suyi magana kan hukuncin da daddy ya yanke a kaina ba sai dai Allah kadai zai kwatoni ga hakan. Na dade wajen sai ga mum ta shigo tayi mamakin ganina a falon zaune take fadin kin dawo ashe na amsa da ehh tun dazun nashigo . Muna can yau gaba daya abin baiyi dadi a gidan nan ba wallahi badon zuwan su yaya ba da Allah ya gyara gaakiya yau da ban san inda fitinan nan zai tsaya ba gidan nan. Don abin ya kaisu har da duka da rotse rotse da girman su suna aikin yara ga hafiz yazo shima da nasa haukan shikan ai ban raga masa ba don mahaifi mahaifine ko ya yake kuwa. Allah dai ya gyara Allah yasa kuma iya fitinan ke nan don gaba akewa gudu tunda abu har yakai ga hukuma ai zance baiyi dadi ba. Haka tayi ta koro jawabi a gajarce ta yadda ba zan fahinci meya faru ba don dukule zancen da tayi ill takardun resit dana mika mata ta karba sama sama ta duba take fadin anyi komai ke nan na amsa da ehh . Tace Allah ya bada sa,a yasa ki amfana damu duka da sauran al,umma baki daya wanan yasa ban damuwa sosai don karatun nan da zakiyi din. Baga Nafisa ba yanzu karatunta ya taimaka mata ga komai har takan manta da abinda ya sameta a baya karatun yana da amfani sosai ga mutum idan ka dage kayisa Allah ya taimaka yaba sa,a na amsa da amin. ZAINAB IDRIS MAKAWA [2/21, 21:53] Maman K: DUBA MIN BAYA FOKON,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Me karatu nasan zakiyi mamaki da al,ajabin yin shiruna haka lokaci guda ba tare dana nuna wani bori ko botsewa zancen daddy ba alokacin . Hakane kwarai hakan kuma ya samo asaline bisa ga gargadin dana samu daga mahaifana dakuma hjy mum dita da sukai min cikin kakausan murya kan yiwa iyayye biyayya don baba ya gargadeni da cewa duk yaji wani rashin mutunci ya fito a bakina in tabbatar dana nemi wani uban bashi a duniya. Amma ke kina ganina kinsan ina cikin tashin hankalin tsaka mai wuyan fita a rayuwana gashi ansano yin shiru koda kuwa ana min habaici ko cin fuska dole nake jan bakina inyi shiru. Saidai yanzu gaba daya na daina fita ko ina daga makarant dana fara a yanzu sai zaman part din mu wanda ya zamo sabon hali agareni yanzu din. Ban shigo ko wajen Dada balle part din hjy mummy da yanzu a kusan haukace ta da kowa agidan don ganin laifin kowa takeyi yanzu mutakat ka zaune a karkashin daddy don tace hadin baki akayi ai mata hakan don aga iyakanta. Tana zaton da bakin mum cikin wanan shawaran kamar yadda nima na zata fa farko koda saninta akai min haka djn daddy ya rasa wanda zai hadi aure sai hafiz dan hjy malka. Matar da bata kaunan ko jin sunana a bakin wani balle ace wai nice a matsayin sarkuwarta kan danta data kwallafawa rai a duniya fiye da kowa da komai nata sai gashi haka ya faru yanzu. Ni kaina nakan zauna wani lokaci inyi tunanen ko meye dalilin daddy na zabana yaba ya hafiz a matsayin mata ko hakan na cikin karin zumuncin da yake ikirarin yanayi da mahaifina ke nan. Duk rikicin nan ban taba sakashi a idanuna ba saidai inji a bakin mum cewa yazo koya tafi cikin zance don dama ba gwanin shigowa part din bane ya gaida mum shi sai lokaci lokacin daba,a rasa ba can ko wani abu kwakwara ya shigo dashi part din mum din. Safiyace sauri nake kada in makara don yanzu tafiyan mu bai daidai da anty Nafisa don ita takan dan jima a gida yasa nake rigata fita a yanzu din. Sauri nake nafito daga cikin gida inata kokuwan gyara hijjab din jikina kamar