Sashe 11
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da tsabta har ita babban Nafisa take fadin. Kece kika gyara wurin nan haka na dago cikin gajiya ina gyada mata kai da sauri naji tace a zozozo don Allah idan kin gama sister kin huta kizo mu shirya dake kinji gaskiya kin burgeni. Ban zauna ba tsakani da Allah da zuciya daya kamar yadda uwata tayi min tarbiya haka na gyara masu muhalinsu ya koma yana sheki tas don dole hjyr nan tazo har dakin Dada muna zaune halima nawa Dada dariya abin karin data kasaci . Don doyace aka soya busai busai sai taliya aka kawo mata tace ba zataci ba ita kan cikinta ya baci don haka mu muci nace nikan na koshi halimatuma tace itama a koshe take sai ga hjy din tashigo tana fadin. Sannu yar nan kece ke kadai kikai wanan aikin haka har ina batun nayo hayan ma,aikata wallahi su gyara min wajen sai gashi karamar yarinya haka tazo ta gyara min shi tasa Allah yayiwa rayuwa albarka. Dadace ta amsa da amin aishi da na kowane don baka san inda zakaci alherinsa ba abinda uwarta ta koyar dasu ke nan ita kan bata kyataci diyanta ba wallahi don ko yaushe zaki shiga gidansu sune a tsaye har kananun kannenta zaki samu suna dan aikace aikacesu a cikin gida. Yasa ko ko yaushe gidan nasu ko abinka ya fadi kasa zaki iya dauka kici do tsabta karyane kije gidan maryama kice kinga kazanta a gidansu. Wayancewa hjyn tayi kamar bata san gugan zanan da Dada ke mata ba tace ai kinga ta huta gashi yarta ta nuna hakan ai yanzu . Fitan hjy nima na mike nace ina zuwa halima nabar Dada na fadin sakarai kin zauna don son kai kin lalata kanki da yayan ki kuma ki hana ayi magana kina takama da bin bokaye sakarai kawai. Part din nan na koma jug din da ak zuba muna kunnu na daukowa dada da sauran fanke na zubo a leda tayi damke muka hade da hjy sai na dan rude guilty,conscious ya kamani nake fadin . Dama Dada ce bata iya cin doyan da aka kai mata ba da taliya shine na dauko mata kunnun nan tace a,a shine baki fada min ba aje wanan din bari na baki me zafi ki kai mata yar gidan Dada. Wani dan flask ta kawo tare da dan kulanshi ta mika min na fita dashi na kai mata na dire a gabanta saiga tsohuwa ta shiga saka min albarka a take tana fada tana zukan kunu hadi da fanke ta shanye kofin kokon ga baki daya. Banje gaiyatan da anty Nafisa din tayi min ba a ranan don ko ana azahar na mike na koma wajen hjy inda muka kwana wace nake kira da gwaggo a lokacin gyare gyare nayi mata sai gani har kitchen dinta ashe kowa nada kitchen dinsa a part dinshi. Nan ma na gyara mata shi tas sai magariba lis na samu kaina a gajiye na koma wajen su Dada ta kalleni tana tambayana ina kika shigane kin gane uwarki kina can ko ? Nace gyara nayi mata shiyasa na dade kin huta nace ke kan kin huta da Allah bai sako maki son jikin banzan nan na yayan zamanin nan ba uwarku ta hutar daku wallahi. Meye cikin son jiki da lakacin matan zamanin nan banda zancen banza aiko gashi aure baikai ko ina ba zakiji ya mutu don lalaci da son jiki mace ko yaushe tana makake da waya tana dariya a daki kamar me hira da aljannu ita kadai. Koke yanzu sai kiji dadin jikin ki ba zancen dibgewa a gareki sai kaji ka tashi wasai washegari don ka motsa jikinka ka hana wani cuta samun wajen da zai makele maka a jiki har yai maka illa. Aiga wanan sakaran da bata da wayau kwance ta wuni tana lalaci anan ko dan kara bata iya nunawa ba dai ta tashi ta biki kuyisa a tare dai itama ta samu wanan albarkan da ake saka maki a,a ta saba da kwanciyan lalaci tana bin gado . A hakane har wai kike da saurayi hakan zai aureki ko shara baki iya ba balle ki masa abincin kullun ina maku kwantace da halin yarinyar nan amma kunki wai ku gata tana zagin halimatu dake kwance saman gadon. To aini bata fada min inzo muyi bane hakimatun ta bata amsa daga inda take Dada ta tare da fadin ke arr ita waya fada mata ta tashi tayi niko ubanki dake gida zaune. Haba Dada har da zagan muna uba dai kan wanan maganan na fada ina zama gefen halimatu din itako cewa tayi ai kinsan dada idan bata zagi uban mutum ba bata huce haushinta akan mutum. Nikan bam aikin banza ga mutanen da basu san darajanka ba su daukeka dan kauye ko nakasashe na kasa dasu tunda ina da uwata da ubana wallahi banyi haka kawai in karar da karfina ga banza saboda su. Dada na fadin kinji ko kinji girman kai irin na dan arewa kaiba kowan kowa ba tusan galadima amma ka dauki girman kai ka dorawa kanka don fadin anta. Yayin da ni kuma