Sashe 10
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
min dayan ku. Akace ku bakwa nan sai Kuburah a gidan shine na aika tazo ta taimaka min da ita shinefa ta dauketa zuwa sashenta kinsan shi yaro karene inda yaga fuska can yake dama wanan ne dalilin kika gansu tare ai amma kayan su yana nan guna ai ko yanzu kinji nace ta bata magani kafinta kwanta ai. Dada banda hakan shin akwai wani barene a cikin yaran nan don Allah ko banza yarinyar nan kakarsu daya da mahaifinta da ita kuburah zaki iya raba halakan dake tsakaninsune kome ,? Ai gata gasu dama ni nauyi ta rage min ai yace baki san hakan ba tunda kin fassara hakan da wani manufa daga inda Dada ke zaune tace wai tsaya intambayeki marka. Mu din ne nauyi yau a gareki da kike wanan zancen ko suwa kike nufi da nauyi a wajen ki ina dai nine sai diyan nan naku biyu da shakuwa yasa nazo dasu tun yanzu garin nan don su debe min kewa. Kin fadi hakan tun yanzu inaga kin tara taron yan uwa an cika maki gida da jama,an arziki kuma kaga musa wanan yasa na daina zugan zuwa gidan ka dama don iyalinka har yanzu ba hankali ne dasu ba. Hjy kin dai ji kin kuma gani da idon ki ni bansan yaushe malka zatayi hankali ba ta daina wanan bakin kishin data dorawa kanta kan kuburah. Wanan yasa na matsa ki taso akwai matsala kin fara ko ganin inda matsalan take yanzu mikewa Nafisa tayi wace za aiwa auren don barin falon don ba zata iya juriyan jin abinda ke faruwa tsakanin iyayyen nasu ba lokacin. Mahaifin nasu yace ki dawo ki zauna kiji abinda za a fada koke abin ya shafeki don gidan wani zaki bako dukkan maza zasu dauki wanan akidar ba ki sanni. Simi simi ta dawo ta zauna tana turo baki kafin muryan Dada ya karde falon tana fadin wallahi marka kin bani kunya sai inje gidan dan uwanku indawo muna marmarin juna dasu kuko nan duk nazo da bacin rai nake barin garin nan kuma duk kece ummul,aba,isin hakan a gidan nan kuburah dai zuwa kikayi kika sameta sun zauna da zuciya daya da wace ta fara samu a gidan nan amma ke kin kasa hakan. Bani ba kowa a cikin dangi ba maza ba ba mata ba tsoron zuwa gidan nan sukeyi don masifan ki da fitina bako bai zuwa baki samu sherin da kika lakaka mas ba kice yayi maki keda diyan ki. Haka yaron nan Aliyu kin hana yaro shakat a gidan nan yau in Musa bai rike Aliyu ba duniya koda bai auri kuburah ba wakike son ya rikeshi a cikin dangi. Yanzu kuma nime nace akan Aliyu hjy ta fada cikin hasala da dago kai tana aon jin ba,asin jefo Aliyu a zancen da sukeyi yanzu din. Ai magance data shafi hakan malka uwar tawa zaki tsare da tambayan nan asheko ranki zai baci dani kiyi fatan ayi bukin yarki kina gidan nan na fada maki hakan ba yau ba. Zan dauka na shaye duk wani hali naki amma banda wanda zakiwa uwata ko wani dan uwana a cikin sha,anin nan kai dagata don Allah Dada ta fada a cikin tsawa yasa ya tsaya. Mikewa Dada din tayi da kyat tana fadin baidai zuwan mu dana yan uwanka da zasuzo daga baya ya kawo wanan kace nace ba a yanzu ? To ku bari goben na dasafe zan saka yaran nan gaba mu koma katsina su kuma dangi zan gargadi kowa kada wanda ya kuskura ya tako sha,anin ku indai ina fada maishi yaji a cikin dangi. Kuka sosai hjy malka din ta saka tana fadin nikan bakin jinina yakai haka yanzun nan kuma za a lauyeni har me nayi da za ace hakan a kaina. Bakiyi ba marka yanzu na kara gane manufanki akan mu sosai burinki shine ki mallakemu kamar yayan ki sai yadda kika juya mu a gidan nan toba zai yuyu ba na fada maki. Kama kanki a watse lafiya shiyafi don a yanzu ba mai daukar maki wanan bakin mulkin naki na kafirci kishi haukane koke kadaice farau tarda kishi a zauna lafiya. Hannun Dada Nafisa ta kama suga shiga daki har lokacin Dada tana masifa Nafisa din tana bata hakkuri saboda tasan idan batayi hakan ba zata kwabewa mahaifiyar nasu kan bukinta din. Mukan bamu san anyi hakan ba amma ita mai shiyan ta sani tun tana sintirin kawo muna abinci tana jin hayaniyarsu a lokacin. Hakkuri irin nata yasa bata kula ba har wayewan garin nan kuma da muka tashi tasan akwai zance a kasa tsakanin abokan zaman nata yasa tayi shiru amma abin nacin zuciyar ta. Ki karbi wanan ki saka don nasan yanzu basu bude part dinsu ba ina ai zai maki irin rigunan da nakan ajenevson haka rabonkine ya dan jima a dakin nan ban kyautar dashi ba. Ki zauna nan ki shirya inkin gama ku dauki man kuyi amfani dashi ga kayan kwaliya a mirro duk dani ba wani kwaliya nakeyi ba amma ba zaki rasa abinda zaki amfani dashi ba a nan. Tana fadin hakan ta fice daga dakin kitchen ta nufa don hada abinda zamu karya dashi din lokacin na bude roban man shafin na lakoto naji yana kamshin wani icce kamar saye ga laushi mai dadi a jikinshi kamar man bama da akecin ganye dashi. Daga roban nayi ina kokarin karanta sunan man naga an rubuta naturalsense nayi nayi na fassara kalaman da hausa na kasa har nagama mulke jikina badon naso ba na rufe roban kada ta dawo ta samu ban gama ba na nufi mirro din a nan ma na rasa me zan shafa kayane birjit a wajen da bansan amfanin su ba lokacin. Bayan na dan shafa na mayar da komai a inda na sameshi na saka rigan a take naga na koma kamar bani bace a gaban mirro din haka na daure na fito daga dakin zuwa inda muka kwana. ZAINAB IDRIS MAKAWA [1/20, 17:40] Aishatu Aliyu Musa : DUBA MIN BAYA FOKON ,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Ranan bani gajiya da satar kallon kaina a jikin mirrow halimatu ba zatace ga tufafina ba don haka bata gane wanan din daga mai shiyan ua fito ba sai faman yabawa da itama takeyi akai da yayi mi kyau . Har lokacin da hjy ta kawo muna abincin mu har daki kokone da fanke sai ruwan shayi kuma shi mukaci muka koshi lokacin halimatu take zancen wanka. Kafinta shiga tace bari ta karbo kayanta wancan dakin ta dan jima kafin ta dawo dauke da jakkunan kayan namu data dauko muna saida ta aje take fadin. Anya ba gida zamu koma ba kuwa zainab don naji Dada na fadin kada mu yamutsa kayan mu tafiya zamuyi yau din nan ina ganin wani abu ya faru jiya bayan mu yadda naga ran Dada abace dana shiga. Inma gida zamu koma zanfi son hakan ai halimatu don ni sam yanzu kanon ya fice mun a raina danazo kuma sai naga ta kalleni tana dariya kafin tace dani kuma dai ? Yanzu har kano din ya fice maki a raine kuma daga zuwan mu na dan bata rai kafin nace gidanne sai a hankali halima tunda naji me wa yan can sukace daku jiya ai. Kedai bari ga wanan ita babu ruwanta sai haba haba da takeyi damu a nan wanka ta shiga kafin ta fito na mike na gyara gadon har daki ta fito tana santin bandakin kafin kuma ta fara zancen man shafi na nuna mata wanda na shafa ta dauka tana wani dubawa kafin tace. Nifa irin mayukan nan ban faye son shafasu ba nafi ganewa ainihin vessiline dina in shafa yafi kama jiki nayi murmushi na mike na bude jakata na dauko mata wanda take son shafawa din na mika mata. Kuje ku gaida mutanen gidan muryan mai shiyan ke fada muna hak daga koda muka amsa da to lokacin halima tagama shiri muka nufi part din don ita tasan hanya niko shiga banyi ba tun zuwan mu din. Ina kallon part din baida bambamcin tsari dana wanda muka kwana iya bambancin kayan alatune kawai da wanan yafi wacan dashi kuma ba gyara gasu duk sunyi kura a jiye wajen da suke. A haka har muka kai daki da Dada ke ciki mukayi sallama muka shiga Dada din na zaune ita kadai a dakin muka gaida ita take tambayan jikina nace da sauki. Dan shiru ya biyo baya wanda hakan zai nuna maka cewa bata cikin yanayin dadi a lokacin can ta dago tana fadin kuyi hakkuri baku karya ba har yanzu ko ? Halimatuce tace tun wani shekara Dada mukan munsha koko da shayi har da fanke tun dazun mun kumayi wanka kafin mu fito. Ai kaji kaji abin su wa yan nan suna nan sunata faman barci kamar masu barcin mutuwa wai sai yanzune suka tashi ake neman abin karyawa din. Duba min don Allah wai har tana fada don me zakuje wajen kubura ku kwana baku tsaya a nan ba ko in kun tsaya uban wa zasu baku yanzu da kun kwana nan din ? Ai har fada tayi dama kan hakan Dada halimatu ta tambaya sai Dada din tayi mata wani irin kallo mai kama da ina ruwanki taja bakinta tayi shiru ni dai ina gefe zaune ina raba ido kafin in mike ina fadin bari na gyara maki dakin Dada. Ban jira tace ba na mike na hau gyaran daki sai gani har dogon corridor dinsu har falonsu har suka sameni muna gaisawa ba laifi don banga komai ga yaran matan ba saidai uwar. Da dakyar ta amsa gaisuwan nawa ta wuce saida nayiwa komai kal saboda sabon zama