nake fadin ayya halimatu gidan uban mune fa idan mun masu abu shine ragewa ko kasawa innan mu kance mu kyautatawa duk wanda ya tsofe muna idan yana bukatan taimakon da mukafi karfinsa ta hanyar bada karfin mu tunda bamu da abin basa sai hakan ya zamo muna alheri a karshe. Innan ku kukace Abu inan ku ai ta dabance don ta tarbiyantu ta kuma baku tarbiyan kuma don ta fadi hakan ai ba abin mamaki bane idan kunyi hakan. Kawai sai jin sheshekan kukan halimatu din mukaji hakan yasa na juya da sauri cikin mamaki din ban taba zaton zataiwa kalamin Dada kuka ba don a kullun haka suke cikin rigima da juna wai a cikin itace mai daman yar uwartama da muka bari a gida sunfi kwasan rigima da Dada din donshi tace bata zuwa sai yan gida zasuzo ta biyosu don halin Dada din. Haba keko don Allah meye haka kuma azo a samu daga zuwan mu kinawa Dada kuka haka na fada cikin jiyowa ina taba mata kafa jin hakan yasa ta dan rage sautin kukanta tana fadin. Ke bakiji zagin ta take min bane tana nufin uwatce bata da tarbiya bata bamu ba daga can kuwa Dada tace na fada tana dashi din ne ta baki ko me ? Fadan nasu dariya ya bani don inda sabo a yanzu na saba ganin fadansu fiye da hakan ma tun agida kuma nan da nan su shirya nace kai amma halimatu akwaiki da wani zance kema. Yanzu aiba a hannun umma kike ba a hannunta kike inma batacine ita ta bataki ai da zaki tsaya zuciya haka tace ai bata ganin laifinta saina umma ko yaushe. Dada tace nace uwarki nakara fadan uwarki din ke kuma kodana daukota ta dawo wajena aida hakoranta tab a baki na daukota nace kwantas tsohuwa kada fadan ya koma nawa kuma kingani Dada bata da gwani a wajenta nima gashi tana shirin sauke min nawa yanzu. Shigowan wanan amaryan dakin yasa mukai shiru banda Dada dake masifa ta kalli Dada din tace ke kuma waya tabaki kike masifa budan bakinta sai cewa tayi ai dole in masifa yarinyar banza zata raina min wayau. Ku halan baku san halin Dada bace kuke biye mata kunsan fa kishiyoyinta basu nan yanzu ku zata mayarwa da kishin kuyi ta fada da ita ko bakuji labarinta ba lokacin mijinsu malam yana raye. Labarin arziki ba nikan lafiya muka rabu da yan uwana ki tambaya ki kara bamuyi irin wanan bakin kishin zamanin nan na iyayyen ku ba. To nikan bari in fita kafin a sake min layi nawa ya sameni ta fada tana juyowa wajen Dada din ta kallo inda nake tace sister banganki ba kuma nace ehh anty na bari nagamawa su mamane sai gobe da safe idan Allah ya kaimu sai nazo na gyara maki hankali kwance. Tace hakan ma yafi ko kinzo kin samu ina kwance ki kwankwasa min zan tashi na bude maki tunda nasan da zance daga can mukaji muryan Dada na fadin sannu kwamishiniya watau ma kinsan da zancen ko daba zaki bude kofan ba ke nan. Wanan kam anyi yarinyar kawai a wajen nan sister don Allah kada ki manta kinji nace to anty tafice tana dariya muka bita da kallo dada na fadin haka za a gidan mijin solai solai ba asan komai ba sai daukin ayi aure ake fadi a baki. Wai dama itace zatayi auren na fada cikin tambaya lokacin Dada din ta mayar da kallonta gareni tana fadin itace mana ba ita bace babban yar ita marka duk haihuwan marka din ai matane sai dan namijin na biyu sauran duk mata gashi a karshen nan ta sake namiji shi kuma gashi ta sake masa ya taso wani sakarai dashi haka. To Allah ya shiryamu baki daya na fada tace amin ai zaki sanshi ba kwanaki sunje can inda nake ba da sukazo mukai ta kwasan rigima dashi dan kawai. Tsofi kan akwaisu da zagi gaskiya komai kayi zagine wajensu nake fada a zuciyana muryantane take fadin ai kinsan ita kubura mijinta na farko rasuwa yayi yayi hatsarin mota hanyar iko ya mutu. Shine data gama wanka wanan baban naku dama gasu yan uwa gasu abokai saiya mayar da ita dakinshi don dan lokacin yana da mata daya suka zama su biyu. To shigowan wanan marka din gidan yasa har ya rabu da ita ta farkon yar makwabtan muce can katsina ita dai kuburah dince data zamo ta gida ba yadda zatayi dole ta barta har aka kai yanzu ciki ba dadi ga zaman nasu. Shiyasa jiyan nan naci mata mutunci iya son raina dama ina da cikinta tun kan abinda tayiwa mai sunan malam yaro marayan Allah kice ba a taimaka masa don son rai irin na marka. Mukan ba zancen mu bane don haka ban tsuka ba saima halimatu da naji tace dani aida gani sai tayi izzan tsiya dama bakiga yadda take kallon mutane a hankade ba. Ni hakan yasa ko zuwa sukayi katsina bani shiga gidansu idan basun shigo gidan Dada sun rutsa dani ba in